[12/17/2017, 1:41 PM] Feenat Ja'afar: "KAD'DARA CE"....
©...Feenat Ja'afar.
1_" Papa!Papa!! Rigar shi ta ke ja,ya yin da hannunta ke nuni ga motar da ke gefen super market d'in,,"Baby Naina kenan, 'Yar(2years),Ta cigaba da nuna mishi,,"Umm, Umm, "Momma..Da gwarancinta na yara..
Baban ya duko lokacin da ya gama sa kaya a boot,daukar ta ya yi, ba tare da ya kalli inda take nuna mishi ba,dan inda sabo,toh ya saba da hakan,dan duk wata mace,a wajen Naina" Momma "ce,.Ya rungumota yana mai tausayin maraicin su.
Tunda Naina ta rasu,ya zama marayan karfi da yaji, ganan yar tilo data bar mishi,itama ta fara maraicin ta..
Ga baya jin zai Iya maye gurbin Naina da wata mace a Duniya..
Duk yai uwa,yai uba,ya hana kowa Baby Naina tun tana (showel) din goyo,,Iyaye har sun gaji da mishi zancen aure,,ya kan ce shi ya gama aure,sai dai in anayi a Aljanna su kara yi da Naina.
~~~~~~~~~~~~~~
Baby Naina tabi motar Matar data kira da " Momma da kallo lokacin da suka zo wuce wa,da halamun ita ma ta motar bata acikin walwala..Ga bata da wayo,balle ta sanar da papan nata lalle "Momma ta gani,wace kullum yake nuna mata ita a photo,,, maimakon hakan,sai ta kara kwantar da kanta a kafadar papan nata,tare da sa Babban hannu a bakin tana tsotsa,, kai da ka gansu abin tausayi, kasan kuma tabbas suna bukatar wani a kusa, wato" UWA....
Horn yai,Baba mai gadi ya bud'e mishi gate yana mishi sannu da zuwa,kai kawai ya daga mishi,,sabanin a da,da fara'a zai amsa yana mishi ya gida,tun bayan rasuwar Matarshi shekaru biyu,komai ya sauya a gidan da rayuwar mai gidan.
Kaya ya ga ya fito dasu a boot,ga baby Naina a hannunshi,da sauri yaje dan taimaka mishi,,("No,am Ok)..
Baban bai bi ta kanshi ba ya kwashi na kwasa yai ciki dasu,dan in ya biye mishi,ga Y'a, ga kaya haka zai shiga.
Kwantar da baby Naina yai a 2 sitter,har yanzu hannunta na baki tana tsotsa, ya sunkuya ya sumbaci goshinta,ya Debi na fridge da kitchen ya kai,kan ya dawo ya zauna,tare da bude system din shi,,Naina na ganin shi ta taso tare da daura kanta a cinyarshi,,ya kallo tare da Shafa kanta,,Naina akwai hakuri,Kila yunwa ma take ji.("Are you hungry?) Kai ta daga mishi,daukar ta yai,sukai kitchen, ya dama mata(cerelic)ya zuba a pida,,duk tana hannun shi, yasa pidan a ruwan sanyi suka dawo parlour,, yana yi yana taba wa,ya huce,yana bata ta karba kuwa,,daga kwancen ta zuke shi tas.. Yai murmushi tare da mayar da kanshi kan (system)din shi.
By
Feenat Ja'afar
Loading....
[12/17/2017, 1:48 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE"... ©...Feenat Ja'afar.. 2_Wayan shi ne yai(ringing),Hajiyan shi ce,tsam yai,lokacin da suka gama wayar,yai ajiyar zuciya," Allah yasa ba wata aka kara jajubo min ba,,Naina ya kalla,wanda itama kallon shi take, hannun nan yana baki,d'aya na jan jelar kitson ta,yai mata murmushi, tare da shafo kanta,pidan ya dauka yai kitchen, ya dauraye kan ya ajiye ya fito,agogo ya kalla,(5)saura,daukan ta yai yana sanar ta Hajiya na neman shi,aikin da bai karasa ba kenan yai waje. A parlour yai turus,ganin taron yan gidan nasu,yayyen shi da su Hajiya da Abban su,tuni ya fara zama kalar tausayi,dan yasan zancen d'aya ne,wato yai"Aure. Bayan ya gaida su,Naina tai wajen kakanin ta, Abban ya kallo shi, kai ya kada, Faruq sai shi,in bai da gaske ba zaya yai ta zama a haka ba aure ne, "Um Baba na? Kallo Abban yai,tare da amsa wa.." A karan nan kam bamu bukatar yardar ka, ba kuma shawara nake nema ba,mun Riga mun yanke hukunci, a satin nan zamu hada auren ka da yar wajen kawun ka Muktar..da sauri ya dago ya kalli Abban,sai dai karan nan ya kula ba sassauci a Abban,d'aya bayan d'aya yake kallon su,duk ba dama,tuni ya zamo kasa,gwiwa biyu ya zube,"Abba kai hakuri dan Allah a duba lamari na, wallahi bana bukatar mata,kuma ma...Hannu Abban ya daga mishi,"ai na fada maka, ba shawara ko yardar ka nake nema ba,mun gama yanke hukunci da kawun ka,tun a kwatano,yau suka zo garin nan,kuma a satin nan za'a daura su juya..ido ya rintse,,baza su gane ba inda ya dosa,amma shi ba mace a agendern shi yanzun.. Aunty Salma ce ta katse mai tunani,"Yanzu Faruq, kodan baby Naina ai zaka so aure kusa,in akai la'akari da mace ce,dole zata nemi uwa kusa..kai yahau kada mata,"Aunty Salma,Naina bata bukatar uwa kusa,ni zan zame mata uwa,dan Allah kisa baki a lamarin nan,gaskiya bazan iya wa Naina kishiya ba...Tashi su Abba sukai,dan ganin zai fara sambatun nashi,, Hajiya ma ta bishi,duk ya bisu da kallo,Aunty Salma kadai ta rage,ido ya rintse,sai ga hawaye ya zubo,tun bayan mutuwar Naina basu taba tilasta mishi ba,kullum lallaba shi suke,in yace baya son abu haka zasu bishi da hakan,amma karan nan ya san ba nasara. "Faruq, kai hakuri ka dau auren nan,dan(same boat)kuke da wacce za'a bakan,sai dai ita ta amince cikin sauki,Laila ce fa,yar gidan kawu Muktar, tahau bashi tarihin ta a takaice,sai dai shi,ba abinda ya shiga kunnen shi,ya Lula a tunanin taya zai wa Naina kishiya?..." Bari nazo da ita,kallon ta yake,harta shige ciki,, tashi yai ya koma saman kujera,sai ga Naina Abba ya sakko da ita,tazo wajen Papan ta,kai sunkuye yai mishi a dawo lafiya. Bude kofar ce ta a Naina kallon wajen,hannun ta ta cire kan ta furta"Momma? kan tai wajen su,kai ya daga,dan a tunanin shi da Aunty Salma Naina take,sai dai mey? A zabure ya mike,baki sake yake kallon Laila,lokacin da ta dau Naina,Aunty Salma tai murmushi,dan tasan hakan zai faru,dan rabon shi da Laila tun tana yar (7years),a kuma kaf Familyn su, Laila da Naina suna matukar kama da juna,,har maganar su. Zama sukai,Shima ya rintse ido lokacin da ya gane lalle kama ce,wannan tafi Nainan shi tsayi da haske. "Umar, ga nan Laila,bari na dawo,kai kawai ya daga mata,a hankali tace mai " ina wuni,ido ya kara rintse wa,maganar Naina sak,kamar an sikare shi ya tashi ba tare da ya amsa ba,kar ta dawo mishi da hannun agogo baya,hannu ya mikawa Naina,ta sakko,uffan bai ce ba sukai waje,dago wa tai tabi bayan shi da kallo,kai ta kada, ashe tsugunne bai kare mata ba,hannu tasa, ta goge hawayen d'aya zubo mata,kila ita tata K'ADDARAR CE haka,wato Rayuwa cikin kunci.. Tunda ya koma gida yake kai kawo cikin parlour, yau komai ya dawo mishi wani iri,daga kallon ta ya rasa nutsuwar shi,ga Naina sai Momma take kira,duk ya rasa inda zai sa kanshi,yau bacci sai barawo. Sati nayi aka daura auren shi da Laila, fur yaki zuwa,Abba yace koda shi ko babu aure kam ba fashi,haka ya tattara yai office dan bawa yan gyaran gida waje,duk da weekend ne,dare nayi aka kawo amarya dakin ta,sai yau suka samu damar jirge kayan Naina a dakin ta, shima ganin ya bar gidan,tun rasuwar ta ya hana debe wa,hatta kujeru an debe,dakin shi ne basu taba ba. Haka kowa ya watse aka bar Naina da Laila,,bacci take a cinyar ta,ita kam in banda hawaye ba abinda take,ta sani bayan biyayya, ba abun da zai sa ta auri Umar,duk wani namiji baya burgeta in ba Mas'ood din ta ba,kwantar da Naina tai,kan ta zuge jakar ta ta dakko kara min(frame),murmushi yake kamar kai kiran shi ya amsa,"Mas'ood",ta furta a hankali tare da rungume hoton, rintse ido tai,hawaye nata gudu a fuskar ta,,"Rayuwa tai min zafi Mas'ood, saboda kai,,"mey yasa zaka tafi kabar Lailan ka a tagaiyare?..ta cire hoton a jikin ta tana shafo fuskar shi,"mey yasa ka saba alkawarin da mukai wa juna da kai? "Haba Maj'nuu,ance rabuwar mu K'ADDARA CE, toh mey yasa ni tai mun haka? Kuka take tana sambatu,inka ganta tamkar wata zararriya,ta shafe awanni kan bacci ya sure ta rungume da hoton Mas'ood din ta. By Feenat Ja'afar "K'ADDARA CE"... ©...Feenat Ja'afar.. 3_A bangaren ango,yana shigo wa yai turus,ganin an sauya mai parlour, lalle bazai shirya da auren nan ba,da sauri yai dakin Naina,komai an sabon tashi,ya bugi kofar dakin,kamar ya zunduma ihu,wato sunce basu taba kayan Naina ba,shine aka cire suka zuba na wata??... Yai kwafa,dakin baby Naina yaji kamar ana shesshekar kuka,yai kwafa tare da yin dakin shi. Gado ya fada,tare da dafe kai, yau ga wata a gidan nan ba Nainan shi ba..hawaye ya fara,lalle mutuwa mai yankan kauna,a yau ya tuno da daren farkon su a gidan nan shida Naina. Hoton ta ya jawo,tamkar karamin yaro haka yake shafa hoton yana kuka," (am really sorry Naina),yau an miki kishiya,ki gafarce ni,ban so ba akai,(believe me)..ya rungume hoton yana ta sambatun shi,har bacci barawo ya tafi dashi. Washegari da kuka Naina ta tashi,Papa kawai take kira,Laila ta rasa ya zatai da ita,gashi asuba ne,gari bai ma waye ba,sabar ta tai sukai waje, taje dai dai kufar da ta kula nashi ne ta kwankwasa,shiru kake ji,ga Naina taki shiru,kofar ta kama,a hankali, sai kuma ta cika,ido ta rintse kan ta tura kofar,wayam ba kowa,Kila yana masallaci, Naina ta sakko,ta fara shafa kanta,"Sorry baby,ta marai rai ce fuska,tuno wa tai ko yunwa take ji,sai tai kitchen, ganan pida tafi biyar a ajiye,gwangwani cerelic ta gani,da sauri ta kunna gas,ta daura mata ruwa,,dankwalin ta ta kunce,kan ta dau Nainan ta goya ta dashi tana dan jijjiga ta,lumm ta nutsu a bayan Lailan,dan rabon ta da goyo tun tana showel,tun zaman Ya Kumbo gidan,ana wata biyu yace taje zai iya. Parlour tazo tana kokarin kunto ta ya shigo,kuka ta fara bata son sauka,da sauri ya karaso tare da kiran ta,dago wa tai ta kira shi,tun jiya rabon da taga papan ta,Kunce ta Lailan tai,tuni ya sunkuci abar sa,wani irin kallo yake watsa mata,kamar wanda tai mai babban laifi,kasa tai da kanta,kan ta mai ina kwana,ko ta kanta bai bi ba yai daki da yar shi,kai ta kada, ,pidan ta kalla,sai ta dauka tare da zuwa bakin kofar tashi,(nocking)ta fara a hankali, a fusace ya ajiye Naina yai kofar,cikin tsawa yace "mey akai kuma?.. a tsorace ta mika mai pidan," Ba yanzu ba,haka kawai yace ya rufe kofar shi da karfi, ido ta rintse,sai ga hawaye ya fara ambaliya,jiki a sanyaye ta koma kitchen ta ajiye,daki ta shiga,tare da fadawa gado, sana'ar ta ta fara,wacce ita kadai ke sa taji sa'ida. By Feenat Ja'afar