Assalamu alaikum. Okay, so I have been slacking on this story, I apologize. I will try as much as possible to keep updating at least twice a week.
I dedicate this chapter and the next to two of my ardent readers, xclusive_jasmien and Ummyasmeen.
Thank you for the push up and motivation.
For others, I love you too 😘😘
Fatima ta na zaune jiran fitar Ya Bello daga ofis din likitan da ke asibitin Gwamnatin Tarayya da ke garin Gombe, wato FMC. Ya saba zuwa ne da Ya Mubarak, amma bayan faruwar abubuwa a dan tsakanin nan, ya janye daga wasu abubuwan sa.
Ba wai a kan Adda Ummu ba ma, kan abubuwa da dama ba jituwa suke yi ba. Babu kuma wanda ya isa ya shiga tsakani ko ya sa baki. Don tun daga firamare suke abota da juna, har zuwa yanzu da suka zama tamkar ‘yan uwan juna.
Tare suka ga Ummu har ma hirar neman auren ma Ya Mubarak ne ya yi wa Ya Bello rabin sa har a ka kai ga aure. Shi kuma Ya Mubarak ya auri kawar ta Saudat.
Ta hakan zumuncin su ya kara kulluwa, har bayan rasuwar Saudat din. Iyayen Saudat din ne suka ba da kanwar ta Rasheeda ya aura don irin zamantakewar da suka yi mai dadi.
Duk ta kosa da son komawa gida. Ta dade da tsanar ziyartar asibiti ko ma zama cikin sa. Warin sa da tsarin sa komai kyaunsa baya burge ta. Gaba daya a dofane take, tsikar jikin ta ya na tashi.
“Fatima Isa?” Ta jiwo muryar da ko a cikin barcin ta ta ji za ta gane.
Ko da ta juya gefen da muryar ta fito, sai ta yi arba da idanuwa biyun da ta dade ba ta gani ba, wadan da suka nuna farin cikin ganin ta a lokacin.
Me ta ke yi a nan? Tambaya ce marar fa’ida, tun da nan asibiti ne. Idan ba a samu likita cikin asibiti ba a ina za a same ta? Ita ce ta karaso wurin da Fatiman ta ke, ta ce, “Really, ke ce haka?”
“Ni ce, Dokta Sumayya.” Fatima ta cakuda murmushi a fuskar ta,
“Kin ga yadda ki ka yi kyau kuwa? I can’t believe it, na kasa gaskata idanuna.” Murmushin Dokta Sumayya ya kara fadi.
Ta na sanye cikin doguwar rigar atamfa, wadda ta dora wa farar riga ta likitoci, sannan ta rufe kan ta da irin kananan hijabai ma su kyau da tsari. Tun fil azal ma hakan shigarta ta ta ke,a kalla tun sanin ta da ta yi daga wannan dare,shekaru hudu da suka gabata.
Fatimar ma murmushin ta kara fadadawa. Akwai lokacin da wannan murmushi na Dokta Sumayya ya yi tasiri a kan ta, ya kasance shi kadai take jiran gani wajen neman samun sukunin rayuwa.
A lokacin Ya Bello da Dokta Sani suka fito tare daga ofis din, likitan ya na zayyana ma sa sharudan da zai ci gaba da kiyayewa. “Mun canja ma ka magunguna saboda wadancan din su na ba ka matsala. Sannan tilas ka ci gaba da kiyaye irin abincin da za ka ci.”
“In shaa Allah Dokta, zan kiyaye.”
A lokacin ya fuskanci Dokta Sumayya sannan suka gaisa. Likitar ta dage kan su karbi lambobin juna ita da Fatima, wadda hakan suka yi. Daga nan ne kuma suka yi sallama.
Kan hanyar su ta komawa gida cikin shiru suka yi tafiyar, in ban da lokacin da Ya Bello ya tsaya ya sayi kayan marmari. Ko ba komai, mutum ne mai maitar tufa da inabi da ma kankana. A nan ya bar Fatima ta na zaune cikin motar kamar gunki. A kalla yadda ba ta motsi ne ya sa ta zama hakan. Amma cikin zuciyar ta a hargitse ta ke. Duk kuma dalilin ganin Dokta Sumayyar ne.
Ta nisa. Ba ta san ranar da wannan abu zai kare gare ta ba. Ita kan ta ta gaji, ta rasa abin da za ta yi. Da a ce mutum zai iya goge abin da ya faru a baya cikin rayuwar sa ya zama tamkar bai faru ba, da ta sai da ranta don ta yi hakan.