🌸 *SHINE GATA NA*🌸
Story &written By
👇🏻
'''Aysher Abbakar(meerah)'''® PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
ɯɛ ɖơŋ'ŧ ơŋٳყ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛ'Ş#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303Follow me on wattpad @aysherabbakar.
*Akwai mutane dayawa Wanda suke kirana da kuma Wanda sukemun magana ta PC kan Dan Allah inayin posting sau biyu arana,maganan gaskiya sai dai kuyi hak'uri Dan karna muku alk'awarin da baxan iya cikawa ba,amma nayi alk'awari in Allah ya yarda zan k'ara yawan typing d'in da nakeyi,Dan a gaskiya inada uziri sossai Dan wlhy typing ba abune mai sauk'i ba,nagode sossai da soyayyarku da kuma kulawarku gareni,I heart u guyx*
*13-14*
Malam hudu ne ya mik'e fuskan shi cike da farin ciki da walwala,key d'in duka gidan ya d'auko ya damk'a mata yace"hajiya ga makullan gidan,Allah yasa an shiga a sa.a Allah ya tsare fitina"
Ta amsa da "amin"
Kama hanun kamal tayi daya tsaya tamkar wani mutum mutumi suka shiga gidan,zubewa sukayi a palon suna mayar da numfashin gajiya.
Shidai kamal ya kasa cewa komai saboda tanbaya ne fal bakin shi amma yana tsoron magana tunda Amma ta kwa6eshi akan batason yawan magana.
Dubanshi tayi taga yayi tsuru - tsuru kaman Mara gaskiya,ahankali takira sunanshi ya d'ago da sauri ya dubeta,kiran shi tayi da hannu yadawo kusa da ita ya zauna,dubanshi tayi tace"kamal nan fa gidan mune,naga kaman a tsorace kake"
Da sauri ya dubeta yace"Amma waya bamu"
"Allah" amsar data bashi kenan
sannan tacigaba da cewa,"kaga lokacinda muke Adamawa kullum Malam hudu yana zuwa ina bashi kud'i har tsawon kusan shekara d'aya,to fili yasiyamun sannan ya ginamun gidannan dashi,sauran kud'in dayake bina ne shine na siyar da gidana na Adamawa na cika mishi kud'in shi,Dan gaskiya kamal hankalina baya kwance a Adamawa sakamakon rasa mahaifana danayi,kuma kaima banaso na rasaka shiyasa kawai na yanke shawarar dawowa nan"
Shuru kamal yayi sannan yace"to Amma idan babana ya ganmu fa?"
"Kamal babanka ya koma Adamawa ai,shiyasa ma nadawo nan batareda wani damuwa ba"
Murmushi yayi yace"Amma kinga gidanmu me kyau ko?ba ruwanmu da sanyi da cizon sauro"
"In shaa Allah kamal"
Nan suka shiga da 'yan kayayyakin su,kamal kuma ya kora shanu cikin d'akinsu ya d'aure su da tumakin sannan yabasu abincinsu daya gani jibge a saman rufin,ya zuba musu ruwa sannan ya kulle su yadawo cikin gida.
Bintu kuwa dukda tsohon ciki amma bata fasa zuwa talle kasuwan mubi ba,Dan costumers d'inta na Adamawa masu mota har mubi suke biyota dayake ta sanar musu zata bar Adamawa.
Haka rayuwa yacigaba da tafiya musu har yau da daddare da nak'uda yatashi wa bintu,cikin ikon Allah komai yazo da sauk'i nan ta Haifa d'iyarta mace,ranan suna aka sakamata sunan mahaifiyar bintu wato *Aysher* Wanda suke kira da *Farzeen*.
Duk wannan lokacin da suka d'auka a hankali bintu ta rink'a siyan kayan d'aki tana Tarawa har komai ya gama tsaruwa,yanzu kanma batayin tallen har gida ake zuwa ake siya.
Cikin ikon Allah sukayi 6ul-6ul kaman basuba,kayan abinci kuwa da yawa take siyamusu.
Shanu da tumaki kuwa Allah ya sa musu albarka yanzu sun wuce garke d'aya,ahaka ne har farzeen takai shekara d'aya da 'yan watanni,babu sunan data iya kira sai Amma da kamal.
Ana hakane kamal yayi ta damun Amma kan takaisu wajan babansu yaga farzeen,tun tana sharewa har ta yanke shawarar kaisu,lokacin farzeen tanada shekara d'aya da rabi,wanda ta shirya suka d'au hanya sakamakon zuwan nasu kuwa zuciyanta ya buga saboda tsananin tunani da tashin hankali kan wulak'ancin da Abdulkareem ya musu,hakanne yayi sanadiyar bugawan zuciyanta cikin Mota kan hanyarsu ta dawowa gida ta rasu.
*wannan shine tak'aitaccen labari kan rayuwarsu kamal*
**********************
Abdul Kareem kuwa lokacinda iyayenshi suka dawo suka tarar babu bintu,tanbayan Abdul Kareem sukayi,nan ya fashe da kukan munafurci ya shirga musu k'arya Wai fita yayi ya dawo ya tarar da ita kwance da wani,kuma Dama an dad'e ana fad'a mishi amma saboda zargi haramun ne,shiyasa bai mata magana ba Se yau da Allah ya gwada mishi da idonshi.
Salati suka soma da salallami,nan yace ai ya saketa,basuwani bashi laifiba nan suka share maganar.
Ana hakane kuwa Allah yasa yasamu Aiki a wani company dayake Adamawa,nan ya tattara ya koma Adamawa shida iyayenshi,cikin k'ank'anin lokaci Allah ya sa albarka yayi arziki,sunkoma da shekara d'aya iyayenshi suka yi hatsari suka rasu,ya rage dagashi sai k'aninshi sai kuma matarshi daya Aura yanzu.
*CIGABAN LABARI*
D'aukan farzeen yayi suka koma gida,Mubarak ma ya biyoshi a baya,tagumi kamal yayi yana tunani yanda zai fara siyar da nono da madara,to mawa zena barin farzeen?
Amina ce k'anwar Mubarak ta katse mishi tunaninshi sakamakon sallamar da tayi,dubanshi tayi tace "ya kamal kawo farzeen muyi wasa"
Ba musu ya mik'ata nan ta zube musu kayan wasa,Amina bata wuce 'yar shekara shida ba,amma tanada ga6an girma Dan zaka yi tunanin takai takwas.
Yana ganin sun fara wasa ya mik'e yashiga d'akinsu,kayan da farzeen ta 6ata ya wanke su tas ya shanya,madara ya tatso ya dafa saboda farzeen,sannan ya d'aura musu shinkafa yanda yaga Amma ta nayi.
Dawowa yayi yasamu Amina tabawa farzeen madara tasha har tayi bacci,dubanta yayi yace"nagode Amina"
Mubarak ne yazo kusa da shi yace"kamal me zai hana kana barin farzeen wajan Amina?kaga ni Se ina rakaka cikin gari siyarda madara da nono"
Shuru farzeen yayi yace"kaga tunda Amma ta mutu farzeen take da kuka,kuma kafin Amma ta mutu na mata alk'awari *NINE GATAN TA*"
Shuru Mubarak yayi sannan yace"to in bakaje tallan ba ya zakayi kabiya Malam sanda kud'in shi?kasan dai bashida mutunci"
Hankalin kamal ne ya dad'a tashi yace"dole haka zanyi,zan samu Ummi,(mahaifiyar Mubarak da Amina) in ta yarda semu bar farzeen wajan Amina".
"Ummi zata yarda mana"
Komawa kamal yayi ya zauna aranshi tunani yake"to yaushe Malam sanda ya siyarwa Amma fili?kuma bata ta6a bashi labari ba,gashi Wanda zai gaya mishi gaskiya Malam hudu ne kuma Allah ya mishi rasuwa,ai na zai samu amsar wannan tanbayar?
For comments only 08144932303
YOU ARE READING
SHINE GATA NA
Fanfictionlabarine me cikeda tausayi,nishad'i,had'eda fad'akarwa,Ku biyoni don jin yanda zata kasance