💫🌼twenty nine🌼💫

2.9K 157 3
                                    

Written by khaair

Da asuba kam fatima bacci tasha bata samu damar farkawa ba sai karfe bakwai hada minti biyar.  Zumbur ta mike,  ta shiga kewaye,  sosai yanda yanayin toilet din yake ya matukar burgeta.  Saida ta watsa ruwa sannan ta daura alwala. 

Sauri sauri ta kabbara sallah.  Saida ta gama adduo'inta sannan ta shafa.  A bisan prayin mat din ta cigaba da bacci.  Bata koma bacci ba,  ta shiga kitchen. Abinci mai sauki ta hada,  amma dukda hakan,  gidan kamshi yakeyi. Asali ma kamshin daya tashi Aliyu kenan. Ta hada ta jera komai a dinning table.  Sannan tayi komawarta daki.  Tara dai-dai Aliyu ya fito tsab ya gama shirinsa na office. 

Bai duba fatima ba,  baibi takan abincinta ba kuma ya ficewarsa.  Sashen Asiya ya shiga.  Itama ta tashi, ta hada breakfast dinta dai-dai cikinta.  Karba yayi yace

"Kin hada breakfast ke kadai kina ci,  shi mijinki kin barsa da yunwa,  haka akeyi? "
Yakai lomar dankali a bakinsa.

Wani dadi ne ya ziyarci zuciyar Asiya,  ba komai bane kuma yanda ta lura Aliyu sam baya rawar jiki kan fatima.  Murmushi tayi kamar ba wacce tasha kuka ba jiya tace

"Ai nayi zaton kunci kaida amarya ne,  bara na karo maka tunda da saura"

Harara ya galla mata yace

"Oh daman akwai amarya gidan nan ne bayan ke?  In baki bani ba,  to wacece zata bani.  kinga ni ya isheni,  banason cika cikina,  naje na kasa aikin komai office."

A sama sama ya ida cin abincin,  dukda kuwa  bai cinye ba.  Sauri sauri ya dauraye bakinsa,  yawa Asiya side hug ya fice da sauri dan ya makara.
Motarsa ya tada ya fita harabar gidan gaba daya.
Duk abinda yayi a idon fatIma.  Shigarsa har fitowarsa.

Wasu zazzafan hawaye suka zubo mata.

"Naga ta kaina ni bintu,  Abba kunada masaniyar inda kuka kawoni kuwa?  Ko 24hours banyi cikin gidan nan ba amma na fara ganin rayuwa?  Ya Allah ka dube da idon rahma ka kawomin saukin lamura"

Ta goge hawayenta,  ta ci abincinta sosai. Saida ta tabbatar da ta rufe part dinta.  Sannan ta koma daki ta shirya jikinta.  Kujera ta hau ta dauki wayarta tana duba abubuwa.

***
Karfe shida na maraice Aliyu ya dawo.   fatima da yake parlour ta,  window din yana ganin duk abinda yake wakana tsakar gida.
Asiya ta gani ta shiryo cikin wata doguwar riga ja,  kayan sun bayyana surar jikinta sosai.  Da gudu ta rungume Aliyu.  Shima dan karya gwaleta ya rungumeta yana shafa bayanta.  Ita kam kara narkewa takeyi ta mishi sannu da zuwa. Tareda karba takardun hannunsa tana cire masa lab coat dinda ke jikinsa duk alamun jini a jiki,  da gani dai wani surgery yayi.  Tare suka shiga part din Asiya.  Komai ta kai masa dakinsa.  Sannan ta kawo nasa ruwa masu sanyi. Kafin ya gama sha ta jera masa abinci kasa tace

"Nasan dai yau ka gaji.  Ka zauna nan na baka abincin da kaina"

Murmushi yayi,  ba musu dan kuwa ya gaji din.  Ya zauna dirshan,  ita kuma tana bashi har saida ya koshi. Sannan ta taimaka masa ya mike.  Dakinsa ya shiga.  Itama ta bi bayansa,  ta hada masa ruwan wanka,  ya rage kayan jikinsa ya rage daga shi sai boxer.  Ya fada wankan ita kuma ta fito parlour ta kauda kayan daya ci abincin dasu.. Wata annashuwa kawai take,  badan komai ba sai yanda yayi halin ko in kula da fatima.

💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫Where stories live. Discover now