Page 1

9.1K 359 67
                                    

Mijin mata biyu

Billy Galadanchi

A short comedy story

Sadaukarwa ga babbar kanwata Sophie G.

Haske writers Asso...

   1

Da sallama ya shigo parlor din se tashin kamshi yake,fuskarnan tasha gyara sajennan yasha mai se sheqi yakeyi, haka sumar kansa ma tayi lublub da ita,sanye a jikinshi kananun kayane dogon wandon jeans blue da kuma T-shirt fara kal kirar polo,ga wani rantsttsen wrist watch dake hannunshi daka ganshi kaga dan gaye irin ajin farko dinnan,mahaifiyarsa ya sunkuya ya gaida ta kalleshi cikeda kulawa tace

"Ali zaki Ali sarki yanzu za'ayi tafiyar ne" wristwatch din nashi ya kalla sannan yace cikeda yanga "yanzu zamu wuce umma lokaci yarigada ya Shiga" Murmushi tayi sannan ta tattare nutsuwarta izuwa gareshi

"Yanzu kai Aliyu iyakar gaskiar ka mata biyu din zaka aura kuma alokaci daya anya zaka iya kuwa?" Sosa kanshi yadanyi yace

"Umma tunda nace zan iya abarni mana,Inafa da abinda zan rike Koda hudu ne,inaga kuwa dan biyu kawai ai Banyi zari ba ko?" Kura masa ido tayi tana nazarin kalamanshi sannan tace "Ina maka fatan Alkhairi Ali,Allah ya sanya Alkhairi aciki kuma Allah ya tayaka riko" Ameen yace sannan yamata sallama ya zarce gidan su budurwarsa safiyyah, tasha ado tafito tana yanga murmushin ta me kayatarwa ta kasheshi da shi sannan tace cikeda kirsa

"Honey Kayi kyau,ina wuni" kura mata ido dukta gama bugeshi yace

"Kema Kinyi kyau baby fiyya ya garin" kallonshi tayi cikeda kashe ido da shauqi tace "garin lafiya lau kawai dai idan bama tare ne ke warka ke damuna" hannunta daya ya rike "Haba my Sophie idan kikayi hakuri saura fa wata daya mukasance atare daganan kuma komai ya wuce" Murmushi tamasa tace "to ya zancen tafiyarka yola wurin Sha'awa?" Hannunta ya kuma rikewa

"Kina burgeni my Sophie sam sam bakida damuwa idan muna tare,yau zanje nadawo jibi" Murmushi tamasa "zanyi kewarka my Ali Allah ya kaika lapia yakuma dawo dakai lapia, gaskia zanyi kewarka" murna fall arasnhi yace "Nima zanyi kewarki my Sophie mu kasance a waya ko wane lokaci" da haka sukayi sallama,yana Shiga mota friends dinshi dasuke tare suka Hau ihu "Choo kaga jarumi mijin mata biyu wlhy ka burge ji yanda take tarayrayarka tamkar ba wurin kishi yarta zaka jeba,tunkan ayi auren kenan inaga idan akayi auren sekasha lygude da gata irin sosai sosai" kanshi ne yaji yana yunkurin fashewa a yangace yace

"Kune baku iya soyayya ba,ni a wannan zamnin idan ba irinaba gwarzon gwaraza wayannan Yanmata ne zasu yarda a daura musu aure da saurayi rana daya" dukan kirjinshi kabeer yayi yace cikin sowa

"Shegen sama,Wato kai baban soyayya ko,wlhy idan dai mata biyune gaka gasu,kasani ko iyayenmu dayar suke karewa da fitinar mata biyu" murmushin kasaita Ali yayi

"Kaga kabeer nifa basir bema cikiba tukunna da lapia ta kuma jini sosai yake yawo ajikina,sannan kuma gashi nidin babba ne awurin aikina inada,duk dukiya irinta mahaifina bata same niba,sabida na isarwa kaina,nidai kam da karfi na da komai ba ragon namiji ba bazan buge ga mace daya ba" dariya dukkansu suka kwashe dashi,Gamu gani kawai suka ce...

A yola kuwa tarba sosai wurin yar fulanin yola suka samu da mahaifanta atake aka tsayarda rana kasancewar damamahaifinshi yazo ya nema masa auren ta kamar handa ya nema masa na Sophie, acewar mahaifin Nasa baze tauye masa haqqi ba tunda kuwa yaji ze iya, murna awurin Aliyu zakin fama ba'a magana.

*Bayan kwana biyu*

   Haj Na'ima ce ta kalli cikeda nutsuwa tace, Aliyu wainikam dudu su shekarunka nawa? Talatin da daya fa? Dan Allah ina kai ina mata biyu? Nisam Banso Abba ya amince maka wannan shirmen ba wlhy" b'ata fuska yayi yawaniyi Kici kicin "Haba Aunty Na'ima nifa yanzu sam ba yaro bane ba,tayaya ma zakuce bazan iya rike mata biyu Ba wlhy nafi danan niba ragon namiji bane kuma inada halin yin hakan" rike baki tayi tana mamakin kalamanshi sannan ta girgiza kai

"Allah ya taimaka Aliyu ko a iya kalamanka na tsaya na tabbatar ka isa ajiye matan biyu" mikewa yayi rai a bace yamata sallama sannan ya bar gidan.

  Ranar wata jama'a aka daura auren Aliyu da Sophie a garin Kano,sannan da yamma tsirarrun mutane dashi angon suka hau jirgi zuwa yola inda aka daura aurenshi da yar mutan yola Wato Sha'awa...

*Hmm tirkashi muje zuwa*

    Safiyyah ce ta fara tarewa agidan Aliyu dake rijiyar zaki,inda dakuna biyune da ita acikin gidan kamar yadda aka ware wa Sha'awa nata itama sai parlor wanda atanan ne zakaje dakunan jikin gidan,atakaice dai dakuna biyu ne da parlor daya se dining area da kuma kitchen daya da store se backyard ko Wanne daki biyu toilet daya ne a tsakanin su,soyayya da kauna a dirza safiyyah da Aliyu har wani zatin yazago Sha'awa ta tare itama daganan suka zama su su biyu inda Ali zaki kejin kanshi wani Babba acewar shi duk a cikin samari ya musu zarrah tunda har ya aure mata biyu lokaci daya gashi yana samun kulawa tako wane bangaren,Aliyu ya kasance me yawa ita zuzuta matansa duk sanda suka  keb'e matsala daya samu itace dukkansu makissata ne,ba wacce ke nuna tana kishin yar uwata afili amma azuci tamkar su shaqe juna,Sha'awa yar mutan yola itace budurwar Aliyu ta farko kuma yana kaunar ta matuka,da wannan ta dukufa haddasa fitina a gidan

   Da sallamarshi yashiga dakinta dauke kanta tayi bata ansa shiba,zama yayi kusa da ita ya rikota yace cikeda rarrashi

"Baby na menene kuma? Yada kauda kai haka laifin me nayi" kwace cikinta tayi sannan cikeda fada tace

"Bazanji wani baby,har zakaje kaceda matarka wai ban iya girkiba,wai har kana cewa banda sarrafa fura ba'abinda na'iya to ai tazo ta sanar dani komai" Kallonta yayi cikeda mamakin kalamanta yace "Nid'in injiwa ya sanar miki wannan karyan?"

"Wakasan ka sanarwa banda wannan matar taka me kamada agwagwa aiyau tazo ta gorantamun hakan" cikin fusata yamike had'e da cewa "idan dai haka ta sanar miki bara naje na sameta,seta sanarmun sanda mukayi magana me kamada wannan da ita" riko hannunshi tayi cikeda kirsa tace "Ai hamma Ali ba haka yadace kayiba,bari zakayi idan mukazo cin abinci tunda nike da girki seka kodashi dakyau dakyau kace aduniya ba wacce takaini iya girki,ni wannan kadai zakamun nasan kana sona" dawowa yayi yazauna yace idan haka kikeso anyi angama yarfillo na". Ilai kuwa suna zama dining cin dinner Aliyu yace alomarsa ta farko

"Kai yarfillo na har Allah Allah nake girkin ki yazago sabida kawai naci wannan dadda d'an girkin naki,aduniya babu girkin daya kaimun nakinnan dad'i wlhy" narkewa tayi cikeda shagwaba tace "Hamma Ali girkina kadai kake wa zumud'i banda ni?" Cikin sauri yace "Haba mana yar fulanin usul harke mana yo idan kina kusa ina zancen wani girki?" Dadine yacika mata zuciya ta wani narke tace "Hamma Ali plss nazo kusa dakai ka feeding nawa,I really don't wannan feed my self" Murmushi yamata "sure 'yar fillo na" sadda kai safiyya tayi aranta tace "Dani kike zancen waike Fulani ko bazaki had'a ni da mijina ba,dage wa tayi cikeda karfin hali tace " Da wayana na kusa dana muku picture baku gankuba dan fillo da 'yar fillo sak" kunyace ta kama Ali ya mike yana Sosa keya.Koda girkin safiyya ya zago bata nuna masa komaiba se washe gari,ze je office tayi zamanta bata tayashi Shafa mai ba kazalika bata tayashi saka kaya da hula ba,bayan ya gama kimtsawa gaba daya ya kalleta batare daya saka necktie nashiba kazalika kuma be rufe igiyar shoe nashiba, yace "My Sophie wai meye haka ne? Haka kika saba yimun ne? Kallonshi tayi cikeda ladabi tace

" yazanyi natayaka yanda nasaba honey? Kaifa kace idan nakuma saka  kaji kunya acikin office naku sai kamun dukan tsiya,nikuwa bansan sanda na daura maka tie a baibai ba Kokuma sanda na daura maka igiyar takalmi ba dedeba" zabura yayi cikeda mamaki yace
"Baby na niyaushe nace miki haka kuma?" Tsuke fuska tayi ta tattaro kwallah cikin muryan kuka tace "Au yar fillon taka daka gayawa ne harka manta,ina cewa Kayi kullum Koda ba kwanan ta bane can zakana rika zuwa tamaka" cikin fushi yayi hanyar waje zeje ya samu Sha'awa, rikeshi tayi tace "Ina kuma zakaje honey?" A fusace ya juyo ya kalleta "zanje ne Inji dalilin Sha'awa na San hadani dake,seta sanarmun sanda mukayi hakan da ita" langwabe kai tayi tace "Haba honey aiba girman ka bane wannan my hrt,kawai kubarta kuma ni nasan bazata maka karya ba haka kawai"

"Kinga abinda yasa nace zan mata magana gashi harkin yadda" Murmushi tayi

"To ai kasan yanda zakayi ka saka na yarda bakace dinba my hrt, muje na daura maka agabanta nasha Yabo" fuuuu yabi iska yayi waje tabi bayanshi, wanka Sha'awa tafito,cikeda kirsa ta tsuguna ta gaidashi ya ansa cikin shan kanshi sannan yace "Lapia lau" ya kalli Sophie yace "my Sophie zoki daura mun igiyar takalmi na kuma ki sakamun tie kinsan fa idan bake Ki kamun tying tie nawaba da igiyar takalmi banajin dadi sam,wasu lokutan ma ba daidai akeyi ba" sosai Sha'awa ta shaqa da yake anfita iya kissa ta juyo a kufule tace

" ni kake so kace ban iyaba kenan ko Hamma" Kallonta kurun yayi yayi pecking Sophie ya wuce abinshi..

Mom nuaiym ce

Mijin Mata BiyuWhere stories live. Discover now