*....B'OYAYYEN* 👒
👒 *AL'AMARI**_Pure Moment Of Life writers_*
© '''Written'''
By
*_Seemaluv_*👄*4-5*
Safna tana fita daga company d'in ta tsaya bakin titi domin samun abun hawa, Bata wani b'ata lokaci ba ta tari mai keke napep tai mashi kwatancen inda zai kaita ' kasancewar K'auyen su da cikin garin bashida nisa.
Farin ciki ne cike ranta ' don kuwa ya kasa b'oyuwa a fuskarta.
"Bawan Allah d'anyi sauri mana".
Cewar Safna.
Haka tasa mai keke-napep ya karawa keken shi gudu, Ita kuwa sai godewa Allah takeyi da k'osawa taga Umman ta.
*AROUND 5:00PM*Safna ta isa gida ' nan ta sallami mai keke-napep sannan ta shige gida, Safna shiga tayi d'auke da sallama a bakinta ta iske Rumaisa tana jan ruwa a rijiya.
Jin sallamar yasa Rumaisa d'ago kanta ta kalli Safna, Cikin jindad'i da nuna farin ciki Rumaisa ta aje gugar a gefe tayo kanta.
"Yaya Safna, sannu da dawowa ' Allah dai yasa antaki sa'a".
Murmushi kawai Safna tayi gami da cewa.
"Umm! Ina Umma take?".
"Umma tana d'aki tare da Anisa".
"Ok".
Safna da Rumaisa d'aki suka shige cike da sallama Umma ta amsa.
"Alhamdulillah Safna ya hanyar?".
"Umma hanya lafiya k'alau, yana barku?".
"Lafiya k'alau Safna, Allah dai yasa anci nasara!".
"Insha Allah Umma".
Cewar Safna.
Bakin gado ta samu da zauna ' sannan ta cire hijab d'inta ta aje gefe, Tukunna ta cigaba da cewa.
"Umma! Kinga wannan takaddar?".
Tayi mata nuni da takaddar dake hannun ta.
"Eh k'warai".
"To mataimakin Ogan wajen ne yayi mun rubutu aciki ' yace kuma indawo ranar litinin da takaddar tabbas zan samu aiki".
"A wane waje kika nema?".
Cewar Umma.
"Umma a babbar ma'aikata ce (Company)".
"Kinga Safna banason abunda zaije yajawo matsala?".
Rumaisa ce tayi sauri ta shiga maganar.
"Haba Umma? Insha Allah babu wata matsala!".
"To Shikenan! Allah ya shige mana gaba".
"Amin".
"Umma? Ina abinci na don nadawo da yunwa wallahi".
Cewar Safna.
"Tuwo ne da miya gayacen ' ki d'auko kwano ki d'iba".
Tashi Safna tayi gami da cewa To ta nufi wani d'an d'aki wanda anan ne suke aje kwanoni, Nan ta d'auki kwano ta dawo d'aki ta zuba tuwon taci.
Bayan ta gama ne Umma tace.
"Safna?".
Ta d'ago kai ta kalleta tare da cewa.
"Na'am".
"Wai wannan ma'aikatar ta mecece?".
"Umma ma'aikar tumatirin gwangwani ne".
"To Allah yasa adace!".
Rumaisa wacce ke gefe tana kallonsu ta amsa da amin.
Safna suna cikin haka ne aka kira sallar magrib, Cikin nutsuwa gaba d'ayan su suka tashi sukayo alwala sannan sukayi sallah.
Bayan sun idar ne Rumaisa ta tada Anisa domi itama tayi sallar.
Atak'aice dai basu kwanta bacci ba saida sukayi sallar isha'i tukunna.Haka rayuwa tacigaba da juyawa ' da dad'i babu dad'i haka Safna da Umma ke fad'i tashi don ganin rayuwarsu ta inganta.
*3DAYS LATER...*
Yau take lahadi, Safna da Rumaisa tunda sassafe suka tashi suka fara aikin cikin gida ' kamar yadda suka saba, Sannan Umma ta tashi ta had'awa Rumaisa waran da zata sayar a k'ofar gida domin su samu su sami abinda zasu ci.
B'angaren Kamal kuwa zaune yake cikin Office d'in shi yana danna laptop kira ya shigo cikin wayar shi, Ganin Oga ne yasa shi yin saurin d'agawa.
"Sir?".
"Yes come to my office right now!".
"Am on my way Sir".
Kamal yana gama fad'in haka wayar ta yanke hakan yasashi tashi cikin hanzari ya nufi office d'in Oga.
Kai tsaye ya shiga ciki ' ya sameshi a zaune saman kujerar shi ya juya baya.
"Sir, Am here".
A hankali ya juyo ya kalli Kamal.
"Good! Zaka iya zama".
Kamal zama yayi cike da ladabi.
"Kamal, Ina fatan komai suna tafiya yadda akeso?".
"Eh sosai kuwa".
"Good, there is a lady ' da naga ta fito daga office d'inka kwana biyu da suka wuce!".
"Ohh Safna?".
"I don't know!!!".
Ya fad'i haka cikin fad'a da tsawa, Hakan yasa Kamal jin fargaba a cikin zuciyar shi.
"What did she think of herself? Who is she to you?!".
"Sir am very sorry!".
"Sorry for what? Me tazo nema?".
"Oga, Aiki tazo nema with secondry certificate ' Sir please a taimaka mata marainiya ce! And is like itake d'awainiya da gidansu....".
"So? What does that suppose to mean?".
"Sir please ' yarinyar tausayi ta bani, Please koda coffee ne saita rik'a had'a maka ana biyanta sallary".
"What??? Coffee? Did you just said Coffee? How? Wannan kucakar yarinyar? No no no! No way!!".
"Sir! Bantab'a neman abu wajen ka ba narasa, Yakamata ka duba".
"It's ok i will think about it! But mind you idan ma wannan ne ' then it would have to be competitive".
"Hmm Okay Sir! Thank you... ".
"You may leave now! ".
Kamal tashi yayi yabar office d'in cike da ladabi.
"Inhar Sunana *FAUZAN IMRAN!* then i will have to teach that what so called Safna ' a leason!, I will teach her how to respect her elders ' batada ladabi ko kad'an".
Yana gama fad'in haka ya d'ora hannun shi saman laptop ya cigaba da advertising products d'in shi".*DEDICATED TO MY FAN'S*
😘😘😘