*LU'U LU'UN SARAUTA*
Hawwadamary
(NWA)
1
بِسْــــــــــــــــمِ اللَّهِ الرَّحْمَ الرَّحِيْم.......K'asar *LU'AL BIYAl* k'asa ce mai matuk'ar girma da yalwal mutane da Aljanu wad'anda adadin mutanen zai haura miliyan d'ari,Aljanu sama da miliyan d'ari biyar sun linka mutanen cikin k'asar sau ukku.
K'asar a rabe take kashi biyu sakamakon rabuwar addini wanda rabi da kwatansu Suna bauta ma gumaka wasu kuma wuta wasu dabbobi wasunsu ma itatuwa suke bautamawa.
Yankin*K'URUZUN NAJ* sunan ya samo asali ne daga sarkin yankin nasu wato *Sarki K'arkil K'usumi*. Mutanan yankin sune wad'anda basu da tsayayyen abun bauta.
Saii d'ayan yankin cikin k'asar ta lu'al biyal Suna kiranshi *DARUL ISLAMA* wanda duka mutanen yankin musulmai ne babu kafiri ko d'aya, *Sarki Sharahudden* shine sarkin wannan yanki nasu na musulmai.
Sai dai k'asar Lu'al biyal tana da wata masarauta mai matuk'ar girman gaske harta masu aikin cikinta ba zasu iya iyakance girmanta ba,akwai dukiya mai tarin yawa wanda zata ishi mutane sama da miliyan goma su fara rayuwarsu Suna d'iba kullum har su gama rayuwarsu ba tare da ta yi qasa ba,hatta fadar masarautar yafi girman gari guda kujerar sarautar kanta da Lu'u lu'u akayita,sai dai yau sama da shekara d'ari kenan rabon da a bud'e masarautar ko wani mahaluki ya shiga saboda a shekaru d'ari da hamsin da suka wuce anyi wani Sarki azzalumi wanda bai san komai ba sai tsafi da zalunci,shi wannan Sarki mai Suna *ZURURAL HAR* bai ta6a haihuwa ba, ya auri mata sun kai d'ari biyar amma cikinsu babu wacce ta ta6a ko da 6atan wata ne gashi abunda yafi damunsa bai wuce rashin mai gadon kujerar sarautar ba bayan ransa haka yasa ya k'ara rud'ewa da son haihuwa duk matar da ya aura yaga tayi shekara bata haihu ba sai ya sa a tafi da ita bayan gari gaban wani tafkeken kogi a yanka ta a watsa jininta cikin tafkin gawar kuma a jefe ma y'an ruwa,wannan yasa kowa ke tsoron Aurensa,yakai ya kawo iyaye masu yara mata suke 6oye yayasu cikin gida amma duk da haka basu tsira ba
Sai ya koma baza amintattun hadimansa mata cikin gari Suna yin 6adda kama su shiga gidajen mutane da niyyar sunje a samminsu ruwa su sha, a haka suke diba masa a fakaice duk gidan da suka ga budurwa basu cewa uffa suke komawa ga Sarkin Sarakai su sanar dashi,shi Kuma ya aiko a kame masa masu gidan duka a gaban iyayen zai maida d'iyarsu matarshi daganan su kuma ya maidasu bayinshi, su kuma mutanen k'asar a lokacin babu musulunci basu san suyi addu'a ba sai suka duqufa rok'on abun bautarsu maimakon abu yay sauk'i saima ya rink'a yin gaba-gaba.
Shiko Sarki Zurural har koda yaga ya shafe lokaci mai tsawo yana haka kuma ba wani ci gaba sai ya d'auki alwashin daga shi babu wanda zai k'ara sarautar k'asar ta dad'i sai wanda yasha wahala sosae fiye da wadda yasha lokacin da yake tara dukiyar masarautar.
Ananan-ananan wata rana ya yanke shawarar yayi ma Lu'u Lu'un dake tare da hatimin Sarki mugun 6oyo sannan ya tsafe kujerar sarautar yanda duk Wanda ya hauta ba tare da ya nemo *Lu'u Lu'un Sarautar* ba Wanda a jikin kujerar ake ajje shi to nan take zai mutu zai shafe a doron k'asa. Tun daga wannan rana ya fara yi ma kujerar6 Sarautar mugun tsafi har sai da yay shafe tsawon shekara d'aya yana yi kafin daga baya ya tada wasu amintattun aljanununsa guda dubu hamsin ya basu *lu'u lu'un sarautar* yace su tafi su 6oyeshi suyi masa mugun 6oyon da ko su yace suje su d'akko ba zasu iya gane gurin da suka ajje ba.
Suka amsa suka mik'e hanyar daji sunata famar keta muggan manyan dajuna sai wajen dare sannan suka samu guri suka ajje saboda matuk'ar had'arin gurin da suka ajje har d'aya daga jikinsu ya mak'ale a wani guri,sukay sukay su fiddo shi suka kasa sai kawai suka tafi suka barshi yana ihun neman agaji,lokacin da suka isanma Sarki Zurural Har da batun sun cika umarninsa sai ya kwashe da wata mahaukaciyar dariya tare da buga sandar dake hannunsa take gurin ya gauraye da hayak'i sai kuma 6at duka Aljanunnan suka shafe ya kashe su baki d'aya,juyawa yay ga kujerar ta Sarautar ya shiga wasu surutai wasu abuguwa ne masu kamar macizai suka dinga fitowa daga jikinsa Suna shigewa cikin kujerar,yafi sama da sa'a ukku yana haka kafin ya daina gabaki d'aya tsafin daya mallaka duniya sai da ya k'arar dashi a kujerar sannan ya buga sandar hannunsa shima nan take ya fad'i matacche,kafin kace kwabo tuni k'asar ta Lu'al biyal ta cika da labarin mutuwar sarkin nan aka shiga walima ana murna,washegari da safe aka d'auke shi aka kai bayan gari aka saka shi cikin akwatin lu'u lu'u sannan aka jefa cikin rafin nan da yake sawa ana jefa matansa tun daga lokacin Alummar k'asar Lu'al Biyal suka maida ma kogin Suna *ZURAL HAR* daga cikin sunan ZURURAL HAR.....
Lu'u Lu'un sarauta zai cigaba da zuwa muku kowane sati in Sha Allah,karku bari a baku labari....
YOU ARE READING
LU'U LU'UN SARAUTA
AdventureSun kasance masu neman Sarautar Lu'al Biyal wannan yasa suka fita neman Lu'u Lu'un Sarauta....