Bayan gidan ta nufa tana karyo kwana ta fara hangensa still yanda ta ganshi dazu saidai wannan karon kwanar da ta fito yake kallo kamar wanda yasan da zuwanta,
Da gudu ta karaso inda yake sai hak'i take,
Ido ta kuro masa kamar mai tunanin abunda zatace ta kalli tagar dakinta sannan ta kalleshi cikin fuskar tausayi tace “dan Allah kai wanene ya kayi kasanni may kake nema a gareni” juyarda fuskarsa yayi ya maidata right side yana duba agogon hannunsa kamar mai jiran wani, ta dawo side din da fuskarsa take ta hade hannayenta tace” plz n plz ka fadamin abunda na tambayeka koda kai aljani ne wlh zan raurareka” sai alokacin ya dago ya kalleta yana murmushi yace ” ni ba aljani bane ni muttun ne irinki saidai kuma kince bazaki sake tambayata ba ko kin manta ” ” kabar zancen baya kawai ka bani amsoshi na karka rikitamin kwakwalwa “, wayarsa tayi kara alamar sako ya ciro ya duba sannan ya bude motarsa ya dauko wata leda ya mika mata murza yatsunta ta shigayi tana kwankwanton karba yace ” duk amsoshinki suna nan gurin dan haka karbi kawai”!!
Kamar wata karamar yarinya ta zama tana shafa hannayenta a rigarta kamar mai goge abu tace ” inna karba bazan bata ba “? yana kallon saman kanta yace” yan gidanku na kallon ki zaki bata! ” tunani ta dan shigayi sannan tace ” kamar ya ban ganeba ” ? Ratsewa yayi gefe ta hango su zainab da zara tafe da saurinsu ” cike da tsoro ta kalleshi tace ” ya aikayi kasan zasu zo “?
Baice da ita komaiba ya duka ya aje mata ledar gabanta ya shiga motarsa!!
YOU ARE READING
DEENAH
RomanceThe beginning of another life. suspicious, terrified, remorseful. DEENAH...! ®2015 NOT EDITED ⚠️