Written by khaair
Tun da fatima ta shiga watan haihuwa, sai kafafuwanta suka fara kumburi. Duk abin saiya fara damunta.
Umma tace mata ba abin damuwa bane ita nata ma mai sauki ne saida ta kusa haihuwata,
wasu da cikinsu ya fara girma ne suke fara kumbura har sai sun sauka.
Aliyu ma kullum saiya mata tausa indai yananan, tanajin dadin abin sosai.Haka yauma ranar alhamis tana kwance bisa gadon inna, Aliyu na zaune kafanta guda bisa cinyarsa yana mammatsawa, umma kuwa suna daga waje itada inna da kawu ishaq yana yankewa inna farce anata hira.
Daga kwance fatima taji kamar an yankar mata kugu. Ai zabura tayi ta tashi zaune babu shiri. Aliyu duk saiya daburce.
"Sweetheart lafia? Meya faru?"
Murmushin karfin hali tayi tace babu komai. Saita ja pillow ta jingina da gadon. Sukaci gaba da hira.
"Are you sure you okay?"
Gyada mishi kai tayi. Saiya dawo ta gefenta ya dora kanta a kafadarsa yana shafa sajen dake kwance ta gefen fuskarta.
"Baby, Allah sa ki haifamin baby mai kama dake."
"Ni yaya da za'a cire cikin nan ma yanzu zaniji dadi. Wallahi kullum ciwon baya, ji kafana duk ya kumbura"
"Baby da kinyi hakuri, nan da kwanaki kadan ma zaki sauke ki huta"
Lafewa tayi jikinshi, ta zagayo da hannuwanta a kugunshi da lumshe idanu. Murmushi yayi, amma har a ranshi yana tausayinta. Haihuwa ba karamin abu bace.
Kamar wasa sai yaji jikinta ya sake. Yana dubata, harta yi nisa da bacci. Daria yayi yace
"Kasa kawai"
A hankali ya bambare hannuwanta daga jikinshi, kamar za'a saceshi.
Ya sauko daga gadon.
Ya gyara mata kwanciyarta ya lullubeta dan kuwa sanyi ya fara sauka a garin.
Wajen su umma ya fita ya zauna suka dasa hira. Sai magrib ya tarkata kayansa ya tafi bayan ya shiga ya tada fatima tayi sallah saida ya tabbatar data tayi alwala sannan ya tafi.Saida yayi har isha sannan ya isa gida. Asiya nanan parlour, da alamu baki tayi, dan kuwa plates din abinci ne a ajiye a kasa. Sannu ta mishi, ya amsa yace
"Baki mukayi ne?"
Sosa keya tayi tace
"Eh"
A takaice"Su waye sukazo?"
Kame kame ta fara tace
"Su munawwara ne sukazo"
Nan da nan fuskar Aliyu ta cenza. Baice komai ba ya wuce dakinsa. Wanka yayi. A gaban mirror ya zauna. Saiga kiran umma, da sauri ya dauka
"Umma lafia daiko?"
Murmushi tayi daga cikin wayar tace
"Kwantar da hankalinka. Mummynku ne ta kira tace ta nemeka bata samu ba, kaje gobe"
"Toh umma shikenan, Allah ya kaimu lafia"
YOU ARE READING
💫🌼FatimaBintuZarah (Binafa)🌼💫
Lãng mạnFatima is the only child to her parents, who grew up with so much love around her, until her father took a second wife. She embarked on the journey of life like every human. Amidst her journey, came Aliyu and Mubarak, twins who would die for her, an...