Written by khaair
Aliyu saida yayi wata guda harda kwanaki bai waiwayi fatima da dukda kuwa su daddy sun sanar masa da cewar an daura aure shi ake jira.
Saidai cewa daddy yayi bai gama gyara mata part dinta ba. Baya son hadasu part guda da Asiya gudun rigima tunda kawaye ne. Kuma har yanzu bai samu ya fadawa ita Asiya dinma gameda auren.Jin shirun yayi yawa mummy ta aika kiran Aliyu. Anyi sa'a kuwa daddy nanan ranar.
Mummy fada sosai tawa Aliyu har nuna mashi tayi bataji dadi ba
"Yanzu Aliyu koda makiyiyarka aka aura maka sai kayi wannan halin ko in kula din da ita iye? Yanzu kayi adalci kenan? Koko kana tunanin kayiwa ita Aisha adalci, kadai san babu uwar da zata ji dadi a wulakanta mata yarinya tunda da gatar ta. Inka san baka sonta, to tun kanta tare, a yanzu basai anjima ba, ga takarda rubuta mani sakinta na bata. Ko sati bazai juyo ba zaka sha mamakin wanda zani hada ta dashi. Yarinya kyakkyawa jini a jika kai har kana wani halin ko in kula da ita. Wallahi toh Aliyu in ba so kake na saka maka ido ba, nabar shiga harkarka, toh kwana uku na baka, kaje gidansu yarinyar nan, ka tambayeta duk me takeso na lefe, dole kaje ka hada mata shi, sannan bawai sai sati ya zagayo ba, cikin satin nan nakeso ta tare. In ba haka ba, cikinmu zaniga wanda ya haifi wani, daga maka nono zaniyi, kabi duniya kowa ya hut..."Da sauri Aliyu ya rufe bakin mummy yana girgiza kai
"Hajiya kiyi hakuri. Dan Allah kiyi hakuri, banyi hakan bane danna bata muku rai. Part dinne nake gyarawa, basai su daddy sunyi wahalar siyen komai ba na kayan daki. Amma in sha Allah cikin satin nan saita tare din. Yanzu bama sai anjima ba zanije wajen zarah din, sai muje tare ma ta fada duk abinda takeso sai ayi order a siyo mata..karki mun baki hajia, kiyi hakuri"
Ture hannunshi tayi daga bakinta, dukda ta sauko yanzu tace
"Toh madallah, haka kawai kusa ma yarinya karama hawan jini bata ji bata gani ba"
"Kiyi hakuri"
Shine kawai abinda yake cewa.
Daddy ma ya kara nashi nasihun, sannan Aliyu ya tashi. Saida ya fara zuwa kasuwa ya bawa Abba hakuri koda ya bata masa rai sannan yaja akalar motarsa zuwa gidan umma. Zuciyarsa kuwa cunkushe, yanzu duk kan fatimar nan ne kowa yake fushi dashi, mahaifiyarsa hada ikirarin zata tsine masa, lallai fatima tana neman ta wuce gona da iri. Yanzu haka kilan itace taka kai karata tunda kamun kanta ma ta cireshi ta ajiye.Haka yayita tunani ya isa gidan Umma. Tun daga kofa yake jin shesshekar kukan fatima, hajia da umma na bata hakuri.
"Toh miye na kuka fatima? Shifa auren nan an riga da an daura, kinsan ko kina shan giyar wake su Abban naki ba rabashi zasuyi ba. To kika daga hankalinki name?
Cikin kuka tace
"Niba kuka nake dan an hadani da ya Aliyu ba, tun kafin na auri kabir shine nace inaso ai, ashe har an rigada an daura auren. Umma shi ya Aliyu son kanshi yayi yawa. Inace ni kaina bansan da auren ba saidai shine ma ya fara sanar dani, amma ya dauki karan tsana ya dora mun. Umma to yaya za'ayi nayi murna da wannan auren. Dubi fa kiga yanzu wata daya da wani abu. Ko keyarsa kin gani a gidan nan. Umma rabona dana sashi ido tun randa aka daura aurenmu da kabir.
Ciwo nawa nayi, kwana na nawa asibitici, masifu nawa suka dinga fada mana. Ya kira ko yazo dubani? Umma ke kanki kinsan inada riko, amma ban taba rikon ya Aliyu a raina ba, dan wani sa'in gani nake hada laifina. Umma amma duk laifi na akanshi, tunda shine yayi nauyin baki, inda baiyi nauyin baki ba. Da ko ya muktar bai kawo kai ba. Sai yazo ya dora mun karan tsana. Ni a raba auren ma banayi. Tunda ba dole bane. Daman ko naje gidan ba dadi zaniji ba, ga tsanarsa ga masifar Asiya danna san ba barina zatayi ba. A barni gida nayi karatuna"
YOU ARE READING
💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫
Roman d'amourFatima is the only child to her parents, who grew up with so much love around her, until her father took a second wife. She embarked on the journey of life like every human. Amidst her journey, came Aliyu and Mubarak, twins who would die for her, an...