Dan ubanki kwadayi kika fara zuwa makota? Hajiya ba haka bane wallahi. To yayane? Wallahi bani aka yi. Waye ya baki toh? Hajiyan ta fada a fusace. Aysha ce ta kawo min dazu. Murja takalleta a yatsine tace wato bayan kwadayi har karya kika iya ko? Wallahi anti murja ba karya nake ba, inti ta fada a tsorace. Kan ta kara magana ta sa kafa ta shure ta ta dauke ledar, dama murja akwai kwadayi. Hajiya kuma ta tsaya tace mata kar in dawo gidan nan baki gama komai ba. Yau tuwo zaki tuka abincin rana da miyar taushe. Inti ta daga kai a ladace tace to hajiya. Girman jikinta na rudarsu har suke ganin komai ma zata iya, kuma shekarunta ba su kai a sa ta wani abin ba ma.
Mikewa tayi da hanzari ta lalubo maganin da anas ya kawo mata ta sha. Tayi maza ta fito, kayan wanke wanke ne himili guda a kitchen din, nan da nan ta fito da su bakin pampo ta koma kitchen ta gyara shi tsaf! Duk abin da ya dace tayi kan goma da rabi na safe ta kammala.
gun murja don karbar kudin cefane kamar yanda aka saba. Kwankwasa kofar dakin tayi a tsorace, daga ciki kuma ka ce shigo. Kallonta murja take sama da kasa tace mata meye? Dama...mhmmm..wai.... Dallacan menene? Murja ta daka mata tsawa. A tsorace tace kudin cefane.. wani dogon matsiyacin tsaki ta ja tare da cewa, ni fa hajiyan nan ita kullum ni zan dinga bada kudin cefane? Wahala nayi ma samo ita ma ta samo mana (dama murja ta raina uwarta) ta kunkuni ta jefa mata dari biyar ta dauke da sauri ta fita.
A gurguje taje tayo cefane ta dora komai.. dama dadin abin murhu 2 ne. Nan da nan komai ya kankama. Tuwon nan haka ta yuke ahi, dan tun bata iya ba har ta iya saboda zagi da mitar hajiya. Tana gamawa ta raba ta hi abin da ya dace. Kan hajiya ta dawo tayi wuf ta wuce gidan su aysha
*********
A gidan su aysha ta iske yaya yazo da matar shi, umma na ganinta ta washe baki tace diyata kin kwana lafiya dai ko? Tace lfy lau. Dubanta umma ta sake yi tace fada min gaskiya dai. Tace umma lafiya lau nake. Juyawa tayi ta gaida yaya da matarshi. Shi dai ya amsata ba yabo ba fallasa amma kuma hadiza sama sama ta ansa ta. Bata ji komai ba dan ta saba da irin wadannan kananun abubuwan. Umma ce ta dubi auaha tace mata sai ki shiga kitchen ku taya su larai a karasa komai ko. Toh tace, kan ta mike intee ta riga ta tace muje na taya ki. Tare suka karasa kitchen din. Nan intee ta zage ta dinga shirga aiki, a takaice dai ita tayi kusan komai, rice and stew da chicken suka dafa. Ga lafiyayyen salad da kunun aya an hada a gefe. Bayan sun gama suka fito da ahi kan dining. Dai dai da shigowar yaya. Kallon wajen yayi yace kamar kun san na kwasota. Umma ta dube shi sannan tace hadiza ki na fama. Dariya tayi a gadarance irin ta rqinin wayo din nan, saboda ita irin yaran nan ne 'yan boko da suka amsa sunan su, ga girman kai da yake damunta,saboda haka kallon kowa take. Shi kan shi yayan ba wao dadinta yake ji ba, ta raina shi ta raina 'yan gidan su, abin mq yazo da sauki dan ba karamin taka mata birki yake ba
Abin da tayi yanzu ba karamin sosa mishi rai yayi ba, kawai basarwa yayi, ga yunwa na dawainiya da shi zqma yayi kowa yazo ya zuba abinci, intee na rakube a gefe, sai da umma tai mata jan ido sannan ta taso, ci kawai suke ana zuba santi. Yaya ne ya kada baki yace wallahi na dae ban ci abinci mai dadin wannan ba, kunun ayan ma is on point wallahi.. aysha tayi karap tace yaya intee ce fa tayi duka. Taya ta kawai mukayi ni da larai. Ya dago ya kalli yarinyar yace intee wa ya koya maki girki? Murnushi kawai tayi bata iya cewa komai ba. Hadiza kuwa na gefe tana tafasa, bata san lokacin data ce shegen munafirci da neman gindin zama ne ya sata ai. Da ganin idonta ta iya kanzagi. Umma ce tace mata hadiza bana son neman magana, yi tayi kamar bata ji abinda aka ce ba, ta cigaba da abinda take. Yaya na kallonta kuma ya san tunda har umma tayi magana to lallai bata ji dadin abin ba. Suna hada ido ya watsa mata wata muguwar harara. Kallon ahi tayi ta watsar tare da rolling eyes dinta, irin " whatever" din nan.
Allah Allah take a gama cin abincin ta wuce gida dan ita bata kaunar tashin hankali. Suna gamawa kuwa tace ita zata tafi. Wani mugun kallo hadiza ta watsa mata tace ai sai ki takeaway ki wuce da abincin, dan dazu kin kusa hadawa da plate din garin loma, yaya ne ya kalleta yace ki ahiga hankalinki kar ki sake bari na rai na ya baci, wallahi zan saba miki. Duban shi tayi tace akan wannan sadaka yallar kake wani rawar jiki? Mtcheww toh Allah ya kyauta maka. Duk abinda ake umma na jiyowa ta ciki. Ta rasa wannan muguwar dabi'a ta hadiza, ke baki bawa mijinki hakkin shi ba, ke kuma bai isa ya yaba a wani waje ba. Ita kam wannan zama da suke yi ya fara damunta. Sallamar aysha da intee ce ta katse mata tunaninta, murmushi tayi ta ce intisar za a wuce? To ki gaida gida, ta miko mata 2k tace ki dan rike wannan. Umma dan Allah kiyi hakuri ba zan iya karba ba, saboda me? Umma ta tambaya, wallahi fada za ai min. Duk da haka umma bata hakura ba sai da tace mata toh duk abinda take bukata tazo ita mamanta ce. Godiya tayi ta wuce.
Ummace ta kira hadiza dake zaune a parlour, tana jin irin bakar maganar da ta yabawa intee kan su fita da aysha. Kallonta tayi tace mata hadiza meke damunki ne? Cikin rashin kulawa ta ce mata ni? Bakomai fa. To dan me yasa kika uzzurawa yarinya daga ganinta. Shi fa mutum da kike gani daraja ce da shi, ba zaka taba sanin inda zai maka rana ba, baka san kumai kai a wanne hali zaka tsinci kan ka ba. Ki nitus hadiza, gaskiya nake gaya miki sabida kallonki nake kamar ni na haifeki. Ya zama wajibi in gaya miki gaskiya. Kiyi kokaro ki chanja dabiunki ki kyautatawa mijinki ki sa shi farin ciki, ki girmama mutum komin kankantar shi, dan hakin daka raina shi ke tsone maka ido, kuma duk abinda ya baka tsoro, wata ran tausayi zai baka. Haka kuma duk abinda ya sa ka kuka wata rana dariya zai baka. Ki kula, ita rayuwa darasi ce.. haka kuma duniya makaranta ce. Dan Allah ki gyara, tashi kije. Fita tayi tana muzurai. Girgiza kai umma tayi tace Allah ya shiryeki
YOU ARE READING
DUNIYA MAKARANTA
Romancelabarin rayuwa da abubuwan data kunsa na farin ciki,bakin ciki,samu,rashi,cin amana, da rikon amana