21 NEENA MALEEK

1.3K 99 12
                                    

Allah yarhaam yagfirri zunuub bi Umma. We really miss u our lovely Aunty 😢😢need ur prayers I miss my Aunty today.

    21.

A cikin jirgi Momy bata uhm ba ta uhm um saidai idan sun saka ba a maganar su sai tace wani abu.
Wata nutsuwa tayi taban mamaki a cikin jirgin sukam yan gari haukan su suke kawai da waya har jirgi Yazo ma tsaya ta Abuja.
Hannun NEENA na cikin na Momy suka sauko inda sukaga motoci na jiran su.
Momy munzo Abuja yau zakiga k'awar ki fa. Batace mata komai ba suka shiga motar sai villa.
A gate d'in k'arshe aka sauke su fitowa sukai...Dada ne yace NEENA inaga a bari ayi sallah a d'an huta sai Malaman suzo koh?.
A'a Dada kawai kai katafi office amma ba zama muka zo ba all I want to see My Mom is ok don't worry  I will take care for her ina ala sauk'i Malaman?..
A part d'in baya ne. Ok d'akin Momy fa?, kusa da naki. That's Gud bara muje kawai. Halex zakuje ko kuwa?, No zamu ai ba yunwa ko gajiya tare damu. Amma maganar Dada gaskiya ce kya bari Uncle ya dawo kuma ko Ummi ma bamu shiga gunta ba.
Tom Dada idan akai sallah yayi?, yayi yar gidan Momy....yar Mama dai I naiwa Momy k'ara ne amma duk duniya koda uwata zata dawo yo fa Mama she's the best ban had'a ta da kowa shiyasa bantab'a kiran kowa a Duniya da Mama ba sai ita.
Dariya su Mama sukai. Cikin gidan sukai masha Allah su baby sai raba idanu suke duk da dai suna zuwa amma saida kaga komai ya canja haka suka shige har Katafaren parlor'n dake gefen dama inda su Mama suke.
Oyoyo oyoyo NEENA ta nayi kewar ki....same Mama nama fiki jin jiki da banganin ki.  Haba dai dariya suka sanya hugging d'in su tai wajen matan yayun ta tayi suma haka kafin ta juyo.
Momy bakiga K'awar kiba, shiru tayi kuma tak'i zama duk yanda sukai da ita ta zauna tak'i saima wani iri da sukaga fuskar ta tanayi..
  Ganin haka yasa NEENA da sauri ta fice a d'akin waya ta dannawa Uncle da Dada tace suyi maza a taho da mutanen nan saboda jikin ta yanason tashi.
Wajen ta ta koma Momy baby ce fa kinason a koma gida bakison nan?, eh banso mai dani gida ke kuma ba baby na bace ni baby na namiji ne.
Kinason wasa da hankali na koh?, a'a Momy nice fa kalle ni kiga bara mu tafi na maida ki d'akin ki taso. Hannun ta taja. Waje sukai inda aka bude musu k'ofar mota suka shiga sai part d'in su NEENA.
Yauwa Momy bara na canja kaya sai na maida ki. Batace mata komai ba ta dai fito. Shiga sukai nan ta haura sama da ita d'akin da aka Warr sabida ita nan suka shiga tana ganin Momy ta shiga tayi maza ta kulle k'ofar ta sauka k'asa daidai nan saiga Mama da su  Ummi. Ke bakida hankali kina zaton idan ta shake ki akwai mai kwatar ki?, sorry Mama bazan kuma ba Dada yace gashi nan zuwa jikin nata tashi zaiyi.
Yama tashi dan kuwa wata irin k'ara take yi tana buga k'ofar tana kiran sunan baby... cikin kuka NEENA tace saida nace ayi komai yanzu saboda inada dalili amma aka ki ai yanzu gashi nan.
Da sauri Uncle ya shigo NEENA ina take badai jikin bane? , shine Uncle tana sama ina suke suzo su fara aikin su dan Allah.
Gasu nan Dadan ki yaje tahowa da su. Tsaye suke kowa da abinda yake sak'awa har Malaman suka shigo su goma.
Bayani a gurguje NEENA tayi musu na yanda tafarayi....kai kawai suke jinjina wa ....zamu shiga yanzu insha Allah komai yazo k'arshe.
Saman suka haura da zuwan su suka bud'eta....da gudu ta fito amma kafin ta sauka har sun rik'o ta rik'o bana wasa ba.
Wani ruwa suka fesamata.....ai fa sai kukan jinjiri kafin wani lokaci saina akuya saita koma kuma kurma. ...hayak'i sukai nan wajen ya turnike da hayak'i wani kala kore kore ja ja ja ja..blue blue.
D'akin ne Ya d'auki rawa inda komai na d'akin saida ya d'auko k'asa hatta gado saidaya karye. Uncle yana gefe cikin sa duk ya d'uri ruwa sukam matan gaba d'aya ficewa sukai daga part d'in NEENA ce kawai ta tsaya amma fa addu'ar samun nasara gun ubangiji take.
Malamai dai suna ciki tun 11 ake abu d'aya amma har 6 na yamma babu wani canji saidai tayi ta koma wa wasu kaloli na dabbobi.
Sallah kanta a d'akin suke Uncle dai fita yai..Abban Aunty Safeena ma ficewa yai saboda abin yafara bashi tsoro. NEENA ma Dada Koran ta yai ta koma cikin gida..
Abu kamar wasa saida Momy tayi sati ana abu d'aya duk tafita hayyacin ta hauka sosai take idan tana k'ara sai gidan gaba d'aya amsa d'akin da take kuwa malamai uku kaf sun k'one saboda tsabar fafatawa da manyan aljanun da suka jima ajikin ta.
Yau kam tun safe Sheikh Al-afasy  na k'asar Qatar da kuma Sheikh Khalifa Isyaka Rabiu had'i da taimakon Sheikh Dr Qaribullah suka dira a gidan President.
Tundaga shigar su gidan suka tabbatar da akwai manyan abubuwan da suke faruwa. NEENA kam batada sukuni kullum cikin addu'a take waya ma da Maleek ba sosai suke ba sabida ta gayamasa akwai Momyn ta batada lafiya.
Sosai yake tausaya wa matar idan NEENA tana gayamasa  yadda ake kai rana akan aljanu.
Daga b'angaren sa shima yawan mafarkin da yake yanzu ganin ta yake a tashin hankali sosai ya dage da addu'a akan Allah yakawo sauk'i.
Duk abinda Allah yaso yana faruwa a lokacin da yaso dan kuwa Allah maji rok'on bawan sane yana yaye masifa lokaci guda yana kuma sawa lokaci guda..
Cikin ikon Rabbi Allah ya amsa addu'ar masoyan Momy akan ta. Kaf wasu aljanu da sammu da kuma sihiri  duk sun karye aljanu sunyi kuka.
Basu tsaya sauraron wanda ya turo suba fita kawai suka ce suyi....d'aya bayan d'aya suka ringa fita saidai sunyi alkawarin sannu zasu juya gun wadda ta turo su dan bazasu yarda da k'ona sun da akai ba.
  Tunda aka samu komai ya warware d'akin kansa saida aka wanke shi da magani ita kuma hayaki aka k'ara yi dan ganin ko akwai sauran wasu ba amma ba'a sami komai ba.
Hamdala sukaiwa Allah. Nan kowa yakama gaban sa bayan d'unbin godiyar da suka sha wajen Family d'in sarki.
Sarkin Adamawa kansa saida yazo yai godiya ga manyan Malam kano ta Dabo tumbin giwa.
  Momy saida tai kwana biyar kafin ta farka. Da salati da hailala ta farka. Asibiti akai da ita inda aka dubata sosai masha Allah babu matsalar komai saidai tana buk'atar hutu sosai.
A asibitin suka barta tunda acikin gidan yake. Tunda Momy tazo gidan sai a yau kowa ya samu sararin zuciya ganin ta ras ta tashi tana magana. Tagane kowa yara da manya na Adamawa sunzo kowa sai farinciki.
NEENA kullum tana gunta sosai takejin dad'i. Matsala d'aya bazata tuna rayuwar ta ta baya ba har sai taga wanda tasani a lokacin da abin ya faru da ita.
Ko a haka ma sunji dad'in ganin ta ras. Umrah Uncle yace aje dan nuna godiya ga Allah. Kaf suka tafi kwanan su goma suka dawo inda Momy tace zata koma uncle yace a'a sam ta zauna anan kawai.
Su NEENA sai yanzu aka samu sararin yawo. Zuciya tayi dad'i babu fargaba.
Maleek dai har yanzu baisan NEENA ba kullum yanamata k'orafi. Su Sofy ne sukace masa kada yaji komai jibi suna tafe zai san wace Hajar.
*****
   Baba fa abu goma da ashirin saboda kwana biyu ba daidai takejin ta ba shiru dai kawai. Ga mafarkin Amina da take da kuma Mai Nasara suna kuka sunata cucesu.
Yau gidan nasu babu kowa daga ita sai yar ta Saratu wadda tazo daga Ghana.
Hira suke yi amma lokaci zuwa lokaci Baba saitayi wani abu wanda ba daidai ba.

Auta ce

     Plx more comments yanzu zakuji wace Baba waye Maleek kuma?.

NEENA MALEEK     {COMPLETED}Où les histoires vivent. Découvrez maintenant