1 NEENA MALEEK.

4.7K 202 9
                                    



1

Maleek wai kai wani irin yaro ne?, kaidai wannan ko a lahira bazakai farin jini ba. Tsinanne to daka tawo kabar shi da lunch box a hannu mutuwa aka cemaka zaiyi saboda haka Aslam koma da flask d'in yaje ya d'akko.
Maleek wanda yake da rike da jakar Aslam da ta sauran yayun sa tsaye yai yana kallon Umma datake zuba masa masifa kamar zata cinye shi.
Saukar mari yaji wanda ya gigita shi dan uwar ka kafura mara addini mene zaka tsaya kana kallo na ko kaga alamar kafurci a tare dani.....Bata rufe baki ba Aslam ya kwad'amasa mari dan uwar ka ba magana ake maka ba?.
Baice uffan ba ya zube Jakun kunan a katafaren parlor'n gidan ya juya zai tafi d'akko jakar Aslam.
Kai Jaki a haka zakabar mana parlour saika bari ka kaiwa kowa jakar sa d'akin sa sannan kaje ka d'akko masa tasa.
Komawa yai ya janyo Jakun kunan ya kaiwa kowa nasa d'akin yana fitowa yaga uniform nasu a k'asa shima tattarawa yayi ya kaiwa kowa nasa.
Fita yai yaje parkin lot ya bude bus d'in ya d'akko wa Aslam flask d'in....rife k'ofar yake k'ok'arin yai Das. ...yaji an tura murfin da hannun sa aciki. K'ara yasaki amma dan mugunta Taufeeq bai bude murfin ba saida yaga jini yafara zuba sannan ya bude yana dariyar keta.
Maleek agun ya zauna yafara kuka saida yai mai isar sa sannan ya tashi d'akin sa yaje ya wanke hannun sa kafin ya dawo ya zuba k'asa a hannun dan jinin ya tsaya.
ku wai ni ina shegen yaron nan ya shiga ne?, Amma ai yana waje kinsan bashida gurin zama sai gun shukoki, hmm wato wallahi da da yanda zanyi yaron nan ya mutu yi zanyi na tsane shi ta ko'ina kai Alhaji baiyi adalci ba da ya auro bara gurbi cikin Familyn D'an masani.
Mts ai kedai bari nifa abinda yake dauren kai shege badai kaga kukan sa ba gashi ko a ina ya iya sallah bakiga jiya yana sallah ke kyace babban mutum keyi Allah dai ya kashe shi mu huta.
Umma...Umma wai ne Maleek ya tsare muku ne a duniya idan akwai wanda yake muku biyayya sama dashi Allah ya tsinen amma yaro k'arami da bai Gaza shekara bakwai ba kuke wa wannan fatan yaro ne fa kuma maraya wanda bayada uwa ku tausaya masa mana.
Seema mu kike gayawa haka no wander ai uwar sa kafin ta mutu ta mallakeki amma kisani nice uwar ki sai danayi cikin ki na haife ki to daga yau indai ana maganar Maleek kika qara saka baki saina......kyale ta haka rabu da ita sannu itama zata gane gaskiya..
Cikin fusata Seema ta mike gaskiya ko k'arya insha Allah Maleek sai yazama shine gatan ku wataran. Yaro k'arami ni ko a labari batajin inda akaiwa yaro haka ba..
Lokacin sallah kun hanashi...yaro yanason karatu kun hanashi saidai shine dan aiken yaran ku mai riqe jaka da flask....ba shi ba aji islamiyya kun hanashi wannan wacce irin rayuwa ce?, bafa daga sama ya fad'a ba..uwa ce ta haife shi...tas taji mari tana waigawa kakar suce wadda ta haifi Abban su.
Seema dama abinda ake cewa akan ki gaske ne to bara kiji wallahi bazamu lamunci rashin mutunci ba ke wace shegiya yo inaga kema ba a halin mu bace dan yaron nan baiyi kama da uban sa ko na kwadala ba...shege da ido kamar na muji ya.
Kinga Baba ki tsaya haka karki sake zagin ta indai fad'a ne kubar ni nayiwa yata ehe kema ai.....Safiya ni zaki zaga akan 'ya?, babu zagi indai Maleek ne a yimasa amma wannan yar banda ita da zakice shegiya yo kowa kenan shege ne.
Safiya nice fa...yo ke a wa da Alhaji yake da rai kike wata yanzu kuwa ba kowa bace indai zaki taban d'a saboda haka ki nutsu yarinya ta mai kirki ce tana gama fadin haka taja hannun seema sukai gaba.
Dariyar Amma ne ya dawo da Baba daga dogon tunanin data tafi.....hmmm ai ga irin ta nan kinjawa kanki zagi sai hak'uri magana kuma gaskiya ta fad'a amma duk da laifin ki idan Boka yagama da ita ai komai zai tafi yadda ake so.
Abida maganar ki Dutse dole na kaiwa Camcambi sunan ta....Maleek kuwa indai ina raye saiya halaka ku cigaba da gana masa azaba dan zuwan sa duniya ba alkhairi aciki ranar da aka haife ka uwar ka ta mutu ranar sadaka bakwan uwar uban ya mutu ai ba alkhairi a zuwan sa duniya.
Hmmm Baba wallahi yadda natsani Maleek ko mutuwa ta ban tsana haka ba. Gashi shege duk abinda akai masa baya gani kwanaki fa Tauheed yasamu yana bashi hak'uri wai idan laifi yai masa ya yafemasa ya ringa kula sa.....ranar nagayamiki naga jidali.
Dan Maleek a d'akin sa ya kwana abinci tare zanyi fad'a ya taso mun...ai zakara sa'a yaban dan banyi wata wata ba naje gun Cancanke yai musu farraqu da duk yara na.
Hmmm ai haka za'ayi musu da Seema nifa tashin hankali na d'aya kada yaron nan ya girma dan girman sa babu alkhairi.
Tab ke kike tada hankalin ki ai wuya makarantar kare zai gaji ya gudu...burin Alhaji akan Maleek bazai tab'a cika ba..dan kuwa ko primary bazai ba bare jami'a har yakai wani matsayin da zai kama mu.
Mts kufa ni narasa kansu wai baku da magana saita karatun Maleek yaron da Boka yace shida karatu har abada yai masa aikin da harya mutu bazai iya karatun A ba bare aje ga had'a words ko Sentence.....maganar kai seema gun boka kuwa kada ku fasa kaita tunda yar kuce.
Da sauri Baba ta taso haba Safiya wasa ake kiyi hak'uri kinji? hmm hak'uri kuma bansan shi ba nagane kinfiya kuskus kuma naga duk wata kutungwila kune kuka had'a nawa kad'an ne yo na meye za'a ringa munafurci na da yarinya ta.
Tsuuuu sukai dan sunsan Safiya ba kanwar lasa bace dan tana iya tona asiri ma wanda yake rufe.
Kinga komai ya wuce yar uwa....baki ta ta be tace naji....anan suka shantake sunata hira abin su.
Seema kam d'akin Maleek ta tafi ta duba shi bata ganshi ba hakan yasaka ta tafi garden dan tasan baya rabo da can.

Auta ce

NEENA MALEEK     {COMPLETED}Where stories live. Discover now