10 NEENA MALEEK

1.6K 125 2
                                    

Baiji karan tahowar kowa ba saiji yai an yi hugging nasa ta baya....Seema ce hawaye sosai take nason k'anin ta Aslam ma tahowa yai ya rungume su duka daga nan saiga Afrah..Amrah..Tauheed and Taufeeq dukkan su nan kuwa masu hoto sukai musu caa anata d'aukan su pics Maleek kam gam ya rike Seema..is ok Maleek kanason nai ta kukan kenan? No Aunty...if ba kaso to kai shiru.
  MC ganin yan gida d'aya ba saiya saka wak'ar zumunci ba..aikam Aslam rawa Maleek dai saidai a jashi Tauheed duk sun manta tsanar da sukai masa kaf d'in su jansa jikin su sukeyi..Afrah ma hannun sa takama itada Amrah suna D'an small dance mana let's us kwaso shoki nan kuwa aka saka musu shoki....tun yanajin kunya harya ware sukaita rawa itakam Seema komawa tayi.
Everybody in the place saida suka basu sha'awa..
Anyi taro lafiya an k'are lafiya inda aka d'aura auren washe gari akai kai amarya katafaren gidan ta dake Tarauni.
  Zaman su zamane na amana da yarda da juna shi yake kaita school ya kuma d'akko ta. Maleek kusan kullum sai sun had'u a school.
Baba dai tagane gaskiya inda ta ringa masifa da balai akan yadda suka Haince ta har Maleek yai primary gashi kuma a matsayin d'an university.
Tayi kuka a d'aki sabida tabbas mai ilimi dole ya gano ina iyayen sa suke...yanxu ita ya zata yi?, tuno maganar bokan ta na China da kuma  Italy  inda suka cemata babu yanda zaayi dangin Kakar Maleek su yi tunani akanta indai ba tadena aske gashin jikin ta ba...ko kuma shi Maleek d'in ya had'u da wanda yake dangin uwar ne.
To daga nan ne fa tunanin kowa zai dawo kan ina take ko ina jikan su yake da d'an su?.
Da wannan take jin kwanciyar hankali  tasan tabbas gaskiya ba zatayi halin ta ba.
Umma dake yanzu ta saduda tadena zuwa gun kowa Istigfar da hailala shi take yawaita yi....Maleek kam babu ruwan ta dashi tadena masa komai na musgunawa hakan ba k'aramin tada hankalin Baba yai ba ganin ta za'a had'a baki ne asan gaskiyar magana.
Su Amrah dai suma duk wata tsana da suke ji akan Maleek yanzu ta kau..dama can Tauheed yana sonsa makirci ne irin nasu Baba.
Karatu sosai sukeyi ba kama hannun yaro kullum cikin research suke dan ma Aslam akwai shi da son yammata da kuma driving d'in ganganci wannan halin nasa shine yake ha d'ashi da Maleek d'in.

5 YEARS Later.

Acikin wannan shekarun anyi abubuwa da dama inda Allah ya sauki Seema yabata yaro namiji daga shi sai mace...Zaman ta da mijin ta zama ne na yarda da juna yana kula da Maleek sosai da sosai.
Amrah da Afrah sungama school anyi auren su a shekaran da ta wuce...su Taufeeq da Tauheed ma sunyi aure komai kuma tubarkallah yana tafiya daidai Maleek bayada damuwa ko kad'an.
Damuwar sa d'aya a kullum ta mafarki ce...wadda a da yanayi amma ba sosai ba to kwanan nan sai abin ya yawaita yana mafarkin wata farar mata wadda suke kama sosai da ita tana ce masa nice mahaifiyar ka ina nan zuwa gareka kaci gaba da hak'uri wataran sai labari.
Wannan shine damuwar Maleek amma bayan haka bayada wata damuwa ko d'aya...tunda kowa na k'aunar sa.
Tauheed yana sonsa suna zuwa gidan sa shida Aslam matar sa mai kirki...yar Ambassador ce sun had'u a Egypt ita taje ganin Doctor tunda ga nan soyayya ta shiga tsakanin su harta kaisu ga Aure.
Afrah da Amrah 'yan gida d'aya suka aura gida Jen su ma kusa da juna ne....Taufeeq yar uwar Umman sa ya aura itama yar masu kud'i ce.
Isma..Baba..Amma kullum cikin hanya suke akan Allah ya tarwatsa Umma dan itace matsalar su yanzu....tunda tak'i saka baki yaran ta side na kula Maleek.
Maleek sungama degree d'in su yanzu haka suna Service d'in su a wata makaranta mai suna Tijjani Usman dake Goran dutse.
Seema tagama masters d'in ta tazama full house wife...yaran ta suna son Maleek ganin yadda yake son Maman su dan kullum yana gidan anan yake cin abinci..ko unguwa zata shine yake kaita indai basuda lecture a lokacin.
Maleek saurayi ne cikakke wanda a ko'ina akace ana neman saurayi cikakke kyakyawa to idan har aka samu Maleek an k'are magana.
  Karatun sa shine komai nasa...yammata baisan su ba dan kuwa tunda yake a rayuwar sa baitab'a kallon wata mace ba har ya d'arsa a ransa wani abu. Baya zuwa kowanne party saidai Aslam yaje....biro da paper sune gatan sa.....Yammata suna son sa amma babu wadda ta tab'a samun damar yama kalle ta bare tace har taji muryar sa.
Tun shigan sa har gamawar sa baitab'a d'aukan second class ba sai first....kowa yasan shi da k'ok'ari he's smart and talented.
Aslam yanajin dad'in yadda Maleek yake rayuwar sa...shima yana k'ok'ari dai amma Maleek is the highest.
Malamai kowa yace Maleek....yaran manya kowa harka yakeson yi dashi amma babu fuska....su ganin su wai jan aji yake shikam a nasa tunanin hakan shine daidai tunda bayada gata gara yai rayuwar sa da wanda yasan su suka sanshi.
Afrah kullum yaje saita masa tsiya kai yanzu ko 'yar budurwar nan bazakayi ba haka zaka zauna? , shikam saidai yace to Aunty Afrah me zanyi musu....ni zan iya rayuwa ta ahaka dan bansan mai mace zata mun ba....itakam kallon sa kawai take idan yace haka tasan akwai lokacin da zai so mace har yai kuka akan ta.
Seema har gida ake zuwa  waidon ayi kamun k'afa  a gunta Maleek yaso su itakam cewa take to bari yazo idan yanaso fine.....idan tai masa magana ranar yaringa fushi....shi bayason kowa ba ruwan sa da kowa...itama dai saidai tai murmushi.
Haka rayuwa take tafiya....mijin ta kam su Baba basa sonsa itada yaran ta kaf saboda baya barin su yiwa Seema tsawa a gaban sa...har cell wataran yace zai kulle Halima akan tace sai Maleek yabar gida dan ba d'an sunnah bane...Seema tai magana aikam mari ta zuba mata tana tsine mata yana zuwa Seema tafad'a masa nan yaringa masifa tun daga wannan lokacin basa sonsa suka tsane shi sosai ko gidan ta basa zuwa....Baba tafi kowa tsanar Cell saboda akan shiga cell rayuwar ta taso tarwatsewa...
  Life move on yanzu su Maleek sun k'are bautar k'asar su....Inda Aslam yace kada su zauna kawai su juya Masters haka akai kuwa nan suka duk'ufa karatu baji ba gani. ...mafarkin matar nan kuwa a kullum sai yayi shi baitab'a gayawa kowa ba saidai yanajin dad'in hiran da matar ke masa takan ce masa ina nan gareka mahaifiyar kace ni wataran zamu ga juna....sun lalata min rayuwa ta sun rabani da kai sun raba yar uwata da d'an ta sai sunga k'arshen su....Akan kud'i suna son halaka kowa to ta Allah bata suba.
Shi bai gane maganar saidai yaita d'aga kai.....dan baisan komai akan maganar da take ba....saidai yaji maganar kawai.
Halima kuna sane da cewa Maleek girma yake kuma karatun sa ya mik'a?, ina gudun b'acin rana ina gudun ranar nadama. ....rayuwa ta zata salwanta ne duk ranar da gaskiya ta fito.
Ranar da gaskiya ta fito ranar kuma taku rayuwar zata lalace. Ranar da gaskiya tafito duniya zata kalle ni tai mun atishawar tsaki ne....Umma da yaran ta zasu zama babu ni babu su.....haba Baba kidena wannan tunanin indai muna raye bazaki wulak'anta ba..su d'in wa akan Maleek kawai?, hmm Saratu kenan ba akan Maleek kawai ba....kema bakisan komai ba amma wataran zan gayamiki.
To nidai kidena wannan tunanin mu bazamu bari rayuwar ki ta lalace ba...saboda haka Italy zaki koma yak'ara aiki akan wanda yayi kodan ki samu kwanciyar hankali....haka za'ayi kuwa sai kiyi waya a sama min visa zuwa nan da kwana bakwai sai naje...Tom hakan za'ayi.
Da wannan hiran suka tashi amma fa kaf maganar da suke a kunnen Umma wadda tazo shigowa d'akin.....hmmm yakamata nasan gaskiyar da kike b'oyewa muguwar tsohuwa...to ne zataje yi Italy?.

Muje zuwa ....plx votes and comments ❤#AnaTare.

NEENA MALEEK     {COMPLETED}Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin