6 NEENA MALEEK

1.9K 122 15
                                    

Don't forget to votes..votes. ..votes...and comments.......

      6.
Maleek tell me  me kake so yanzu?, Aslam one things danake so shine karatu. C'mmon broth insha Allah..zakai don't worry....yanxu dai a kaya wanne kake so?, kuma wacce k'asa kake son zuwa?.
Hoo Aslam don't play with my mind ooo...I know u love me now..but don't take.......heeyyy Maleek u can speak English how comes?, oya tell me....Murmushi yai yace Aslam ina tare daku fa anytime kaga dole na koya..tunda ku baku magana saida turanci Bayan haka ma ai ina d'an zama kusa da class d'in ku...
Haka ne...amma ni ba wasa nake ba kagayan wacce country kake so kaje?, Makkah. Ok in Allah ya yarda zanyi wa Tattoo magana dama lokacin Umrah ne yanzu.....tnq Aslam....kagan ka Ya fad'a yana murmushi...tare sukaci abincin....kana sukai wanka. Aslam ne ya d'auko system nasa yana d'an latsawa..shikam Maleek Alquran ya d'auka yafara karatu.

*******
  Umma da sanin ki d'an ki yai haka kome?, bangane ba ina zaton agaban ki nai masa magana....da fad'a shine zakice da sani na..yo idan ma da sani na meye naki a ciki.
D'a ne ya mutu...anyi kuma rabon gado...wannan da muke ciki na kowa da kowa ne....bakida hurumin tada mun jijiyar wuya...Kuma maganar Aslam gaskiya ne da yace meyasa ba'a barshi ya nemo dangin sa ba...nayi kaico  da ban san wace Hajar ba..har ta mutu.
Wallahi da ni da kaina zan kaishi....kee ni kike gayawa haka?, kwarai kuwa na fad'a dan ke d'in ba macen arzik'i bace...iya biyayya ina miki....ni banyi zafin kishi ba na an mun kishiya sai kece zakiji zafi....ko Salma ai nasan kece kika saka dole ya aure ta.....idan kinason zaman lafiya kidena zagarmun yara.
Too nashiga uku....ya abubuwa suke faruwa ne haka?, batace komai ba ta fice...ko ita Salman da zatayi magana amma sanin masifa irin ta Umma yasaka tai shiru.
Ke Seema jeki gun Aslam kuce me zai ci?, yaci fa dan naga Indomie aka dafa masa..ok jeki huta...kai Kuma Taufeeq duk randa naga ka k'ara d'ora hannu a jikin Maleek sai naci uban ka....su suyi amma nadena kyarar sa.
*****
  Maleek kaban labari mana kai shiru....d'an kallon sa yai kafin yace Aslam banda labari....tunda ni ba fita nake ba...ok wai bakada aboki?, tab bansan kowa ba.
Ayya...sorry koh?. Turo k'ofar akai da ido suka bi k'ofar ganin waye zai shigo. Aunty Seema. Yes Ooo yan samari me kuka ci ne naji k'amshi?, abin dad'i mana. Maleek ko ka ragen?, Aunty na rage miki fa Aslam ya kwashe....ayya rabu dashi...Allah yai muku albarka kunji?, Ameen Aunty.
Yauwa kai namanta ina Khaleed?, eh eh...yauwa yana waje fa wai yazo...Maleek advice me ya zanyi?, Aunty gaskiya ki soshi tsakani da Allah Aslam kyakyawa ne sosai...yanada kud'i kuma yanada kirki....Mudai ki aureshi kawai.
Hmm Maleek banson tafiya na barka. Nasan da haka..amma dai naji ana wa'azi ace aure shine mutunci mace. Kuma kinga ai kinyi girma.....to ya zanyi Maleek yana so.
Kaje kuyi hira kafin na fito. Tom tashi yai ya fita...Aslam ne yace Maleek ka kula da kanka....insha Allah broth.
Inda motar sa take Matrix bak'a nan yaje....dan  nocking yai...khaleed dake ya ganshi lokacin da zai fito budewa yai.
Maleek ya kake?, lafiya lou Ya Khaleed...ya Exam kuma fatan komai normal?, wallahi normal yaya.
Masha Allah....Ina Auntyn ka?, tana nan fitowa...plx Ya Khaleed ka rike Aunty da daraja...tanada kirki...batada hayaniya itace farin ciki  na. Insha Allah Maleek ina son Auntyn ka sosai banda burin na wulak'anta ta fatana ta Soni muyi aure kuma. Zata so ka kaji..gata nan kazo muje sitting room ka zauna kafin tazo.
"Tafiya sukai...ni bara nashiga gida..Tom Maleek sai gobe koh?, bye bye.
  Khaleed kallon Seema yai sosai tabashi dariya yace Seema wannan cin maganin fa?, baki ta tab'e daga can kuma tace ai nacin naka ne yai yawa kuma ma yaushe ka ganni harda zakace wani saina aure ka kai tsaye?, calm down yammata nifa na jima ina son ki ba wai a yau kawai nagan ki ba....plx Seema ki soni wallahi ina k'aunar ki....Kuma zan yi k'ok'ari na cika miki burin ki akan Maleek.
Ki yarda dani kinji?, hmm nifa banson sweet mouth....aure kamar takura ne a guna...dan bazai bari na cika buri na ba..amma idan ina haka I can do what ever I want...without anything....nasan darajar aure akwai lokacin da fita zata kamani akan lamarin Maleek indai ban tambaya ba ba inda zani..amma kaga idan ina free ba ruwa na zanyi yadda nake so ne..
Seema darajar mace d'akin mijin ta...Kuma nayi alkawari tsakanina da ubangiji duk wani abu daya shafi Maleek zan lamunce miki shi...ke koda baki nan ni zanyi k'ok'arin ganin yasamu abin..kodan na cika burin masoyiya ta.
Kallon sa tai sosai...babu ma kusa a tare dashi...Indai haka ne ina maka murna samun soyayyar Seema cikin ruwan sanyi...Maleek shine buri na...dalilin sa yasaka nake karatun low a school..Kuma Alhamdulillah karatun nawa yai albarka dan bantab'a samun problem ba...yanzu haka ina matakin k'arshe na Masters d'ina....banson aiki amma duk randa aiki yakama akan Maleek zanje nayi sharia da kowa ye.
Good mata ta. ..na tayaki murna Allah kuma yasawa zaman mu albarka. Ameen tace sosai ta sake dashi sukaita hira har wajen 10 na dare saida ta kalleshi tace halan kayo sallama tundaga gida ne?, sallama kamar yaya?, eh naga bakada alamar tafiya ne...dariya yai sosai yace yanzu zan tafi.
Rakoshi tai har inda ya ajiye motar sa...kana ta juya. Bata kai ga shiga ba tajiyo maganar gate man d'in su...Hajiya gashi yace abaki...kallon hannun sa tai leda ce guda biyu mai tambarin Jifatu.
Amsa tai tashiga gida.....Ya Seema wai ina kika shiga ne?, ina waje..ido suka bude gun saurayi?, eh menene...kai amma naji dad'i sosai ashe zamusha bikin zata ai ba zakiyi aure ba...ke Amrah Rufan baki uwayen gulma...garama Afrah wataran amma ke hmmm.
Dariya sukai sosai...Umma ce tace Seema nai murna koda yake da alama Maleek ne yasamo mijin?, kamar kinsani kuwa...mts ai kedai kamar ba nono na kika sha ba..gashi Aslam ma kin janye shi ohh naga jaraba.
Umma naga d'azu akan sa kikai fad'a yanxu kuma tsanar ta dawo?, uban ki nace...dariya sukai mata sabida suna son Umma kodan jarabar ta.
Aunty halan wani mai Matrix ne....kyakyawa?, eh shine dan yace mun yaga wata mai kama dani sosai...yama zata nice sai kuma yaga ni nafi k'iba akan ta...nace to ko Amrah ce ko Afrah....ashe kece.

*********
Life move on. ....Allah yana taimakar bawan sa be a duk alokacin da yaso....Aslam da Maleek shak'uwa ce a tsakanin su kamar me.
Komai tare hatta kaya ma iri d'aya suke sawa....idan an magana ya d'akko wuk'a yace zai dab'awa mutum.
Duk yarda Kaka da tsinanun yaran ta har ma da k'anwar ta uwar Saratu suka so k'ara musgunawa Maleek abin yaci tura...dan hatta Umma ta canja musu sabida itama tana zargin wasu abubuwa a tsakanin su....Amma yar k'anwar tace dole ne taso ta akan ta...hmm oh ni Umma Allah ka yafemun tai ta cewa.
Rayuwa ta saiya Su Tauheed suna koma school...dama a Egypt suke karatun su..Sai kuma Amrah da Afrah wad'an da suna ABU Zaria  acan suke karatun su.
Seema cikin wata ukun nan an kawo kud'i ansaka rana...biki kuma zai kai wata uku..amma idan kaga shirye shiryen da ake kaikace bikin wani satin ne.
A b'oye Khaleed ya kai Maleek ya zana jarabawa ta Jamb....wadda waje mabanbanta suka zana tare da Aslam.
Masha Allah komai fa yai daidai dan kuwa sun sami mark daidai da yadda ake so.
Baba yau tun safe ta tafi katsina wajen bokan ta akan Umma...saboda taga yanzu tafara sauya wa..Dole a d'auki mata ki a kanta.
Kuma daga nan zataje WURMA gun Cancanke akan ko da Umma tazo kada yabata maganin komai dama sune suka kaita.

Auta ce

    

NEENA MALEEK     {COMPLETED}Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang