A hankali ta fara motsi sannan ta bude idonta tashi tayi zaune tana karanta kamar shahada,Ta shiga kallon mutanen dake zagaye da ita
Matan duk suka shiga fadin ” Alhamdulillah ” dantijon cikin yace ” sannu yarinya sannu ” cikin tsoro tace ” ina nake waya kawoni nan “? Wani saurayi cikin mutane dake zagaye da ita yace ” kwantarda hankalinki mu mutanen kwaraine tsintarki mukayi bakin gulbi a yshe koda muka duba mukaga kinada rai kuma ALLAH kawai kike fadi duk da idonki a rufe yake shiyasa muka daukoki muka kawoki nan gurin mai anguwa ”
dafe zuciyarta tayi tana maida numfashi ta koma ta kwanta tana fadin ” Alhamdulillah2 ” dattijon ya kalli matar dake kusa da dinah yace ” kawo mata abinci ” tashi tayi tana ” toh malam ” ta nufi wani daki
Tuwon dawa ne da miyar bushashen kubewa makota ma suka shiga kawo mata sai jere mata abinci ake kamar mai ciki goma,
Babu abunda taci in banda yogurt da fura da mai gari yasa aka dama mata ganin ta kasa cin komai
Guraren 3 na rana dinah na kwance bayan tayi wanka tayi sallah
mai gari yazo kusa da ita ya zauna duk yangidan suka nufota suka zagayeta har da makota,
Tashi tayi xauna ta gaishe shi tare da masa godiya bayan ya amsa cikin ladabi tace ” dan Allah baba ina nn nan wane gari ne “?
” kina cikin wani kauye ne da ake kira more ” kai kawai ta daga masa tayi shiru
Can mai gari ya kalleta yace ” yarinya ya sunanki kuma maiya kawo ki nan garin “?
Gyara zama dinah tayi ta kwashe duk abunda ya faru ta fada musu duk abunda ya faru
Suka cika da tsananin mamaki sai jinjina abun suke,,,,,
Girgixa kai mai gari yayi yace ” lailai duk wadda ya rike Allah baya tabewa Allah yayi miki tsari yarinya Allah ya kara tsare gaba ” duk suka amsa da ” amin ” maigari yace ” yanzu zaki iya gane gida in aka tafi “?
Shiru tayi alamar tunani sannan tace ” ae zan iya ganewa ” wata mata ta kalleshi da alama matarsa ce haba tace ” haba malam wane irin ta gane gida yanxu tadai bada number waya sai akira su afada musu sai suzo suje da ita ” kai ya daga ” to ai babu matsala ” ya kalleta ” kinada numb daya daga cikin yan gidanku “? Da sauri ta daga masa kai ” ae akwai ta yayana ” maigari ya ciro wayarsa ya mika mata ” to samin anan saina kira ” tana sakawa ta mika masa ya danna kira ringing 2 ana 3 aka dauka saida suka gaisa sannan naigari ya fada masa komai
can ya mikawa dinah wayar karbi zaiyi magana dake ” da sauri ta karba sunyi 4 suna magana sannan ta mikawa mai gari wayar ” wai yace ka masa kwatance garin ” karbar wayar ya masa kwatance sanna sukayi sallama,,,
Can guraren biyar na yamma dinah na zauna tana fira da matan mai gari. Akayi sallama da sauri ta tashi tsaye ta nufi mai sallamar tana fadin ” yaya ” rungume ta yayi ya rumshe ido yana sauke ajiyar zuciya,
ta bayanta zainab ta rungume ta tana kuka sun dade a haka sannan ta juyo ta rungume nafisa da zara,
Tana daga kai ta hango momi tafe tana hawaye. Da sauri tayi gurin malik tana kuka tana kallon momi ” dan Allah momi kiyi hakurri wlh bansan haka zai faruba bansan ayimin wannan tarkon ba ” kama hannunta malik yayi ya rike sai a lokacin ya lura da wani farin wahala da tayi idonta sunyi wani baki sun shige ciki,
Momi na kawowa kusa da ita ta rungume ta tana hawaye.
Duk suka mashe da kuka har matan mai gari saida sukayi hawaye,
Kukan da ba daina ba kenan saida abbah ya shigo, sannan suka shiga share hawayen suka tsagaita kukan.
Da gudu dinah tayi kansa ta rungume shi tana kuka
YOU ARE READING
DEENAH
RomanceThe beginning of another life. suspicious, terrified, remorseful. DEENAH...! ®2015 NOT EDITED ⚠️