12

1.9K 207 1
                                    

Nuna kansa yayi yace “nine mataimakin shigaban wannan kungiyar a nan Nigeria abuja nake zama amman saboda son da nake miki yasa yana aka ginamin gida a nan sokoto kuma na tare  a nan dan na rika ganinki ” 

Hannayensa ya shiga nunu mata ” dubi rabin jikina ki gani dinah duk sunanki ne sai kuma na kungiyarmu ” 

Hawaye nabin fuskarta kamar fanfo tace ” mie yasa kai bazaka bada kanka ba anya kuwa kai kikanken musulmine kasan hukuncin wadda yake aikata wannan aiki a gurin Allah “?

Gyara zamansa yayi yana murmushi yace “ni musulmin ne sunana manir muktar mahaifiya ta ce kirsta na tashi a uku a can nasan wannan kungiyar na har na zama mataimakin shugaban “

Ta sowa yayi ya dawo kusa da ita ya rika fuskarta yace ” wlh ina sonki dinah fiye da tunaninki “

” bazan iya sadaukarda kaina bane saboda ni Conductor ne ko da na sadaukar ba zasu karba ba sai in na aikata laifi ko na…….”

shiru yayi kamar wadda ya tuna wani abu ya cige lips dinsa ya tsura mata ido. 

Ita ko sai hawaye take tana karanda addu’o’i a hankali 

Murmushi yayi ya bugar mata baki ” daina abunda kikeyi bana so ” 

Kamar shi take jira aiko ta kara karfin addu’ar tashi yayi tsaye yana dafe kansa ya juya mata baya  “ohhh dinah ki daina plz na fada miki bana so ko ” yi tayi kamar bata jishi ba ta cigaba da addu’o’inta 

Juyowa yayi fuskarsa a hade cikin daga murya yace ” dinah in baki daina ba zan daina ganin tausayinki fa kina bata mana aiki ”   yan rufe baki aka turo kofar 

Wani katon mutun ne ya.shigo sanyi da wata karuwar riga ja har kasa baki kirin dashi fuskarsa babu annuri 

Saida ya kare mata kallo sannan ya kalli manir din cike wane yare ya shiga magana dashi 

Shima manir din ya mayar masa cikin yaren sunayi suna kallonta can kuma maganar ta koma cikin fusata suke yinta

Ido dinah ta sakar musu tana ta addu’o’inta bata ankara ba taji wani irin mugun bugu a baki ,

Katon mutumen ne yakai matashi nan da nan bakinta sai jini 

Cikin fusata manir ya cigaba da magana dashi .duk da bansan mie suke fada ba amman daga gani kasan fada suke. 

Can kuma naji yace ” ok ” mutumen ya juya ya fice shi kuma ya kalli dinah tare da riko hannunta ” tashi muje ” tashi tayi cikin tsoro sai addu’ah take 

Sakin hannunta yayi ya watsa mata mari ta bayan hannu yace “nace miki ki daina bana so “,

Hannunta ya sake rokawa ya fisgeta da karfi suka bar dakin 

Wani gurin matsatsin corridor suka bi, 

Ya dade yana tafiya sannan ya shigo wani dakin da babu komai cikin sai jajayen kyalaye da kandir 

Tunda suka tamo hannya addu’ah dinah take saidai bata bari yagane ba, 

Zaunar da ita yayi ya kama mata hijab ya cire  yace ” karkije ko ina ki tsaya nan zanzo ” yana kaiwa nan ya fice 

Addu’ah kawai take zuciyarta na bugawa kamar zata fito,

Yayi awa daya da fita sannan taji kamar an taba kofa, 

Da sauri ta kalli kofa tana maida numfashi a hankali aka turo kofa wani irin kalon macijine baki kirin sai sheki yake kai 

tsaye ya nufo ta kalmar shahada ta shiga karantawa jikinta na rawa 

Saida ya kawo kusa da ita sannan ya tsaya yana kallonta idonshi jawur dinah babu abunda take fadin banda ” la’ilaha illallah muhammadu rasulilah3  ” kamar shahada dinah take ta karantawa ta matsa jikin bango ta matse kanta 

Macijin ya dawo genfenta na dama ya koma na hagu haka yayita yawo sai kalonta yake can kuma ya juya ya fice 

( yan uwa mu rike kalmar shahada babban abuce duk lokacin dakaga abunda kake tsoro ko kaga makiyinka ko wani mai mugun nufi akanka ka karnta masa kalmar shahada zakusha mamaki dan inma da niyar cuta yazo bazai iya cutar dakaiba in mafadacine ko kuma kana jin tsoronta  zakaga ya kyaleka dan kalmar shahada tana karyar da  zuciya mai mugun hali ko cuta )

Karmar shahada kawai dinah taketa maimaitawa idonta sunyi wani ja sunyi zurfi, 

Baifi minti 15 da fitaba ya sake dawowa wannan karon da gudu yayo kanta 

Ita kuma bata fasa karanta kalmar shahada ba saida ya kawo kusa da ita ya tada kansa tsaye sai leko mata harshe yake kamar zai lasheta 

Ya dade a haka sai kamar shahada dinah take karanta mishi

Faduwa yayi  riff ya fice 

Can kuma ya sake dawowa wannan karon a fusace ya shigo ya nufota 

Lauyewa ta yayi ya matseta sosai can kuma ya saketa da sauri ya fice 

Haka suka wuni ita da macijin sai yaje ya dawo yaje ya dawo tun tana iya karanta Karmar shahada har takai inya nufota saida tace ” Allah ” 

Fitar da yayi ta karshe bai sake dawowa ba sai wasu maza uku suka shigo dakin 

Kai tsaye suka nufota biu suka rikata suka fice da ita

Harabar gidan suka fito da ita suka nufi parking space dayan ya nufi wata mota cikin motocin ya yajanyota suka sakata suka shiga suma

 dayan sai zabga mata mari yake fuskarta duk ta kunbura,

Bakin gulbi suka nufa da ita suna isa suka fito da ita suka nufi gulbin da ita suna kokarin jefata wayar dayan tayi ringing 

da sauri yayi picking yana karawa a kunne ya kallesu da sauri yace ” ku dakata kada ku jefar da ita ance mu dawo da ita ” suka juyo suka nuffo motar da ita 

Gurin sakata motar abu ya zama rigima dan kasa sakata sukayi saboda wani karfi daya zo mata sai watse su take 

Kana gani kasan ba ita kadai take ba, 

sukayi2 su sakata mota suka kasa har kusan asuba ana abu daya can dayan ya ciro wayarsa dake ringing ya kara akunne

Banji mie yake fada ba dan  cikin  wani yare yake magana can kuma ya katse wayar ya kallesu suma cikin yare ya musu magana bansan mie yace musuba 

naga sun nufi gulbin da ita suka luluyata suka jefar cikin ruwan.

VOTE

DEENAHWhere stories live. Discover now