🏯🏯🏯🏯🏯🏯🏯🏯🏯
⛲⛲
⛲
GARIN BASAM
⛲
⛲⛲
🏯🏯🏯🏯🏯🏯🏯🏯🏯♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
(E.W.F)
{ɧơɱɛ ơʄ ℘ɛą¢ɛ ɧơŋơųγ ąŋɖ ʂų℘ɛγ щγıɬɛγʂ}Story and written by
нαℓєємαтυѕ-ѕα'α∂ιууα🤸🏾♀Aysha Wakili ina miki fatan Allah ubangiji yabaki lafiya,Allah ya yaye maki abunda ke damunki da musulmi gaba daya, yasa kaffara ne. *GET WELL SOON* DEAR🤭( *Readers din murmushin ajali🤡 ataya Aysha Wakili da addua Allah yabata lpya*)
Page *91-95*
Bangaren Muhammad kuwa sai shiga lunguna yake ,a haka har Allah yasa ya tsinci kanshi cikin kasuwar wani gari waishi Fantai,tafiya kawai yake badan yasan inda zaijeba,sai ji yayi an dankeshi tabaya ana shine barawon gashinan aikuwa mutane sukayi kanshi,yasamu ya fizge daker sannan ya diba da gubu suna binshi yana Cewa"Aisha!!!" Aisha shine kadai abunda bakinsa yake fada,Yana ganin wani gida ya afka da gudu tareda shiga dakin farko daya gani.
Ji yayi an taboshi ta baya dan haka yai saurin juyawa yana cewa Aisha"janyeshi baya mutumin yayi tareda bude kofar gani yayi mutane sun cika cikin gidan nashi suna cewa"kawai kabani shi mu kasheshi barawone sata ya......"bai karasaba yajiyo muryar wasu daga waje suna cewa kufito wannan ba barawon bane ga barawon cen ankama"Ai kuwa rii...suka fita cikin sauri.
Mutumin ne yajuyo da kallonsa kan Muhammad yana fadin "Bawan Allah yasunanka"
"Aisha" Muhammad yabashi amsa ,dan haka yatsaya ya karewa Muhammad kallo inda ya fuskanci gaba daya jikin Muhammad bai nuna wata wahalaba ko talauciba"toh amma mai zaisa wannan bawan Allah shiga wannan halin domin daga ganinsu daga cikin jin dadi yafito"Aisha" Muhammad yasake fada,hakan ne yatabbatarwa da Malam cewa Muhammad yayi losing memory,Dan haka yajashi cikin dakinsa yana fadin"kazauna anan ina zuwaKallonsa yayi sannan yazauna,Malam kuma yayi cikin gidanshi yana fadin "kulsum!....kulsum!!"
"Naam Malam ganin nan" tafada tana fitowa daga cikin wani daki. Ina yarinyarna Khadija,tazo ta dama min fura nayi bako"kiran Khadija tayi tafada mata sannan takoma ciki .Juyawa yayi dakin daya ajye Muhammad yana tunanin Allah yasa bai tafiba,aikuwa yadda ya barshi haka yake.
Bayan yan mintuna kadan,saiga Khadija rike da kwarya ahannu,"salamu-Alaikum"tafada cike da nutsuwa.
"Wa'alaiki-Salam" Malam ya amsa mata.durkusawa tayi tareda ajye kwaryar "Baba gashi".
" yawwa Khadija sannu"._GARIN BASAM........._
Labarine ya isarwa mai martaba cewa Muhammad da Aisha tareda Rufaida ba'a gansuba kuma daga yanayin yadda akaga bacewarsu ya nuna cewa bataa kofar fita suka fitaba domin,Masu tsaron kofar dukansu sunanan kuma basuga fitar kowa ba.Hankalin Mai Martaba ba karamin tashi yayiba ina take yajishi tafiyama bazai iyaba,jira suke yayi magana amma sukaga yakasa ,nan da nan hankalin kowa yatashi dan haka akai asibiti da shi."Tashin hankali ba'a saka maka rana,Readers kuzo kuga yadda gimbiya Zainab ta susuce ,batason tanason mijintaba saida taga yazama unconscious ansakashi amota tana zaune gefansa sai kuka take safiyyama tabiyo bayansu a mota,domin ganin condition din mai martaba yatayar mata da hankali.
Suna shiga hospital directly A&E aka wuce dashi.
_CAIRO......._
Aisha ce zaune tana kuka rungume da hamna wacce take baccinta hankali kwance,tunani take Anya Muhammad lafiyarsa kuwa baizoba" mutane babu imani kuraba mata da mijinta,Ku raba Uba ya yarshi,wannan wace irin masiface,tsabar son duniya"tafada tareda kara share hawayen data manta yaushe rabon daya daina zuba.
I'm sorry na Dade banyi typing ba sannan nayi kadan amin afwa su Maimuna Lawan da Maryam gombe yau sai amin magana naga har Fishi ake😜
YOU ARE READING
GARIN BASAM
General FictionLabari mai dauke da tausayi,zalunci,son zuciya tareda sadukarwa