25 NEENA MALEEK

1.4K 86 18
                                    

Tnx for loving my book...more expecially Khairiyat and Alolo MrsMj.

      25.

Yaya Seema ki shirya yaufa zamu ga Hajar two eyes...hmm Aslam nifa gaba d'aya nashiga wata duniyar daban...dama akwai sauran marasa Imani a duniya haka...ta rabamu da kowa bamuda alak'a da Baba ko ta ficika...kishiyar kakar mu  ce...Inalillahi ashe bamu san dad'in yan uwa ba duk abinda muke sai kuka.
Plx Yaya Seema ki bari mana kada Maleek yagan ki haka yafara daga hankalin sa...tunda munji ba sai muyi abunda Allah yace ba mu k'ara addu'a akan wadda muke kafin mu tunkari maganar da muke son yi.
Haka ne  bara yazo. Basu jima a tsaye ba kuwa saiga Maleek yai kyau cikin kayan sa.
Hannu sukai da Aslam kafin su shige mota sai airport. Tsaye sukai ba'a jima ba kuwa suka fara ganin taron mutane anzo ganin NEENA. Aslam yar President ce fa tazo inaga ko Hajar su sai anjima?, aikam dai dan kuwa babu hanyar wucewar wani ma a gun nan sai tasu.
Aunty Seema bara mu k'ara jira naga tace mun dai sun taso maybe ko jirgin su na anjima ne. Think so. Kalla yadda kowa yake saita camera xa'a d'auki NEENA yarinyar akwai farin jini da taimako. Murmushi Aslam yai yace ai NEENA samari dubu inaga zata aura to kaga yaran gidan Sarki can  a gefe...gana governors a gefe wa zata d'auka wa zata bari.
Hhhh kajika ai duk tak'amar mace miji d'aya zata aura a dai gama ruwan idanun.
Budewar k'ofa ce tasa kowa ya maida hankalin sa gun...Halex ce a gaba sai Baby...Khadeeja..Maama..Sofy...Nana...Sumy...Khadee..Sumy baby TSR a layi suka fito kowacce tayi kyau tagaji da had'uwa basarwa suke sabida ganin har 'yan media akwai a gun.
Wajen katafarun motocin su sukai inda security sama da guda arbain suke jiran su.
Kowacce tsaye tai a kusa da k'ofar motar da ka bude mata. NEENA tana ciki bata fito ba kowa kuma ita yake son kalla....kamshin turare Hajar ne ya d'oki hancin Maleek da sauri ya waiga....nan kuwa ya hango ta cikin Hijab d'in ta da nikab d'in ta tana nufoshi saida ta kusa dashi sannan ta yaye Nikab d'in tana sakarmasa wani mahaukacin murmushi mai narkar da zuciya.
Idanu ya ware nan ya kalli bayan sa yaga babu wata fa sai ita...baya yafara ja ita kuwa tana nufoshi ganin ta kusa cimmasa da sauri ya d'aga mata hannu please NEENA kike kowa kiyi hak'uri ni akwai wajen wadda nazo ba gunki nazo ba bansan ki ba kada kisaka Hajar taji ba dad'i.
  Wayar ta ta Danna nan kuwa wayar sa tafara tsuwa. ..d'auka yai ganin Mine cikin siririyar murya tace Mine nagode agaban mutane ka yarfa ni dama nasan ba sona kake ba.
Juyowa yai kwarai Neenah ce kenan itace Hajar....hararen sa tayi tace Yaya Aslam kaga wannan k'anin naka koh?, Aunty Seema nafara gajiya kuzo mutafi tunda Maleek baiyi murna da ganin mine ba.
Da Sauri ya damki hannun ta yace wayace banyi murna ba...ni Hajar nasani bansan NEENA ba shiyasa zuciyata takasa yarda da kece....hararen sa tayi tace ai Yaya Aslam ya koyamaka magana inaca a Minjibir nace muku akwai lokaci ba gashi yazo ba.
Ku me NEENA take ne kodai Maleek d'in ne?, inaga shine dan naji tana masa waya..aa kuzo muje mana.
Tahowa sukai daidai nan Tauheed da Taufeeq suka taho inda sukaga Maleek suna tsaye.
Security d'in wajen sun so hanasu shiga dake tana tsayawa aka zagaye su amma ganin suna kama da yan gidan yasa suka basu waje.
Baby ce tace NEENA kinfa shanyamu....magana zata k'ara Maleek ya d'ago da sauri suka zubamasa idanu cikin karkarwar baki Sumy ta furta wannan ne Maleek?, shine me kuka gani?, ikon Allah amma ke baki tab'a ganin kamannin Momy Safeena a jikin sa ba...wallahi da ace dan tsintuwa ne babu abunda zaisaka nace wannan ba jinin mu ne.
Kai NEENA duba bayan ki ki gani. ..Yaya Tafida ne yaushe kazo?, a'a baiwar Allah Tauheed nake ba Tafida ba kunga wannan wasan kwaikwayon is ok kai Maleek mai suke nema gun ka...kasan dai su waye kada ka jamana abinda bazamu iya ba.
Kana nufin kace kai ba shi bane to waye kai...Sofy..Halex..Baby ku kalla wai wannan macen ma ba 'yar uwar mu bace wallahi ku ku family d'in mu ne kalla kiga koni ina kama da wannan ta nuna Taufeeq.
Kallo fa ya koma soma dan kuwa ko security sun shaida kamannin su. Maleek dan annabi juyo da bayan ka mu gani. ..juyawa yai ihu NEENA tasaka tace wallahi wallahi kai jinin Momy Safeena ne ga irin abin gidan Baba waziri nan.
To ai muma munada wannan tawadar Allah d'in Seema tafad'a cikin dauriya dan kuwa ko ba'ace ba tunda taji suna Safeena to magana ta k'are amma ta yaya take raye bayan ta mutu?.
Kunga ba zama zamuyi ba wallahi kuzo a tafi Abuja yanzu ko Adamawa bazaku tsere ba. Tauheed  cikin fusata ya nuna baby yace ke Muda kika ganmu da iyayen mu maza da mata  bamuda alak'a da ku saboda haka kuyi nan ya nuna musu hanya.
Kaga waye kai wallahi bazaka tsere ba sai anje Abuja kagama fad'an ka kai jinin mu ne.
Zai k'ara magana Seema tace babu Shakka mu jinin Wazirin Adamawa ne wannan kuma shima Maman sa Safeena 'yar waziri ce amma ita ta rasu tun bayan haihuwar sa anan aka samu matsala.....da baku ce tanada rai ba sainace yes d'an tane..amma.ita Tamu Safeena d'in ta rasu.
Aunty Seema Momy bata mutu ba. Wayar ta ta Danna takamomata photon Momy Safeena....inalillahi wa Inna ilaihir raji'un itace wallahi amma garin Yaya?.
Tauheed tabbas akwai wani sirri wanda babu wanda yasan dashi daga ni sai Aslam muma a yau mukaji mu bamuda alak'a da Baba amma ku kunada ita saboda yayar kakar kuce warware komai sai anje gaba.
NEENA juya mu koma banda matsala da Khaleed zan masa waya. Kada kuce komai kuzo muje.
Tafiya sukai sai cikin jirgi. Kowa a wajen mamaki yake to me suka ce ya zata koma babu amsa sabida security sun zagaye inda suka tsaya.

ABUJA

Dada dasu Uncle zaune suke a conference suna dan tattauna wa saiga matan su da kuma Momy Safeena sun shigo.
A'a Safeena sannu jiki yai sauk'i Allah yakara afuwa. Ameen nagode sosai badan ku ba nasan haka zan koma ga Allah na..NEENA banda abunda zan saka mata dashi a duniya saidai addu'a tagari.
Ayya Safeena babu komai fatan mu Allah ya had'a ki da wanda zaki ita tuno rayuwar ki ta baya shine matsalar mu yanzu kawai.
Dariya tayi kawai. Gidan shiru baby ta tafi ta barni. Dariya Mama tayi tace aini kin kwace mun 'ya...itama yanzu komai Momy...aini ma yaji zan muku tunda ware ni ake.
A'a ki rufamana asiri baby takice.. ni ai nabar miki ita....ko aure tayi sai ku tafi tare. To fa mijin zai yarda ne?, dolen sa tunda Momy Safeena ce.
Sallama akai daga can. Kamar muryar NEENA fa nake ji?, nima haka.
Kafin su k'ara magana sunga mutane da yawa sun shigo idanun Seema suna had'uwa dana Momy da gudu tai kanta ta fad'a jikin ta.
Aunty Fulani kece sai kuka dama baki mutu ba?, kikabar Maleek da shan wahalar rayuwa kinyi adalci kenan..kullum addu'a ta Allah ya bayyana dangin Maleek ashe dangin sa suna kusa adalci kenan kinsan wahalar rayuwar da Maleek yai.
Maleek kam cikin fushi yace Aunty Seema indai a duniya inada ke to kowa minus ne yanxu ma bana buk'atar ta tunda ta iya tafiya ta barni saboda ita mai kud'i ce ta iya rayuwa babu ni to mene amfanin xuwa na me zata mun.
Babu abinda zata mun ba wanka ko tsarkin fitsari zata mun ba...ba wanki ko biyan kud'in makaranta zata yi ba ai babu sauran abinda zata mun indai itace uwata to na yafe taso mutafi ku kun isheni rayuwa bazan so wasu bayan ku ba.
NEENA ina son ki amma tunda kema jinin wadda ta yarda d'an ta ne gaskiya baxan iya auran ki ba...Yaya Aslam taso mutafi tsayawa anan b'ata lokaci ne.
Cikin tsawa da fushi Seema ta mike mari ta bashi wanda saida ya gigitashi bata bari ya d'ago ba ta rufe shi da duka ta ko'ina.
Maleek lallai wuyan ka ya isa yanka. A gabana wallahi babu wanda ya isa ya tab'a Aunty Fulani na kyaleshi koda kaine mara hankali. To bara kaji ni ina sonta saidai kaine zaka tafi amma ni babu inda zani idan baka sani ba kasani idan kace bazaka amshi Safeena matsayin uwa ba dole ka amshi dangin ta matsayin dangin Abban ka.
Ai Aunty itace xatayi fushi da kai saboda rabon kane yasaka rayuwar ta a wahala..badan kai ba da Aunty bata riski rayuwar ta a haka ba.
Zo kabata hak'uri kasan darajar uwa kuwa...ilimin ka bayada amfani...nayi takaici sanin wanda baya daraja uwar sa wallahi..Maleek kaban kunya sai kuka.
Aunty d'an annabi kiyi hak'uri bazan kuma ba bara nabata hak'uri ki ji wallahi ina son ta na rantse da Allah ina k'aunar ta..Aunty kada kiyi fushi vara naje.
Wajen Safeena na yai wadda ta ke a zaune tabata yai...luuu yaga tayi baya ta fad'i.
Ihu suka saka kaf d'in su wayyo ya kashe mana ita.....Mr president ne yace wayace ta mutu a kira Family Doctor yazo.

Auta ce

NEENA MALEEK     {COMPLETED}Donde viven las historias. Descúbrelo ahora