17 NEENA MALEEK

1.5K 83 3
                                    

Na
Re@l Autar hajiya

17

Suna tafiya wajen almajiran nan NEENA tayi....Bata tsaya komai ba tace musu gashi su raba tana basu tayi gaba suka wuce.
Aunty Mimi dai dad'i taji ganin lallai k'anwar tata good girl ce. Zagaye sukai sosai sune har jakara daga kwari drivern Aunty Mimi yasan gari shine ma yake kaisu kasuwanni ..Aunty yanzu ina mukai?, ba BUK kika ce zaki ba?, eh yauwa nan kuwa..to ai nan zamu.
Tafiya drivern yake Yazo dai dai wajen da zaiyi kwana itakuma Seema tazo tsallakawa dan shiga motar ta baikula da ita ba ya kwashe ta....da gudu suka fito kafin jama'a su taru Aunty Mimi tasamu sun kamata sun sata mota....wani asibiti ne mafi kusa da nan?, NEENA wallahi bansani ba nikaina ba fita nake ba yanzu ya zamuyi?, Hajiya ai kawai mu koma hanyar gida akaita wani HUAZHONG naga ana zuwa sosai....ok yi sauri muje.
Gudu yake shararawa nan da nan suka iso...karb'ar ta akai da gaggawa akafara dubata inda Allah ya taimaka tsagewar kashi ce kawai sai kukkujewa.
Zama sukai saidai shiru bata farka ba..Jakarta Aunty Mimi  ta d'auko wayoyi ne manya saidai kaf akwai lock jikin su  Allah yasa akwai karama a ciki nan ta d'auko dubawa tayi taga sunan Boy shine last call nata  NEENA ceta karb'a ta kirashi.....suna zaune jugum..saijin banko k'ofa sukai...saida ya shigo kuma sannan yai sallama ganin mutane a wajen.
Assalamu alaikum Aunty inalillahi meya sameki waya kade ki waye shi baya gani ne ko kuma bai iya driving d'in bane?.
NEENA cikin sanyin murya tace afwaan Malam bada niyya bane kuma da daniyya ai bazamu kawota asibiti ba har mu maka waya ku ringa uzuri please.
Juyowa Maleek yai ya kalli mai maganar fuskar ta a rufe take amma saiyaji muryan ta so sweet wani abu da bai tab'a ji ba ya ziyarci zuciyar sa..kasa magana yai illa jan kujera da yai ya zauna kusa da Aunty.
NEENA zakici abinci Aunty Mimi tai maganar itama k'unshe da niqab?, no Aunty zan jira naga jikin matar nan yadda zai...aa NEENA kadafa Dadan ki yace nabar ki da yunwa kubar ni da amsa query dan kalla kiga tun 1 muka fito yanxu kuma 5 saura...don't worry Aunty zan jure koma naje gida Ruman nakeso da apple sai hanta zallah....kanta ta dafa  tace Allah yamiki albarka...Ameen Aunty na.
Shiru sukai shikam haushi cika Maleek yai ganin wai riritawa ake bayan ga Auntyn sa a kwance...suna zaune Ya Khaleed  yashigo mijin Aunty.
Baice komai ba illa dai jajantawa da yayi kana yai godiya akan kawota asibitin da akai.
Sai da Yayar Maleek tai awa biyu kan ta uku kafin ta farka...muna zaune shiru shikam yana ganin farkawar ta da sauri suka mike shida mijin ta...sannu Aunty sannu ina ke miki ciwo?.
Maleek ba inda kemun ciwo nasan buguwa ce ma tasaka aka kawoni amma I'm much fine jikina garau, murmushi yai anya Aunty kidai ce da sauk'i amma ba kamar yadda kike nunawa ba?, hmm ancemaka ni kaine mai rakin ciwo?, Aunty kenan raki sai dan gata wanda bayada gata ina yaga wani raki ko shagwaba?, wanda baitashi a matsayin komai ba taya zai ce zaiyi abinda masu komai suke kawai dai ke d'in dai ke ke shagwaba ni keda Yaya.
Hannun sa ta kamo tace nagayamaka kadena cewa kai ba komai bane...wataran zaka zama komai indai Auntyn ka na raye.
Hawaye ya goge yace Aunty banda bakin gode miki lokacin da aka bugo min waya wai kinyi accident baki ji yanda naji ba...nafara kuka nace shikenan uwata..ubana...Yaya ta...aboki yata....zata tafi ta barni..banda kowa saike idan wani abu ya sameki sainaga laifi nane keda kike ban lokacin ki amma gashi ni ban baki nawa ba har wani abu ya sameki.
Maleek kadena cewa haka idan kuma kasake wallahi zanyi fushi dakai...nima zanyi fushi dashi ne wallahi mu d'in nan mun zame maka iyaye kodai baka son mu shiyasa kake son canja wasu?.
Dariya ya sanya yace Aunty kinji mijin ki koh?, najisa ai nima tunanin dana fara kenan....ko kasami dai budurwa shine kake kame kame?.
Baki ya riqe Aunty ina ni ina budurwa abunda ban tab'a sha'awa ba....wace zata auren a haka?, zamana a haka yafi mun tun kowa baisan asirina danake rufe wa ba shiyasa ba ruwa na da aboki bare yasan waye ni wataran rayuwata xata kare ne a kula dake da kyautata miki.
  Maleek zakai aure insha Allah....kama dena cewa haka kaidai kawai ba kasamu maison ka ba...amma akwai time.
  Tausayin sane yakama NEENA tafara tunanin wannan kyakyawan Saurayin number one ne ke cikin wannan halin.
  A zuciyar ta kuwa cewa take tasamu mijin aure dan tun shigowar sa taji wani bakon al'amari a tare da ita.
  Aunty Mimi  ce tace sannu koh...Lah sannu mun barki muna ta zuba angode fa. Aya ba komai naga qanin naki naji dake kamar me...ohh Maleek haka yake.
To kai banda abinda ya za'ayi kace bazakai aure ba nikam da ina ganin ka harna maka mata yanzu kuma.
  Dariya Auntyn Maleek tayi tace to kaji an maka mata ma ya zaayi?, tab anty yoni wai wace zata Soni ina nasan yazanyi hiran ma bare ace har aure....NEENA kam ita Dariya ma yake bata ace kamar sa baisan komai ba to waye shi ma dai?.
Hmm nidai nace nabaka qanwata saidai idan baka son tane?,  yo kunsaka wnn abin taya za'a kalle ku ma?.
  A haka dai nabaka NEENA...itama Auntyn Maleek da dariya tace nima nabata Maleek....shikam mijin Aunty cewa yai lallai daga gani wannan had'in yayi NEENA MALEEK.
Wow sunan kuma fa ya hau NEENA MALEEK to Allah ya biye bakin mu....dariya yai yace Aunty kenan ke nufin ki duk wadda taji waye ni zata aure ni?,  tsawa Aunty ta da kamasa tace u ar not serious wallahi kai d'ane kamar kowa kuma kowa yasan waye uban ka name zaka dameni da wasu zancen banza fice nan nadena ganin ka.
  Shiru yai yakasa cewa komai baizata Aunty zatayi fushi ba....wai Maleek ba dakai nake magana ba nace ka a kuce kaje gun iyayen naka tunda ka raina abinda nake maka out I said.....tsugunawa yai yakama k'afar ta Aunty kiyi hak'uri banzata.....Maleek ka bakace daga gabana wallahi zan bar maka d'akin idan baka fita ba.
   A hankali ya mike yana waigowa a haka har ya fita....Seema baida ce kiyi masa haka ba kinsan......Plx Khaleed  barni dashi bayada hankali wallahi natsani naji wanann maganganu saikace kansa farau ko k'arau.
  Naji amma kinsan halin sa dai gara ya bata da kowa akan ki pls kiyi masa afuwa matar arziqi kanta ya shafo yana lallashi. Hmm rabu dani dashi idan ba haka ba wallahi a haka zaiyi rayuwa....dan shege ma yake aure bare me uwa da uwa da yan uwa...
   Kinga kiyi hak'uri kinsan kowa da irin halin sa ai hakan da kike shine zaisaka yaji yatsani auren tunda a kansa kike masa fad'a.  Nan sukaita bara baki kana tace ya shigo.
  Magana yake mata a hankali yanda ba wanda zaiyi itakam NEENA kamar a kunnen ta ake....duk taji komai.
Tashi sukai suka tafi sabida Aunty tafiyar ta ba yau ba...sallama sukai musu sukai juya.
  Wash Allah azaba Aunty zan mutu...waih wannan rayuwa ta niqab ko.wahala?, dariya Aunty Mimi  tasaka tace NEENA kece fa kikace mu saka dan kada a gane mu baki ji ba ba yana rabona da driving wallahi tun a London bakifi 4 years ba amma kinsaka na wahala...drivern namu kin tura shi d'auko mata mota mu tsaya yazo kink'i saida muka taho..
  Ga dan bazan go slow kamar me?, saida nace  mu dakko GLK kika k'i gashi nan duk mun wahala.
  Hmm Aunty gaskiya rayuwa  akwai dad'i. ..wato mata ma masu driving kansu suna ganin sun gaji da gayu ashe yan wahala ne?, aikam dai NEENA nidai ban k'arawa.
  Aikam Aunty Mimi zaki k'ara dan wallahi nidai wanccen Maleek d'in zan so ban fara sonsa ba amma naji a jikina zan soshi.. 
  NEENA kenan kina tunanin Abba zai baki wanda bayada asali ko zaibaki miskinine?, wasa ne kima canja tunani.
  Haba Aunty inaga kowa Allah ya yishi bakisan waye shi ba dan kinji yana fad'an haka..gaskiya nidai kada kimun haka kibari kiji labarin sa kafin ki zartar da hukunci.
Tom yar gidan Dada zan bari kada kisa a ce kidawo dama da qyar aka ban ke. Hmm Aunty akai musu kayan abinci mana.
  Tnx qanwa banyi tunanin haka ba...waya Aunty ta d'auka ta kirawo wani tabashi adress na asibitin da d'akin tace akai musu lemuka kayan tee manyan tins da kuma swan water da take away na Dalal saboda tafi Gane abincin can.
  Suma suna zuwa gida wanka kowacce tashiga akan suka dauro alwala ana sallah ko abinci basu nema ba suka hau gado sai bacci.
Basu suka farka ba sai wajen Isha'i..har lokacin mijin Aunty Saky bai dowo ba.
  Acan ganin ana shigo da kaya kamar hauka yasaka suka tambaya anya ba makuwa akai ba?.
Oga nan akace mukawo ba kune NEENA MALEEK ba?, hhh mune ma da kansu tunda ka fad'i haka mun gane amma kuce hakan bai yawa ba?.
  Ba yawa a nan sunce zasu dawo ma anjima, to shikenan angode fita sukai sukuma sukafara duba kayan daga gani kasan naira tayi kuka dan gaskiya komai mai tsada ne na k'arshe wasu abin ba basu tab'a sha ba.
  Gajiya bata barsu sun tashi ba sai wajen magreeb dan iya gajiya NEENA tagaji ita bata tab'a gajiya haka ba a duniya ma....dolen ta ta tashi dataji ana kiran Sallah.
  Wanka tayo da alwala sallah tayi a d'akin kafin ta zabo kayan da zata saka wad'an da aka kamata su wajen kala 20 daga gun d'in ki simple doguwar riga ce dan bata iya d'aura zani ba...shiysa tace ai mata gowns kawai.
  A'a NEENA yar Dada baki bari anzo an d'auko miki kayan ba?, haba Aunty nace miki fa inason rayuwa kamar kowa bansaka da komai ba inason koya.
Kinsan gobe fa zata fara zuwa mai koyan girkin naga ba wani hutu da zanyi tunda danshi na biyo ki...ba matsala zatazo goben yanxu dai ga abinda kikace can an had'a....ok in aci sai muje koh?. Tanason koyan girkin Hausa wa shiyasa ma ta nace zatazo dan a koyamata.
To nima saina huta zamu dan naji jiki gashi oga bai nan bare yamun tausa....kai Aunty Mimi nikam kiramin wata daga cikin servant d'in ku tazo tamun kafin kiga ma.
Haka akai kuwa saida suka huta sosai kana suka shirya ilai yanzun ma niqab suka d'aura driver ya jasu sai asibitin.
  
Auta ce

NEENA MALEEK     {COMPLETED}Where stories live. Discover now