01

8.8K 434 7
                                    

TSOHON LITTAFI NE, AKWAI TYPING ERROR SPELLING MISTAKES AND LOT 🙂


©®Hakkin mallaka nawa ne ni Khadeeja Candy, ban yarda a sarrafamin labari ta kowace siga ba balle har a dorashi a Website ko YouTube ba tare da izinina ba, yin hakan kuskure ne babba domin zai iya janyowa mutum matsala saboda haka a kiyaye

_________________________

Da sauri sauri take tafiyar ganin unguwar babu mutane sosai ta tada kai ta kalli sama sai ta kara bata fuska ganin hadarin daya lullube garin!

Bata ankarava taji an sako da ruwa mai karfi nan da nan ya fara jikata da gudu ta nufi wata bishiya dogon yaro tafake aiko ruwan kamar ita suke jira suka kara karfi!

Kankame jikinta tayi ta bata fuska kamar zatayi kuka

Ruwan suka cigaba da zuba harda kankara duk sun jka mata kaya

Wata kafirar mota ta wuce ta gabanta sai kuma naga tayi reverse ta dawo daidai inda take tsaye ta tsaya!

Ahankali naga ana sauke glass din motar ni khadeeja candy nace"Allah gwanin iya halitta"

wani kyayyawan saurayi ne na gaban kwatance da bazai wuce 33 yrs ba na gani a driver seat!

Fari fes mai manyan ido da dogon hanci akasan hancin an yanka masa madaidaicin bak'i!

Cikin sanyayyar murya mai taushi naji yace"my dear deenah shigo" kallonsa da yaga ta tsaya masa ne yasa yace" plz shigo mana kar ruwan ya kare a kanki"

Tattaro rigarta tayi mai kamada ta indiyawa ta shiga tare da rufe ganbun motar!

DEENAHWhere stories live. Discover now