[12/17/2017, 1:50 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE " ©Feenat Ja'afar 9_Murmushi take,har hakorin ta na fito wa, a hankali ya furta "Naina".. Dan gaba d'aya ta rikide mai ita,barin da take murmushin,,gaban ta ya je ya tsaya,murmushi ya fara tare da sa hannun shi a nata,,murmushin tane ya karu, a nata shirmen Wai ko Mas'ood din ta ne,,sai ta kara rintse hannun tana dan magana a hankali, ido ya rufe shima tare da yin abinda tayi,, walkiya akai gaba d'aya ta haska wajen,wata tsawa da akai ce tasa ta tsorata tare da fadawa jikin shi ta lafe,,,ajiyar zuciya suka sake a tare,da sauri ya kara kankame ta,a hankali ta furta("I missed you Maj'nu).. Hawaye ya biyo baya,,("I missed you too Naina)... K'wak'walwar tace ta fara dawo wa saiti lokacin da ya Ambaci Naina,da sauri ta bude ido,dan tunawa da a duniyar da take,,kiciniyar kwace wa ta fara lokacin da ta tuno a kirjin wa take,,sai dai shi kara kan kamo ta ma yake,dan jijjiga ta yake yana" (Don't leave me please Naina,I can't take it anymore,, please I really missed you)... Ido ta runtse, tare da sakar kuka a hankali, "wayyo rayuwar ta,ya akai haka? Mas'ood take bidar ji ba Faruq ba." Laila wanda ya mutu baya dawo wa...kuwar wata zuciyar tata,sai ta kara kuka akan na da,shikam sai dan jijjiga ta yake. Chak! taji numfashin ta da kukan ya tsaya,sakamakon jin bakin shi datai a wuyan ta,ido ta rintse,"taya zata fara kwatar kanta?..Lalle tasan baya cikin hankalin shi,gaban ta ne yahau faduwa,take tsoron shi ya dirar mata,tayi imani in ya dawo yasan itace toh tasan sai buzun ta. Sai dai mey? Kan ta ankara sai taji ya bala'in zarme wa da yawa, Naina kawai yake kira murya na rawa,,a zuciyar ta fada mishi take"ba Nainan ka bace Laila ce,sai dai tsoro ya hana ta baiyana. Batai aune ba taji ya tushe mata numfashin ta da hancin shi yana,kokarin kwace kai take,sai dai ina,tuni ya kara furgice mata. Chilak ya dauke ta suka bar cikin ruwan,k'ugiyar son Naina da tsohuwar zuba sai janshi suke, sai da sada ta da gado tukun. Take ta kara matse ido ta kan kame jikin ta, burin ta kar ya sa ta saba alkawarin ta da Maj'nu na zama tashi shi kadai,,,sai dai shi a nashi bangaren yai zurfi, da taimakon sanyayyar iskar da ake tare da rashin wutar gari yasa hankali kara gaba,a hankali yake binta,tare da rada mata zantuka,wannan bata ma sanin kansu,,,burin shi kasancewa da Nainan shi a dis moment ne kawai. Hawaye kawai ke kwarara mata tsawan awa guda,jitai wani mugun tsanar Faruq ta mamaye ta take,,burin ta dama a halin da suke Allah ya dau ranta ta huta ko taje ta samu maison ta. Lalle rashin mai sonka a kusa da ciwo,sai dai suna manta dukkan abu K'ADDARA CE daga Rabbi. Zuwa wani lokaci kadan ta daina jin sambatun zarewar shi,ajiyar zuciya yai,halamun mai bacci. A hankali ta zame jikin ta tare da jan bargo. Baya ta juya mishi tare da cigaba da rera kukan ta,,duk ta takure kanta,ji take tamkar ta sabi mahalliccin ta,tayi da na sanin futar ta tafi dubu. NEPA ce ta dawo,iyanzu yayyafa ake,Naina ce ke ranta, burinta kar ta tashi taji ba ita,,a hankali ta daga kanta dan neman agogo,(8:15pm)a hankali ta juya tare da jan rigar ta a hankali, saura rabi ta cire yai dai-dai da kukan Naina da ihun kiran Momma,kamar a mafarki yake dan jiyo kuka,a hankali abubuwa suka fara dawo mishi,,a razane ya mike zaune harda salati,jikin shi ya kalla,da sauri sannan ya kalli Laila data sunkuyar da kai hwaye na zuba rike da blanket a kirji,,ido ya rintse tare da cije lebe,, By Feenat Ja'afar
[12/17/2017, 1:51 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE " ©Feenat Ja'afar 10_A hankali ya furta"Ya ILLAHi"..Ido ya bude yana kallon ta da sababi,,kiciniyar sa riga ta fara,bai jira ba ya fara sauke mata taburmar kunya,,iyanzu burinta tai wajen Naina mai kuka kamar ta shide. "Shikenan kin samu abinda ranki yake so koh? Shikenan kinsa na karya alkawari 4(and all because of you)da tsawa ya karasa,tuni ta dira a kasa,tare da zaro ido,dan a zaton ta marinta zai,,ilahirin jikin ta karkarwa yake,ga wani sanyin zazzabi daya fara shigarta. Da tsawa ya sake fadin, " (what are you waiting for?)sai wani zare mata ido yake,,"ba burin ki ya cika ba? Toh Oya,bace min,a razane ta kallo shi tama kasa koda daga kafarta,,(I said get lost),,ai ba tasan sanda takai dakinta ba. Da sauri ta rufe kofar tare da danna jam lock tamkar zai biyo ta... kallon Naina data kifa kai tare da yin goho tana kuka take,ita kwa jin rufe kofa yasa ta dagowa da wuri,,"Momma "..cikin kukan shagwaba ta kira ta,zame wa tai daga jikin kofar tai kasa tare da sakar wani irin kuka mai cin rai,,kanta take dokawa a kofar a hankali tana matsar kwalla. Jin an dafata ne yasa ta bude ido da sauri, Naina ke kallon ta itama tai narai-narai da ido tana shirin kara wani kukan. Hannu Nainan takai tana mai goge mata hawaye kamar kullum tana girgiza mata kai halamar tai shiru,da sauri ta goge hawayen tare da janyo ta jikin ta,," (am sorry baby,,)"Momma ce? Kai ta daga mata tare da kwantar da kai a jikin ta,tashi tai tare da kashe fitila dan yanayin da take ciki rigar a jike,,a hankali ta lalubi wayar ta tadan danna,ajiye ta tai kanta bude drawer ta dau zani ta daura,kunna wutar tai,kamin tace tai hakuri zata je bathroom tai wanka,kai ta daga mata tare da sakko wa,a kofar ta rakabe jiranta ta fito. Ruwa ta fara sakarwa kanta,tuni wani irin dumi ke zuba a jikin ta yana bin kasa,,kuka sabo ne ya dawo mata lokacin da take tuno abinda ya wakana,sai dai ta dau aniyar dan ba kara kuma. Ina wajen Faruq????? By Feenat Ja'afar ®NGRT WRITER'S ASSOCIATION (NWA)
[12/17/2017, 1:51 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE " ©Feenat Ja'afar 11_Tun futar ta ya dafe kai,"mey kenan hakan yake nufi? Ya akai tazo nan har ya kasance da ita,Ya Salam,hoton Naina ya kalla tare da furta sunan ta da wani yanayi"Naina"...bai san mey zai sanar wa da Nainan ba,gani yake kamar yaci amanar tane,hoton yakai hannu ya kifa shi kamar mai kunyar hoton...hakika ya zubar da girman shi a wajen ta,kila ma ta rainashi daga yau,sai dai a yanayin jikin shi ji yake kamar ya sauke wa kanshi wani nauyi ne,tashi yai ya lallaba bandaki. Da sanda ta bude kofar ta dan leka, kitchen taje ta rufe kofar sannan ta daibar musu abinci ta dawo daki,,waya ta dauka tare da kiran Momyn Mas'ood, tasan iyanzu idon su biyu,kila in taji muryar ta kamar taji ta danta ne,sai dai fur network ba kyau. Washegari tun wuri ta gama abincin ta ta koma daki kan ya dawo daga jogging, har yabar gidan bata yarda sun hadu ba. Kan ya dawo ta gama komai ta ajiye mishi abincin ranar shi,iyanzu kam ya saduda cin abincin ta,in yana ci har wani lumshe ido yake,tun shekara 2 dakan shi yake girki,in yaji baijin na gida sai yai restuarent,bai zuwa gidan su bare suga gazawar shi,,yaga ba sarki sai Allah, (hmm waya fada maka Borno Gabas take?). Tun daga ranar suka fara wasan yan buya dashi,takan aika Naina wajen shi dan ta fita laifi. Misalin karfe (5pm) Maman Nana tai sallama makociyar ta,da fara'a ta amsa,,ta karbi Nana, "mu ai fishi muke Momman Naina,, dariya tai kan tace" ai mana afuwa zamu shigo,tace"hmm haka dai kike fada,bazan iya kirga zuwa na gidan ki ba,Allah a duk Arean nan ke kadai na yarde wa zuwa gidan ta,gani ba yar gari ba,ke kuma kinki a saba,,murmushi tai tare da kallon Nana dake ma Naina dariya,,"kiyi hakuri,tunda nima nazo gidan kusan wata biyu sau d'aya naje gida,amma nai miki alkawarin zuwa miki cikin satin nan,,kai ta kada mata tana tunanin maganar ta,kamar ya tunda tazo gidan nan wata biyu? Kallo ta tai,da halamar tambaya,, sai dai tai shiru tana kallon Naina,,yarinyar tana mata kyau musamman wannan (special hair styles)din Lailan, ta shafo kan Nainan,"kai Mom Naina Allah bamu gashi muma ana mana irin haka,tai murmushi tare da shafa kan Nanan, "a zatai ne,,magana a takaice take yiwa Maryam din,dan ta gagara sakin jiki da ita har yanzun sosai,duk ita bakinta a bude yake. Abin sha ta dakko mata,tana dan janta da fira a haka har suka zurma,sai da taga ta saki jiki da ita sosai a yau kan ta tafi,sai dai tana da tambayoyi da yawa a kanta,dan sau biyu Faruq ya same ta a gidan,a kuma yadda ta fuskanta kamar basa zaman lafiya,sai dai Laila bata bata fuskar tambayar ba. Zaune suke ta kunna dish suna kallon Tom and Jerry a mbc3,dariya suke ita da Naina,dan tana son tom and Jerry,musamman na yar tsuntsuwa,,ita kuma Naina cartoons din ne suke bata dariya in suna gudu, gani take kamar Teddyn ta ne. A gajiye ya dawo,dan tun fitar shi bayan la'asar,kofar parloun ya bude,lokacin Naina na gwada mata yadda yar tsuntsuwar take yi a tana tafiya bayan an sako wani sabo," Momma cheddy ta fadi (I try I try,but no body loves me,)sai tai dariya,harda harde hannu irin na tsuntsuwar tana yin kalar tausayi,tana"(I wish I can swimm)... Dariya Lailan take harda rike ciki,,takanyi mamakin Baby Naina yadda a take take haddace abu. Rufewar kofar parlourn ne yasa tai saurin kallon kofar,tsaye yai yana kallon su da murmushi, sai dai suna hada ido da Laila yai saurin gintse wa,kai takai kasa,tare da barin dariyar gabanta na faduwa,dan tun wanchan ranar rabon ta da ta yarda su hada ido yau kwana biyu,sai yau daya ritsata.. Ga kallon TV ga dariyar da baya fatan tayi. Ciki ya shigo Naina tai wajen shi tana oyoyo,nuna mishi TV take tare da bashi labarin yar tsuntsuwar ciki, kan ta nuna mishi karen ciki wai Berry ne.. Murmushi ya zauna,tare da dan satar kallon Lailan,riga da skirt ne yan kanti blue da ratsin flower orange, ta kama kanta da ribom sai k'yallin mai yake da kamshi,kamar kullum haka yauma powder fara kawai da lip gloss tasa amma tai kyau kamar wata baby,da sauri ya dauke kanshi ya fara biye wa Naina. A hankali tai mishi sannu da zuwa ba tare da ta dago ba,shiru ta ji kamar yadda ta zata. "Ki shirya gobe zaki fita.. Sukai daki shida ya'rshi, ajiyar zuciya tasau,ganin bai sauke mata sababin ba. A daki Naina duk ta dame shi da surutu,wanda aksar na Momman ta ne,karfi da yaji so take sai tai fira da dan guntun hausar ta,inta kakare tamai da turanci,, kanta ta dafa cinyar shi take nuna mishi,,ya shafa gyaran gashin nata,kullum kan sake yawa yake da kyau,tana samun matukar kulawa,sai dai taurin kanshi ya gagara ya yaba mata har hakan yasa ya sarara mata. Murmushi yai kamin ya dago kanta,("wow my little Angel,u look so pretty),kumatun ta yaja a hankali, duk sun fara zama lufu lufu,sai murmure wa take abunta. By Feenat Ja'afar
[12/17/2017, 1:52 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE " ©Feenat Ja'afar... 12_Washegari gidan Aunty Salma suka sauka,ba yabo ba fallasa ya nuna wa Aunty Salman, ganin hakan yasa tace ya barta anjima sa tafi tare gidan Hajiyan. Aunty Salma ta kallo Lailan,"Laila naga chanji a tare da Faruq a yau,tabbas kin cika y'a ta k'warai, mun gode da(sacrifice)na farin cikin ki da kikai dan ceto shi...kasa tai da kai,tuni ta fara hawayen zuci, da sun san abinda take diba da kila su ce ya sauwaka mata,dan ba tajin zata iya tankwasa Faruq,musamman ganin tsoron da take nashi,,,kamar Aunty Salman ta san abin da take tunani ta dafa ta, "na sani Laila kin daure ne kawai,amma ina rokon ki kodan Naina ki kara hakuri,sannan kiHajiya,ita adu'ar ya'yewar bakin ciki. Kai ta daga tana kallon Naina da take kallon ta," InshaAllah Aunty,sai dai kuma...sai ta kasa fada,,"no ki fadi abinda ke cinki Laila kar ki k'wari kanki.. "Ba komai,k'ema Aunty ki tayani da adu'a,murmushi tai,dan tasan kawai ta fada ne. K'arfe biyu suna gidan Hajiya,achan itama zancen kenan ta kara hakuri,in ta kira yan kwatano ko sun kira ta suma zancen kenan," ki kara hakuri,shin suna fuskantar halin da take ciki kuwa? Lalle da tasan haka zata tsinta a gidan Faruq da bata yarda da auran ba. Sai(9pm)suka bar gidan,a mota duk ta tsunduma tunanin maganganun Aunty da Hajiya, na roko da ban baki,rokar ta suke duk abinda tasan yana mata da bata so ta sanar ma Hajiya,sai dai ta kasa fadin komai,kuma ta rasa dalili. A dan sace ya kallo ta,"kuna son wani abu?..kai ta duk'ar kan ta kada mishi,"babu,, parking yai,ya siyo musu kayan k'wadayi. Daki ta wuce da Naina datai bacci,ta kishingida,yau an kara daure ta da jijiyoyin ta, su Hajiya sun sake karya lagon ta,a hankali taja numfashi ciki,"Allah na yi iya yina,ya Allah ka tayani sauran. Bayan kwana(2) da haka suna d'aki ita da Naina suna 1,2,3..sai dai da alama yau yan karatun basa kusa na Naina,ita kawai burinta wai Baba mai gadi ya kaita wurin Nana,,t'sam Laila tai,ya kamata yau ta leka ma Maman Nana, bawai tai ta tura mata Naina ba,(at least)ta nuna mata so,,toh amma ta ina zata fara tunkarar shi da batun fita? Dabara ce ta fado mata,sai ta yagi takarda ta rubuta ma Naina wai ta ba papan ta sai ta zo suje gidan su Nanan,,da murnar ta tai dakin,ya gama shiri zai fita kenan (5)ta kusa yaji bugun Naina,kofar ya bude,da sauri ta bashi tace"Momma " zata juya,ya kira ta,,"inda hali muna son zuwa mak'ota gidan Maman Nana "..sai yaji haushin tambayar.(reply
)ya mata a kasan rubutun tunda tafi karfin tambaya da baki," ba hali,,ya ninke ya bawa Naina,,data karanta sai tai parlour, dai dai ya fito suna hada ido ya dauke kai. By Feenat Ja'afar
[12/17/2017, 1:53 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE " ©Feenat Ja'afar 13_Naina ya daga wa hannu,sai ta biyo shi, da sauri tace"dan Allah ka barmu muje kusan kullum tana hanyar gidan nan... Kallon ta kawai yake,kan yai waje shida Naina,a kujera ta zauna,tana tunanin wani iri ne Faruq? Da Allah ta hadashi fa? Tai k'wafa. Sai ga Naina da paper a hannu tana bata tare da jan hannun ta wai suje,, bude wa tai,"ki je"..shine abinda ya rubuta,(4 d first time)da ya sata murmushi,,Naina ta jawa hannu lokacin da taji fitar shi daga gidan sukai daki,takalmin ta na hannu,tasa mata,tare da daure bukle din,,powder kawai ta mutsuka as usual, dama basu jima da wanka ba,gyale ta zara, (5:09)suka shiga gidan Maman Nana,, da murnan ta tare ta wai ta mata ba zata, murmushi kawai take har suka gaisa. Maman Nana aiki ya kawo mijin ta Adamawa,sai kuma ya kasance makota suke da Lailan,an kawo Laila da sati suka zo unguwar, duk da estate ce ba da wanda take hulda sai Lailan.. sai dai yadda ta fuskanta kamar ita batta saurin sabo,yaranta biyu suna rasuwa wajen haihuwar su,sai Nana. Naina ta kalla lokacin da take wa Nana wasa a sittern ta,ta jiyo kan Lailan, "kai mom Naina halamu ya nuna Naina na bukatar k'ani fa,,,murmushi tai kan ta kalli Nainan,Maman Nana tace" ko ba haka ba Naina?? Nainan k'ai ta daga mata tana ma Nana dariya,,tace"toh kinji,dariya tai mata, kan ta kada kai.. "Amma kin mata ya'yen wuri ne shi yasa,,Nainan Lailan ta k'alla, kan ta dawo kan Maman Nanan,," ba ni na haifi Naina ba fa Maman Nana...Baki ta saka da kamar mamaki,"kar dai kice min kema kunyar y'ar fari kike mom Naina? In ba haka ba ko makaho ya laluba yasan Naina jinin ki ce. Murmushi tai mata,kan ta k'ada kai,"Naina jini na ce Maman Nana, amma ba nice na haife ta ba. Da mamaki Maman Nana take kallon ta,sai ta kalli Nainan,,"kai mata,ban yadda ba,,cikin murmushi Laila tace"Allah da gaske. Ido Maman Nanan ta k'ank'ance, "toh wace ce Maman ta? Laila tace" Naina ce"....Dariya Maman Nanan take,sai ta zata wasa take mata,tace"toh waye Baban ta? Ta sake murmushi, "papan Naina(of course)Umar Faruq... K'ada kai Maman Nanan tai, kan ta tashi,Jug ta dakko da tsimin B'aure ta zuba musu a cup kamar juice,," toh in tambaye ki mana? Kai ta kada mata, dan taga har yanzu wasa ta dau abin,,,"tunda naga kin dage har da wallahin ki,toh ina son sanin mutane uku...... wace"Laila"?.. wace"Naina"?... Sannanan waye"Umar Faruq"?.. Toh fa...ku biyo yar mutan Yobe,dan jin cikakken amsar Tambayoyin nan.... By Feenat Ja'afar.
[12/17/2017, 1:53 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE " ©Feenat Ja'afar 14_Umar Ahmad Umar(Faruq),Naina Aliyu Umar,da Laila Basir Umar K'akannin su d'aya,duk din su ya'yan w'a da k'ani suke,Inna Bilki ita ce babba,sai Alhaji Ahmad baban su Faruq,sai Baffan su Ali,kan Baban Laila,Baffa Basiru,, su hudu ne a dakin su,,asalin su yan Yolan ne,yan cikin garin Mubii,Inna Bilki yaran ta (3),yayin da Baban su Faruq suke su hudu,,Abubakar,Usman,Aunty Salma,sai Umar mai sunan kakan su,(Faruq). Familyn su masu hadin kai ne,kowa yana matukar girmama kowa,kila hakan baya rasa nasaba da zama a gida d'aya. Hajiyan su mai son yara ce musamman mata, ga d'aya Allah ya bata,hakan yasa take rikon ya'yan k'annen mijin, sai dai duk daga sun dan tasa suke tafiya,ana nan aka haifi Naina yar Baffa Ali da Laila yar Baffa Basiru,,tsakanin su baifi wata biyu ba,,tun daga yaye Hajiya ta dauke Naina,sai dai sabon su da Laila yasa itama ta biyo ta,haka ta hadasu su biyu tai renon su,,sai kuma akai katari jinin Naina yafi haduwa da Faruq akan sauran yaran da suke dauka,,Kowa a gidan naji da Naina da Laila,in ka gansu tamkar Twins, fari d'aya tafi d'aya kawai, duk da yake Laila na tafiya gida in son chan ya debe ta,, Faruq yafi su sosai,dan a lokacin zai tafi secondary school El_kenemy dake Maiduguri. Daga baya su Laila,watoBaffa Basiru ya koma kwatano da zama,gidan ya dawo sai Naina. Shekara (10) bayan wannan,daga nan ne komai ya fara. Tun daga kasa take kwadawa Hajiyan kira,har tai sama,Hajiyan da ta bude kofa,"nikam wannan irin kira kamar na tashi sama? Cikin shagwaba ta fara"Shine kika gudu dan nai bacci? Taje ta lafe a jikin ta, "nifa banson kimin nisa Hajiya,Allah, sai nai kuka.Kallo ta Hajiyan take tare da rike baki,," Tunda kuka baya miki yawa ba,,tuni kwa ta fara sheshekar shagwaba,Hajiyan ta hau lallashi,, "Naina ina jin jina wa mijin ki,dan ba mai daukar wannan shagwabar taki sai ni,,murmushi tai,kan ta dago daga jikin ta suna sauka kasa," nifa Hajiya Miji na sai dai Ku bashi d'aki anan,,dan ba inda zan tafi na barki. Murmushi Hajiyan tai mata,lokacin da suke zama a kan kujera,tuni ta zame kamar mage ta daura kanta a cinyar Hajiyan. "In banda shirmen ki Naina, wa kika taba gani an bawa mijin shi d'aki acikin gidan su?kai ta kada mata"sai ni toh,dan ba inda zani na barki,ta juya tare da rirriko cinyar ta,, murmushi tai,tare da tuno itama ranar rabuwar ta da Naina,sai dai tasan aure ya zama dole...jijjiga mata cinya taji tana yi," Hajiya ina ta magana,,da sauri ta kallo ta,"mey kika ce? Tace"Yaushe Yaya zai dawo? Murmushi tai tare da gyara mata gashin ta da ya bazo mata. "A satin nan zai dawo..a zabure ta tashi ta zauna,tare da k'ankamo Hajiyan,,"wayyo dadi,, dariya take mata,tana. "toh karya ni ki huta,,,cika ta tai ta hau lissafi, sai kuma ta bata rai," ni yanzu a satin nan fa zamu koma Hajiya? Sai ta kwanto mata ta fara mata kukan shagwaba,"nidai a dawo dani day,dan Allah Hajiya,rabon da naga yaya kusan shekara, kullum cikin sab'ani muke,,lallashi Hajiyan ta fara,"kiyi hakuri, ki raka shekarun da suka rage miki,ki dawo mu zauna duka ma gaba d'aya... Lamo tai a jikin ta, ba ranar da in zata makaranta ba ai artabun da ita ba,ta tsani Boarding school, kodan rabuwa da Hajiyan ta. Abba ne ya shigo yana musu murmushi, "auta da Hajiyan ta,, ana ta taba abun ne? Murmushi tai kan ta sadda kai kasa," sannu da zuwa Abba? tashi tai ta karbi ledar hannun shi, kanta ya dafa,,"Yauwa Nainan Hajiya,ya gida? Ya shirye shirye? Da fatan kin fara shiri? Gun- guni ta fara,yai murmushi,tare da ruko ta su zauna"Naina da haka ake makarantar, kiyi hakuri ki gama tunda kin kusa,daga nan kibi sahun yayan ki Zaria koh? Kai ta sadda tana murmushi, chan kuma ta dago,"nidai Abba sai ya Faruq ya dawo zan tafi,in yaso ayi report, banni lafiya kawai, kaji Abba? Ido ya zaro"karya kenan Naina? Ta girgiza kai tare da karyar da kai tana kallon Hajiya,halamun tasa baki. By Feenat Ja'afar
[12/17/2017, 1:54 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 15_Hajiyan ce ta sa baki da lallashi, "Alhaji ai hakuri ko kwana biyu ta kara,,kallo su yai," toh in an koro miki Y'a ni ba ruwana,dan kun san ba'a kara hutu,, da sauri tace "InshaAllah ma baza a koro min ita ba,,ya kada kai" Toh Amin,kan ya tashi yai sama,,da sauri ta rukunkume ta,"kai Allah ya bar min ke Hajiya ta,murmushi tai kamin tace"toh barni na je gun Abban naku,da sauri ta chinnu baki gaba,,"toh karki jima Hajiya,,pls? Baki Hajiyan ta rike,kan ta mata dakuwa"kinci gidan Ku, kaji min Y'a? Toh sai na jima din. K'afa ta fara bubbuga wa a kasa irin na shagwaba,, kai ta girgiza Hajiyan kan tai sama,,"maza kan na sakko ki daura mana ruwan tuwo,yamma ta kusa. A kitchen tana abinci tana ta murmushi ita kadai,harda dan tsallen ta,murna fal ranta, zata ga yayan ta week din nan,tai missing din fitar su yawo da saya mata ice cream. Da dare kamar kullum sun taro su ukun su suna cin tuwon dare wayar telephone din parlour tai kara kirar Nokia.. hannu ya side yana dubawa,,Laila zata tashi yace ta zauna ya koshi shi,,hannu ya wanke kan ya dauka,daga kwatano ne,Naina tana ji ya ambaci suna ta hau murna,kira take"Abba kace Laila,yai murmushi, "ga nan mutuniyar na neman Laila,daga chan Baffa Basirun yai murmushi, Mamyn su Lailan ya kalla,yai mata halamun tai kiran Lailan,,tashi tai tare da dosar dakin nata,tai rub da ciki a kan gadon su tana kallo hawaye shabe-shabe a fuska,,mamyn tai sak'akare tana kallon ta,Tvn ta kalla, a sama taga ansa " Vivah"kai ta girgiza,kan ta tsaya a gaban Tvn,"hawayen mey kike Laila?da sauri ta kalli mamyn nasu,sai ta sau kuka tana nuna mata tvn cikin shagwaba,, Tvn Mamyn ta kara kallo,kan tai murmushi, "Allah ya shirye ki Laila,,,baki ta tabe irin na shagwababbun yaran nan,Mamyn ta juya tana kallon K'annen Lailan da sukai bacci,kan ta dawo kanta," ganan Naina online,in kin gama kukan kya zo..ta wuce tana tunanin shirmen Laila,baci yai mata yawa,in ba haka ba meye abin kuka wa film? baban ta ya gama batata. Parlourn ta fito,duk jikin ta yai sanyi, film din ya bata tausayi,Abban ya bata,gaisawa sukai dasu Abban kan ta karbi wayan tai d'aki. Nan suka kare a firar su kamar kullum,tace suma zasu zo sallah,kan sukai sallama.Tunani Lailan take,rabon su da Nigeria kusan (5years),tana daukin sallah tazo suje,tana matukar son 9ja,sai Abban su shi yaje ya dawo,sai kuma waya da kusan kullum suna manne da Familyn. Taja gauran numfashi, kan ta kunna kallon ta da ta sa (pause),taci gaba. Washegari Laila tai shirin zuwa shagon inda take siyan CD plate dinta ita da k'anin ta,kusan unguwar zango duk ire-iren su Lailan ne,sai yan Niger. Da French ko kwatakwali suke gaisawa yana mata tsiya wai matan shi,ita kwa sai zurma shi take, tuni zai fara fito mata da kaset iri iri kyauta. Yauma kamar kullum sun gaisa yana ta yage mata baki,,yake itama take mishi,tana kara zuga shi,wani ne yazo shagon,da zuwan shi ya sau ajiyar zuciya, "Thank God..ya kalli mey shagon,yadda yake zazzaga yaren su,,toh taya zai fada mishi wane iri yake so? Yasan aksar ba turanci suke ji ba,sannan basa jin Hausa,shi kuma bai iya French ba,sannan bai iya yaren su ba,kodan yarbancin da yaji wasu na tabu kawa shi bai iya ba. Ya furzar da iska,,gaskiya Momy yau ta sashi aiki ba karami ba,dakyar fa ya samu shagon, gashi kuma yazo bai san yadda zai tambayi a bashi Hausa film ba. Kurmanci ya tuna,sai yai murmushi, kan ya kutsa cikin shagon. Hannu yake nuna wa mai shagon kan wani film,shagon a cike yake,mai shagon ya dakko yaruba film,kai ya girgiza mai, dai dai Laila ta gama zaben wanda zata dauka tasa a jaka ta dago,drama ta tsaya kallo,tsaf,ita ta gane abinda saurayin yake nufi,sai tai burus. Mai shago ya kara dakko American film,, dan takaici bai san ya kai hannu goshin shi ba ya dafe,tare da fadin"Ya Allah! Dagowa yayi,tare da girgiza wa mai shagon kai,sai ya mayar, tare da nuna mishi saitin wanda yake so, zai dakko na saman shi da sauri yace(" no,dat one)ya nuna mishi,tuni mai shago ya fara bambami,kira yake toh ya shigo ya dauka,sai dai shi bai ma san mey yake fada ba. Dariyar da Laila ta fara ne ya dawo da hankalin mutumin kanta,,"MashaAllah, shine kalmar da ya furta,tuni yasau baki yana kallon ta,budurwa ce bata fi (15 to 16years)ba,da ganin ta ka ga fara bafulatana,sai dai zaman garin wasu ya sauya ta da dabi'un ta,fara ce,mai dan dogon hanci da zara-zaran idon ta, wanda da ganin su kaga na shakiyanci,bakin ta dan karami chul dashi,gashin idon ta da girar ta kadai zai tabbatar maka da gashin kanta,dan ganan sumar shi har kusan kumatun ta, fararan idon ta da hakorin mai dauke da siririyar da beauty point dinta sunfi komai daukar hankali,,doguwa ce,amma ba chan ba, ,mai dan kaurin jiki,dan ba siririya bace,,a haka ma Laila mai kyau ce,bare zuwa gaba kan nan mai sassake budurci ya sassake ta. Sanye take da riga da skirt na English wears,wanda ta mayar su tamkar sasu ibada,tun tashin ta,bata da kaya sai English wears,dai dai da zani,har yau bata iya daura wa ba,sai a Nigeria take sanya skirt na les ko attamfa. Duk da yana yin kasar, zai wahala kaga iyalan gidan su Laila jiki a waje,ko yawo ba dankwali,,da dai gani,sun rike addini,duk da Laila ta watsar da Al'ada. "Kai ba ma gajiya wa da dariya a garin nan... Rai ta hade ganin yadda ya sau mata na mujiya,,hannu ta tafa a kusa da fuskar shi, jin tana Hausa da turanci yasa ya kasa dauke kanshi,hannu ya mika mata,,da sauri ta ja baya,,shi duk mamaki yake,yau watan su d'aya a garin nan,fitowar shi uku,bai taba cin karo da Bahaushe ko wanda yake jin turanci ba sai yanzu agun Laila. " Dan Allah danyi Hausa na kara ji kadan please,,harara ta sakar mishi,kan tace"mey zakaci da hausa ta? Murmushi yai,kamin ya gode Allah,(at least) dai yaji dadi ya samu dan uwa a garin. "No ba kom,pls kice ya mikon wanchan hausa film din,,kallon shi tai,kan ta k'ank'ance ido tare da rike kugu" a nawa? Hannu yasa a aljihu,kan ya ciro kudi ya mika mata, murmushi tai,kan tace "wasa nake,,kan ta juya kan mai kaset tana mishi wani yare,wanda shi ya zata ma yarbanci ne. Tuni suka dinke kan su rabu,har kusan gida ya rako ta suna tadi,Allah ya hada maganannu biyu. Washegari ta dawo a makarantar cikin unguwar mai kamar islamiya taga mutum a tsaye a kofar gida,da sauri ta karaso,,yana ganin ta ya hau washe baki. Kalle kalle ta kalle shi, " ya dai? Murmushi yai kan ya kada kai yai shiru,kugu ta kama,"nace ya akayi? Hannu yakai bakin shi ya zuge,ma'ana bazai magana ba,,kai ta kada,kan tai hanyar shiga gida,da sauri yasha gaban ta,"bakiyi sallama bane,,kinsan kuma hukunci. Fuska ta saka,kan tace''auf,sorry...sai ta dan koma baya,kan ta mai sallama, yai murmushi, "yauwa,ko ke fa,kan ya amsa,ska gaisa,"ina Yunus? Hannu ta daga mishi," ina zuwa,gidan ta dan leka,kan ta dawo,"nikam ka fadi abinda ya kawo ka kan a ganni a nan,,kai ya kada,kan yace"taimako zaki min irin na jiya,na fito siyayya ne, en ban san mey zan ce ba,(please help me)..Kallon shi take ba ko kiftawa. By Feenat Ja'afar
[12/17/2017, 1:54 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 16_Kan ta jin jina kai,kamar mai yin rada tace ya jira ta, gida ta shiga,kusan minti goma sai gata,hara ta mishi,kan tace"ka sa na zulawa mamy karya. Kunne ya kama,kan suka tafi,tace"wai kai a unguwar nan kake ne?? Kai ya kada mata,tambayar ta yake sunan ta, ta kalle shi,kan ta kalli titi,"interpreter"... Murmushi yai lokacin da suka shiga shagon. Ya kallo ta,"tun dazu nazo shopping, na rasa mey sunan kayan siyan, naji kamar French yake,,kai ta kada,kan ta tambaye shi mai zai siya? Yace "madara, sugar,da dan sauran abubuwa.. Pls help..murmushi tai ganin yadda yake kwantar da kai,tace"ok, Juyawa yai kan mey shagon,da sai murmushi yake mishi,ya juyo gunta,yana mata halamar ta fada man,matsowa tai kusa dashi,kamar mai rada tace" madara""Lait", murmushi yai kan ya juya ya fadawa mai shagon,,kara juyo wa yai gunta,da rada ta kara ce mishi"sugar "sucre"..bakinta yake kallo,yadda take pronouncing abin,a haka har ya gama siyayyar shi suka fito. A mota ya zuba,kan ya juyo da murmushin shi,"(thanks much missaa...ya nuno ta hannu,da murmushi tace"interprète"... murmushin yai,kan yace" please..har da dan dukawa,,tai murmushi,kan a hankali tace"LAILA".. Ido ya rintse,tare da budewa ya furta sunan,, "uhmm,Laila,(nice name)..kai ta kada mishi,kan tace"(I know),da sauri ya kallo ta, dan bai tunanin taji ba,sai yai dariya,ta kalle shi tana duba agogon hannun ta,da murmushi tace "zan wuce,mister?... Shima yana murmushi yace "MAJ'NU"... murmushi tai, tare da kada mishi kai,halamun bata yadda ba,,sai yai murmushi," Mas'ood ". Kai ta kada,kan tace "(nice name)..Shima a wasan ce yace" I know.. sai abin ya basu dariya. Kamar jiya yau ma ya rako ta har hanyar gida yana mata godiya. Tun daga sannan ta zama mai masa fassara, bini bini sai ya dai dai ci ta dawo a islamiya zai zo. Yau kwana biyu bai zo ba,duk sai taji tana kewar shi,in ta zauna sai tunanin shi, takan yawaita murmushi in ta tuno da nashi murmushin. Har mamy ta gano ta,da yamma suna zaune tana wanke ma mamyn shuwaka sai murmushi take jefi jefi,duk Mamyn na kula da ita,,gashi ta sau famfo sai zuba yake acikin sink din,amma ina,ita hankalin ta ya tafi ga Maj'nu. Karasowa Mamyn tai ta rufe fanfon,kan taja ta harde hannun ta a kirji tana kallon gudun ruwan Lailan,,,chan taga sai ta salamce mata ganye da dirza,sai ta sa hannu ta dauke natan,,da sauri ta kalli Mamyn,hararar ta tai,kan da fillanci tace ta bata wuri. Kitchen din ta bari,tana tunanin lafiyar kanta kuwa? Yunus ne ya shigo gidan da dan gudun shi,lokacin suna zaune tai filo da cinyar mamyn tana mata Oiling,"Aunty Laila,,yana haki yake nuna mata kofa,"uncle"..a zabure ta daga kanta a cinyar Mamyn,sai kuma tai kasa da kai gabanta na faduwa. Janta Yunus din ya fara,,sai tai burus tana dan satar kallon mamy.. Ita dai mamy kallon ta kawai take, sai ta rufe manta ta tashi wanke hannu. Tashi itama tai tana dan leken waje daga inda take. Sallamar Abban su suka ji,kiran Mamyn ya fara,sai gata ta fito a kitchen, tai mishi sannu da zuwa. Yace yana tare da bako,wai wajen Laila yazo, da sauri Laila tai d'aki gaban ta na faduwa,,"na shige su,ya mutumin nan zai mata haka? Tashi tai tana leken window, ganin Abba tai ya koma ya shigo da Mas'ood din gidan,koma har parlour.. Gaban ta ya cigaba da faduwa,,in Abba taji tana wa mamy nan raki tasan sai buzun ta. By Feenat Ja'afar
[12/17/2017, 1:55 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 17_Sallamar Abba ne ya katse ta,da sauri tai kalar tausayi tare da tsugunawa kasa. A bakin gadon ya zauna yana kallon yana yin ta,sunan ta ya kira,kan ya nuna mata kusa dashi,,"Laila ga bako yace kin mishi taimako sosai,yazo gida yin godiya, sai dai ina kika samo dan Kano? Kai ta kara kaiwa kasa. Hannun ta Abban ya rike,kan ya kira ta ta kalle shi,,"Yace auran ki yazo nema....da sauri ta dago kai tana kallon Abban,Murmushi yai,kan ya kada kai,,"kin san bazan miki dole ba Laila,amma at least ki bari kiyi ko degree ne kamar yadda kika ce karatu zakiyi..kai ta kara yin kasa dashi,dan bata da amsar Abban a yanzu,,ganin haka ya tashi,"yanzu kije kiji da mai yazo,sai dai ki kiyaye,dan ba kowa zakina yarda har irin haka ta biyo baya ba. Kai ta daga. Zai fita sai ga mamy,duk ranta a jagule,a bakin gadon ta zauna,"ina rokon ki Laila da ki tsare mutuncin ki,kin kai shekarun da bai kamata kina hulda da wani namiji ba sai Baban ki,,wai har rakiya kike mishi ni ban sani ba...kasa ta sakko,"dan Allah mamy kiyi hakuri,wlh bazan kara mishi ba. Kai ta kada..."yanzu ki kintsa kije kiji abinda zai ce,ki sanar mishi kuma da muradin ki. Kai ta kada tana murmushi, bata san abun zai zo da sauki ba. Powder ta shafa ta cire kananan kayan tasa doguwar farar riga da mayafin ta. Ta fito mamy na kallon ta, tray ta miko mata na kayan sanyi,kai kasa ta karba tana murmushi. Da sallama ta shiga,shida Yunus ne, Kai ya dago yana mata wannan kallon nashi,da sauri ta dukar da kai kasa tana murmushi, a tsakiyar Center table din ta ajiye,tare da tsiyaya mishi ta zauna. A hankali ta dago suka hada ido,da sauri ta dauke tana murmushi,, "ina wuni?.. Murmushi yake kawai yana kallon ta, mamakin da yake yadda yaji kwana biyu da bai ganta ba. Jin bai amsa ba yasa ta kara kallon shi,kallon ta kawai yake,sai taga ya kara mata kyau,kullum da kananan kaya take ganin shi,yau kuma shadda ce,sai ta samu kanta da kare mishi kallo,ba laifi akwai fara'a, ga shi handsome dashi,duk da ba fari bane,amma ba baki bane,yana da hanci kamar shi ya daurawa kanshi,da dan sumar kanshi mai kyau,yafi mata kala da yan sudanist din nan. Fara'ar shi tafi komai tafiya da ita..ba laifi yana da kyau dai dai misali,gashi da kamar zai yi karama a fuska. Kai ta kai kasa,kan ta kara mishi ina wunin, yace" ai nai fushi ni,da sauri ta dago,,gira ya daga mata, "2days kin jini shiru bakya ko cikiya...kai ta langwabe mishi kamar yadda ta saba,,sai ya ga ta koma mishi yar baby,,," kinji sakon Maj'nun ki ko Laila??.. Kai ta sunne kasa tana wasa da gyalen ta,,taso wa yai ya dawo kujerar kusa da ita,murya kasa-kasa yake aika mata sakon zuciyar shi,ina,duk kunya ta cika ta,dan karo na farko da wani ya taba furta mata so a rayuwa. Duk da samari da dama yan garin na kawo mata hari,sai dai fatattakar su take,dan karatu ne burin ta ba aure ba...Sai dai a abinda bai fi sati ba har Mas'ood ya sauya mata tunani. Sai dai data tuno da mamy sai ta fada mishi cikin ta,yanzu kam shima ba aure zai ba,dan karatu yake,dama yazo a sanshi a gida ne kan ya tafi karatun shi U.K.. Tun daga ranar Laila da Maj'nu suka dinke,kusan kullum yana gidan su mamy,wayeyye ne shi, dan baya surikar dasu mamy,sai dai tun daga ranar bai kara zaman zance da ita ba, sai dai su zauna a tsakar gida tana koya mishi abubuwan da bai san sunan su ba. In suna tare kace kanwa da yaya ne,dan duk dun su abin dariya gare su,musamman a wajen karatu,in bai fadi abu dai dai ba har da bulalar barazanar Laila... Mamy takan kasa kazawa da shirmen su,dan biye mata yake ba ruwan shi. Har Hajiyan shi kawo gidan,kan wani lokaci zumunci ya kullu tsakanin yan kasar d'aya. NIGERIA: Tunda aka wayi gari yau Naina ta kasa zaune,ta kasa tsaye,ita dai baza tace ga irin murnar da take ba,sai dai wani abu,in ta tuno da yayan sai taji gaban ta na tsananta bugawa,,fara'a yau tamkar an biya mata makka. Hajiyan sai murmushi take,takanyi mamakin shakuwar Naina da Faruq,ko shi bai son yazo gida ba Nainan shi..Sun shaku matuka. Karfe uku ta shiga wanka,a gaban mirror kuwa,yadda kasan wacce zatai bako,haka tai ta kyali,tun jiya har kitso tai,duk da bata son kitso. Karfe biyar ta fito daga d'aki,sai kumbura take yayan ta yaki zuwa,,hajiya sai dariya take mata..Littafin Hausa take karantawa ko zata rage zafi.. Tana yi tana hararar kofa. A kofar parlourn ya tsaya da jakar shi yana kallon ta yadda take abun,Naina ta sake cika mishi ido,,ilahirin kyaunta duk ya fito,ajiyar zuciya ya sauke,ya rasa mey yasa yafi daukin ganin Naina sama da kowa,duk da ya zata karan nan ma bazai same ta ba. Dago wa tai haushi na kara cin ta,ta sau wa kofar harara a hankali tana fadin ko ya zo ba zata kula shi ba,kai ta duk'ar, sai dai da sauri ta saki fuska kan ta dago tare da mike wa.. "Yaya Faruq..gira ya daga mata, da gudun ta tai wajen shi da zummar rukunkume shi,sai dai kan ta karasa ta tsaya,murmushi take ta zabga mishi,ba daban Hajiya tace mata Yayan ta ma yana cikin mazan da zata daina mu'amula ba da tuni ta rungume shi... Maimakon hakan,sai taji wani irin kunyar shi na shigar ta..a hankali ta karasa tare da mika hannu,jakar shi ya bata yana kallon ta da murmushi,lalle Naina ta nutsu,sai dai shagwabar yasan tana nan..." Sannu da zuwa yaya,,kai ya kada mata "yauwa Naina,,waje ta bashi ya shigo,,tuni kuma ta fara kwallawa Hajiya kira,jakar ta ajiye tai sama tana kiran Hajiyan..kai ya girgiza yana mata murmushi, ya gano murnar ganin shi take sosai. Kusan shida Hajiya tace ta kira shi yaci abinci,,kamar jira take kwa ta mike,kai hajiyan ta kada,Naina da Faruq sai Allah. By Feenat Ja'afar
[12/17/2017, 1:55 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 18_Da dare Hajiya tai saman wajen Abba,Naina tana parlour ya shigo,,kai ta dukar tana mishi sannu da zuwa. Yace "ke kadai ne? Kai ta daga,,zama yai yana kallon ta, duk ta sauya mishi,tunda ya zo yake kula da yadda take duk'ar da kai kasa,," hala ta fara kunyar shi ne ko mai? "Naina'' kai ta dago ta kalle shi, jin sautin kiran har ranta yasa ta kasa amsawa. " ss2 zaku shiga ko? Kai ta kara daga mishi,murmushi yai kan ya dawo gaban ta ya zauna."Naina saurayi fa,kina dashi? Kai ta dukar tana murmushi,, tuni gaban shi ya fara bugawa.. Tun dazu da taje kiran shi ta tarar yana shafa hoton ta na tun tana Yarinya yana murmushi... Yace"kin tuna ranar da aka dauke ki? Zama tai tare da karbar hoton tana kallo,tabbas ta tuna,lokacin akan coack take rigima ita da dan gidan ya ibrahim ran sunan Aunty Salma,shi kuma faruq yaje ya siyo mata,a lokacin mai hoto yazo daukar su hajiya daga gidan mai jego,tana wa Aliyu gwalo aka dauke ta.. Murmushi tai ta kada mishi kai..kai ko ita tasan ta zuba tabara a gidan nan son rai...labarin yarintar ta yake bata tana dariya,wani ta tura baki,ita bata san tayi ba,,kallon ta ya tsaya,komai Naina tai burge shi take,labarin zuwan su kwatano take da yadda ta bata achan,wai har matse ido take tana nuna mishi irin kukan hajiya...kallon ta kawai yake ba ya ma gane mey take fada..ya rasa tun tashin Naina mey ke yawo a kwakwalwar shi in suna tare. Irin kallon da yake mata ne yasa ta tsagaita labarin itama ta hau kallon shi.. Hajiya ce ta katse su. Yai murmushi lokacin da ya dawo daga tunanin dazun,dago wa yai,suna hada ido ta dukar da idon ta,mai maita tambayar yayi yana jira yaji amsar ta, kai ta girgiza mishi,halamar babu..yai murmushi, "toh ni fa?ai ni saurayin ki ne koh? Da sauri ta rufe fuska da hannu tana murmushi,, yai murmushi kan ya koma kujerar da ke facing din ta ya zauna..tana ganin haka ta tashi da sauri tai dakin ta..a gado ta fada tana murmushi, a karance karancen ta tasan mey ne ne so? Ta kuma san tabbas ta fada son yayan ta.. Filo ta ja ta damke,,rayuwar da take tunawa,parlourn da bata koma ba kenan. Washegari tana kitchen ita da hajiya suna breakfast ya shigo,daga training yake,sai haki yake zuba wa,ruwa yazo dauka a kitchen din,dai dai Nainan zata kai abinci parlour,,saura kadan ta barar yai saurin tare wa,bata kula dashi ba kawai ta ganshi a gaban ta,,kallon ta yake da wani yana yi, kai ta duk'ar tana mishi ina kwana,yace bai amsawa,jiya shine ta gudu,kanta yake kallo,gashin nan yasha kitso,,Hajiya ce ta juyo tana kallon su,,ganin irin kallon da Faruq din kewa Nainan yasa ta katse su,"bari kika min koh Naina? Da sauri ta kada kai ta raba ta wuce,binta yai da kallo yana murmushi, kai Hajiyan ta kada,yanzu ta gano inda suka dosa..kitchen din ya shigo lokacin daya girgiza kai yana murmushi, ganin Hajiya na kallon shi yasa ya hau kame kame,yi tai kamar bata san yanai ba ta cigaba da aikin ta. Dazai fita ma haka sukai,lokacin Naiman ta dawo..ganin Hajiya yasa ya bar kitchen din,Nainan ta kalla,murmushi take fuskar ta a kasa,lalle sunyi nisa... "Wai mey yasa bakya son dankwali Naina? Da sauri ta shafa kan,kan ta tuno ta kunce damarar da taci da dankalin. A wajen cin abinci ma Hajiyan na kula dasu,a kwano d'aya suke ci suna murmushi, ta kada kai, sabon da ta musu kenan,amma lokaci yayi da za'a daina, dan ta lura kar kuma a fara kauce hanya...don Faruq ba muharramin Naina bane. Ran talata aka tattara da kuka zata tafi,sanye take cikin uniform dinta riga da wando na check orange, rigar har gwiwa,da tsagu gefe da gefe kusan cinya,sai dan hijab din ta da ko kirji bai rufe ba,takaicin Faruq kenan,sai dai ita da halama ta saba dashi a haka..uniform din sun bala'in amsar ta,kugun nan an fito da shape,Hajiya takan ce tsiyar ta da Federal schl kenan... Da drivern Abba da yayan aka tafi kaita,sai goge hawaye take da handkee, ta tsani rabuwa da Hajiya,sai dai karan nan da biyu. Yakan dan kalleta ta mudubi,dan shi ke driven,ya kan jin jina bacin Naina.. Har akaje makaranta yana duban ta,bacci ya sache ta. Jin tsayuwar motar ne ya tada ta,ido ta bude tare da kallon window, tsirarin yan school din su ta ga,halamun an tashi daga evening pref zasu wajen game. Murmushi tai kuma,duk tsiya tai missing friends...Kallon ta yake,ganin tana murmushi, sai ta juyo kallon shi,murmushi tai lokacin da ya daga mata girar shi kan ya fita,tana kokarin budewa ya bude mata. Dake Abba yai report,kuma 2days ne,basu sha wahala ba,sai dai lokacin da zai tafi kuka ya dawo sabo,da alkawarin zai zo mata visiting wani month din tai shiru,,haka suka rabu da kewar juna..duk da bai sanar ta yana son ta ba,ita tai na'am da ta fada tarko. A K'watano,zumunci sosai suke da gidan biyu,Momyn Mas'ood dasu mamy,kowa yana muradin ganin nashi a kusa,ko da kuwa dan garin ku ne. Laila ce ta rako Momyn Mas'ood ita da Yunus,suna tafe tana mata fira,tamkar ba mai shirin zama sirikar ta ba,sosai suka saba,dan takanas za tazo gidan ko ta aiko Laila tazo tayata zama. Asalin su yan Kano ne,baban su Mas'ood din dan kasuwa ne sosai,sannan yana aikin gwamnati,yakan k'etara kasashe musamman na kusa damu dan exchanging kaya,yana da mata d'aya da yara uku, Mas'ood shine dan fari, sai k'annen shi biyu duk maza,sai duk yafisu sosai, dan daga dan 13 sai 10,daga nan haihuwar ta tsaya..a Kano duk suka tashi, Mas'ood Allah ya bashi son karatu mai zurfi,hakan yasa baban shi tsayawa tsayin daka har iyanzu da yayi retire suka dawo nan. Sai dai duk da haka bai fiya zama ba,yau yana chadi,gobe chemero,jibi Ghana,saukin yawo ne yasa ya dawo zaman nan zuwa wani lokaci. Da sallama suka shiga,zunnu suna parlour suna kallon ball,sai ihu suke..kai momyn ta kada kan tai wajen tvn ta kashe,"tunda bakwa jin sallama,nakan rasa mey ake kwasa a ball,, sannu da zuwa suka mata kan suka hau bata hakuri akan za'a wuce su,Laila ta kalli Momyn,"Momy please... Murmushi tai kan ta kada kai,da sauri ta kunna musu,zama tai itama suna kallon tare,na ihu ta taya su,na tsaki tayi, murmushi momyn ke yi tai daki ta barsu nan,Laila na burge ta,kanta a waye yake. Ana haka gogan ya shigo,ganin sahibar tashi a parlourn yasa ya hau yage baki,kai ta dago lokacin da aka ci kwallo tana taya su zunnu fadin ''a gooooo..murmushi yai mata,sai kuma abin ya bata dariya,dan fa ta tsani ball,,tashi tai tana tambayar shi daga ina? A gajiye ya zauna,"daga neman viza nake,,rai ta bata tare da rike kugu,"oh I see,,visa koh? Da sauri ya girgiza kai,"kiyi hakuri na manta ne,,ina son na tafi dis coming month,,ta kada kai,"amma sai yanzu nake sani?toh ba tafiya... kai ya kada ganin yadda ta tsatssare shi tana jijjiga,su zunnu sai dariya suke,,tashi yai hannu yasa a baki kan ya nuno ta"waye mijin toh? Da sauri tai yadda yayi"wace matar?wace malamar??lokacin Momy ta fito,kai ta kada,wannan zasu kar mutum da dariya,, zama yai yana kallon ta,"toh malama ta,zauna a sasan ta,,kafada ta make halamar taki, momyn ta kalla,,sai kuma tai murmushi,dan bataji fitowar ta ba. Kitchen momyn tai,sai ta tashi tabi bayan ta ganin ya taso...abinci ta taya mamy ta daura,tamkar k'awar mamy haka ta dauki momyn,,labarin Kano momyn take bata tana murmushi, tace mata mey zata karanta? Murmushi tai kan tace"Nurse take son zama..momyn tai murmushi,"toh Allah taimaka, kice za kuyi anko,ga Nurse ga Doctor.. Kasa tai da kai da kunya..har ga Allah manta mamy surukar ta ce take,ganin shima soyayyar a kusan wasa take tafiya..shi kuma Mas'ood biye mata kawai yake,dan birge shi Laila take in tana mishi shakiyanci. Sakare yai a kofar kitchen, ba abinda yake son gani sama da ya yaga Laila na yar kunyar nan...ta juya zata miko wa Momy flaks taga yai sakare yana kallon ta da murmushi.. Juyawa tai,taga Momy bata kallo,ruwan kwasar tuwan ta debo a hannun ta watsa mishi a fuska, da sauri ya lumshe ido tare da sauke ajiyar zuciya.. Gwalo ta mishi kan ta juya bawa momyn flaks din,kallon ta taga momyn nayi tana murmushi, sai ta wayan ce tare da juya wa. By Feenat Ja'afar
[12/17/2017, 1:56 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 19_Yau sunyi resuming a school, ya kama saura sati uku Mas'ood ya tafi. A gajiye ta dawo,dan day ta ke,,su mamy ta tarar a tsakar gida suna ta zulumi,,da sauri ta karaso,"mamy lafiya? Hannun momyn ta rike tana kallon ta,,murmushi ta kwakulo,,"Aiya,kin dawo? Kai ta daga mata,neman bayani kawai take,,"Mami mey ya faru? Kafadar ta ta dafa,"ki ci abinci, zan fada miki,,sai ta hada da yake,dan tasan Laila da rikici da tsoro. Dan ci kadan sai zulumi take,,ta watso ruwa tasa riga da skirt kan tai parlourn Mamyn jin abun. "Ba fa wani abu bane fa,duk kin daga hankalin ki,,dama Mas'ood ne..da sauri ta waro ido,,"mamy mey ya same shi? Hannun ta ta kama,"ke ciwan ciki ne,yanzu zunnu yazo kiran Abban ku wai Abban su baya gari,,, tuni Laila hawaye ya wanke fuskar, hannu take yarfe wa,wayyo Maj'nun ta...mamy tace"mey toh na kuka? Nace miki da sauki ai,,kwanciya tai a cinyar mamyn, sai dai bata daina hawaye ba,tafa tuno ciwan cikin nashi, kwanaki shi ya kwantar shi kwana biyu bai zo ba... Dakyar mamy tasa tai shiru,tare da ce mata da yamma sa je dubo shi. Da yamma suka je asibitin da aka kwantar da Mas'ood, su Momy suka tarar a tsaye dai,idon ta duk ya kada,,tuni Laila ta kara rikice wa,"Momy ina yake? Hawaye ta fara,momyn ta ruko hannun ta,"Laila da sauki,,yana bacci ne,,bar kuka kinji? Dama yana haka wani lokaci,, amma kan anjima zai ware..mamy tace"Allah sa. Har dare Laila tana nan,kan Abba ya dauke su suka tafi,Momy sai godiya take musu,dan Abba yai jigilar komai dan ba inda ta sani. Washegari dakyar taje makaranta,dukkan wanda ya ganta sai ya tambayi mey ya samu Laila? Dan sun san Laila mai kichaniya ce, duk da su biyu ne kawai musulmai a ajin,amma tana k'yak'yawar mu'amula da kowa..duk malamin da ya shiga aji kuwa,toh baya shakkar bama Laila Questions,,asali ma burge su take, ganin yadda ba yar kasar bace, amma tana da matukar kokari,,sannan tana da riko da addini,dan akan yafa dan karamin half sannan ta sun sha fama,ita kam tace da tadaina sawa, gwara tabar makarantar. Ganin yadda sukan karu da ita,kodan wajen Quize da Competition tana musu kokari,hakan yasa suka bar ta. Kasa zuwa gida tai,don jiya har ta bar asibitin Mas'ood bai farka ba,,taxi ta tara tai asibitin, tunda tai hanyar word din sai kallon ta suke,riga da skirt ne uniform din,skirt din blue iya gwiwa,sai rigar shi fara mai gajeran hannu da na top irin na b'ulu shima blue,an rubuta sunan makarantar a baya da farin zare,socks ne ya taho har kasan cinyar ta,su suka rufawa kafafun ta asiri da suke a wajen dingilelen skirt din,sai hijab dinta iya kafada dan tozon parking din gashin ta ya fito,a kafada ta rataye schl bag din ta,duk sukuku take tafiya har tazo dakin. A hankali ta tura dakin da sallama, yana zaune an jingina mishi filo da daurin ruwa a hannun shi,mamy na zaune kusa dashi tana juya mishi tea,,dagowa yayi jin sallamar ta,,sai wani rarrabewa take idon ta akan shi,,Momy tace"Laila shigo man,,tashi zunnu yai ya ba ta kujerar,a dan dosane ta zauna tana murza hannun jakar ta.."Momy ina yini? Murmushi momyn tai kan ta amsa,"ya mai jiki? Ta kalli Mas'ood din da yake mata murmushi.. Momy tace"tunda kinzo ke malamar shi,kila yasha ko ruwan tea din,,ta karasa tana murmushi, a tausaye ta sake kallon shi, duk yai mata wani iri daga jiya kawai. Zunnu ne ya katse ta,"mom,ai nasan Laila zatai ma yaya dure yanzu,,dariya sukai,shikam murmushi kawai yayi,,dan kamar ya lura hawaye Lailan take. "Mu fita auta, kar muga fadan nan...da wayo ta jashi suka fita. Kamar jira take kuwa ta mike ta zauna a gun da Momy ta tashi kusa dashi,,duk ta marai rai ce mishi,,shikam kallon ta kawai yake yana murmushi..tai mishi kyau a uniform din. "Sannu",,kai ya daga mata,sai ga hawayen da take damkewa sun zubo,,kai ya girgiza mata,"(am ok)fa Laila,naji sauki,,kallon shi take,kamar mai son ganin saukin,, ta duba tea din ta dakko,, "Toh kasha in kaji sauki,,kai ya kada mata,dan gaba d'aya baya jin dadin bakin shi,,sai dai yasan in yaki yanzu zata hau bori,yasan ta tsaf. Baki ya kawo wai ta bashi,yar harara ta mishi,kan ta make kafada,,koma wa yai shima ya make kafadar,, tuni ta langwabe kai gefe tana tabe baki kamar yaro zai sau kuka.. Murmushi yai a hankali ya miko mata dayan hannun,,sai ta tashi ta matso ta bashi. Kujerar ta matso da ita kusa dashi,da ya dan kurba sai yaji kamar magani, ajiye wa yake kokarin yi yana kallon ta,baki ta zumburo tana bata rai..da ido da gira tamai halamar sai ya sha.. Murmushi yai kan ya sake kurba,haka sukai tayi har kan ya kula ya shanye. By Feenat Ja'afar.
[12/17/2017, 1:56 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 20_Kwanan shi 3 aka sallame shi,Abban su yazo, tambayar shi yake da jikin zai tafi? Shikam sai ya daga kai,dan hutun ya ishe shi. Alfarma ya nema wajen Abban,kan yaje gun Abba nema mishi auren Laila, da alkawarin achan zai barta tai makarantar ta..tsamm Abban yayi..kan yace yana zuwa,,cikin dakin mamy ya same su suna dariya,,Lailan na basu labari,kai ya girgiza yana murmushi,, yasan ranar tafiyar Laila gidan miji duk zasuyi kewar ta. Mamyn ya yafico,,a dakin Laila suke yana sanar ta yadda sukai da Abban su Mas'ood,, itama tsam tai,duk da nan da shekara 2 Laila ta girma sosai,18 take kenan,toh amma ya Laila zata iya zaman bautar gidan miji? Tasan ta iya girki,toh dabarun zaman gidan miji fa? In ba shagwaba da wannan gwallin zata nuna mishi ba,"amma tana son shi? Wata zuciyar ta katse ta,kai ta girgiza,,kan ta kallo Abban,"mey kuka yanke toh? Ya kamata muji ta bakin ta,,,kai ya daga mata,tukun yace ta kira Lailan... Da suka fada mata zancen auren kasake take kallon su baki sake,ta waro ido tana sama"Abba U.K za'a kaini nai karatu? Da sauri ta kada kai,"wallahi na yarda, U.K fa,ta kyalkyale da dariya,,kai Mamyn ta kada tana kallon Abban,kafada ya daga mata yana dariya,lalle sai yau suka yarda Laila danya ce sharaf.. Wato ita fitar ta karatu U.K shine murnar ta ma da yardar ta ba auren ba? Daga lokacin mamy ta yarda Laila bata san ma meye auren ba kila. Kuka take marar sauti,duk in kaganta kaga na baci ne,kamm ta rike jakar shi,murmushi kawai yake mata da ban hakuri,''Haba interpretè"nan da two year zan zo mu tafi duka ma fa,ko bakya so? Kai ta daga,"ina so, amma har 2 years zanyi ban ganka ba? Kai ya daga,"nima ba haka naso ba Laila,, but zan samu nai sequizing naga na zo duban Ku a 1 year.. Kai ta daga, Allah yaga tana bala'in son Mas'ood, bata muradin rabuwar su,,sai dai in ta tuno da ta gama fa zata chale U.K sai ta fara Allah Allah lokaci yayi. A haka sukai sallama ya wuce..sai kuma gani na biyu. Da gaske mama ta zauna koyawa Laila Dabarun zaman aure,duk da tana tsinta a gidan,sannan gwanar Indian film ce ita,irin soyayyar nan duk ta iya,,a makaranta kuma ta dan san wasu abu,duk da a haka baza kace tasan komai ba,dan wani abun in mamy na koya mata har dariya take,,don tuni ta kware tas a fagen. Project Faruq yake, ba kama hannun yaro,dan burin shi yai ya gama su dau hanya,dan yana d'aya daga yan sponsorship da aka dau nauyin su..burin shi in ya tafi,toh bazai dawo ba sai yai PhD,, dan sosai yake da muradin karantar ilimin zane. By Feenat Ja'afar
[12/17/2017, 1:57 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 21_Da sallah kuwa kamar yadda Abban ya alkarwanta suka tafi gida(Nigeria)sallah, Laila gidan Hajiya ta sauka wajen Naina K'awa. Saura 3 sallah, kowa ya hallara a family,na wani gari ma ya zo gida sallah, ciki harda Faruq,,Naina ce zaune ita da Laila kusa da Hajiya,,"Hajiya wa zai kai mu karbo dinkin Laila? Hajiyan ta kallo su,"kai kunyi kyau,,sai dai Laila ina kayan ta? Jikin ta Lailan ta kalla,"kai,Haji
ya ga kaya a jikina,, murmushi Hajiyan tai,"aa,kayan nan ai na zaman gida ne,,Naina ta kallo,"ki bata attamfa koda da skirt ne tasa da mayafi,,ita dai Naina dariya take, Laila tace"Hajiya,nikam achan a haka nake fita abuna,,wannan ai manya ne,,Hajiya tai murmushi, dan fa ita Naina bata sa kananan kaya, duk sai tai ta ganin Laila wani iri.. Fita Nainan tai zuwa dakko ma Laila wasu kayan,,a kofar ta hadu da Faruq yana kokarin shiga,kasa tai da kai da sauri tana murmushi, shima haka,har tai kasa d'aki tana waiwayen shi,,ajiyar zuciya yai kan ya kut'sa dakin Hajiyan. Zuba ya samu Laila na ma Hajiya,,sam ita batta bakunta,,labarin chan take bata kan ba ruwan wani da shigar ta in tai haka,,ita dai Hajiya dariya kawai take,ita kanta hausar Lailan dariya take bata,, kamar wata kaka haka suka dauke ta. Kallon Lailan yake,yarinyar akwai rawar kai a ganin shi,shi yasa Naina ke burge shi,duk da shagwabar ta akwai hankali da shiru shiru... Hajiya ce ya kalle shi tana murmushi,,"ka ganni da wannan K'anwar taka koh? Kallo shi Lailan tai,dan batama ji shigar shi ba tana ta zuba. Da hannu ta nuno shi,,"ya Faruq,right? Kai ya daga mata yana dan murmushi,, Hajiya tace"tun jiya baku hadu ba hala? Laila ce ta karbe,"hajiya,nifa rabon da na ga ya Faruq tun ina yar haka...tai kasa da hannu,,"sai dai in ji labarin shi a gun Naina..kallon shi take da murmushi,,shima da mamaki yake kallon ta,shi bai tunanin tana jin Hausa haka ba,,suna haka sai ga Naina,riga da skirt da mai zani ta dakko mata,,"Oya, zabi ki sauya muje kar dare yayi,,kayan Laila take kallo,,daga kan gadon ta rarrafo ta fara dagasu,,duk zuba mata ido sukai,,ta daga wannan ta daga wanchan, duk ta wargaza gugar,,Nainan ta kallo,,"Sis,zaba min,,kai Nainan ta kada tana murmushi, wani cotton les ta bata blue mai skirt,,kan ta mika mata,a jikin ta ta kara kayan,, da shakiyanci take daga musu gira tana,,"zan yi kyau yaya? Murmushi Faruq din yayi,kan ya kallo Naina,sai ya daga mata kai,,tace"tnks,,sai kuma ta kallo Hajiyan,,"ga nan yaya,ya kaimu karbo kayan,,Hajiya ta kallo shi,"yauwa,dan Allah ka sauke mun su kan ka wuce,, kai ya kada,,"amma suyi sauri,dan sauri nake,da sauri sukaje dakin su Laila ta sauya kayan,in ka gansu kamar wasu yan biyu. A mota Laila tana ta mata tadin tafiyar su U.K in Mas'ood ya dawo,,na dariya tai tana dan satar kallon Faruq,duk ta takura,dan duk kallo idon shi na kanta...yakan kada kai,mamakin surutun Lailan yake,ba coma ba full stop,,har tafi yar gidan sake wa,har ya sauke su a shagon karbar kaya. Ya kallo Nainan,"an baku kudin dinkin? Kai ta kada,,tuni yar gari Laila har ta fita..ya kada kai,na dawo wa gida ya basu. A shagon mai dinki style Laila ta tsaya gani,kan suka rankaya siyar sarka,kan asha ruwa suka dawo. Washegari suka je kitso da lalle. By Feenat Ja'afar.
[12/17/2017, 1:57 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 22_Yau take sallah, dan shiri rita ko sallar edi an bar su a gida,,anko sukai na attamfa purple da pink,da zani wrafa,Naina ta sakko ta bar Laila tana ta k'yali a dakin Hajiya,a goga nan a shafa chan,,abinci ta d'akko tana jerawa a parlourn, sai ga su Abba sun shigo suda su Abban Laila dasu Faruq da Manyan yayun shi,kowa da sallaya,,halamun daga masallaci suke,,Gaida su Naina tai,Abba yana"an gaishe ku da shiriri ta,ina yar uwar taki?? Sama ta nuna mishi,sai gata tana sakko wa,zani na harde ta rike da dankwali a hannu tana kwalawa Naina kira,dariya Naina ta fara,ganin yadda duk ta wani burkice tana kokarin faduwa daga stairs din,su Abba suka juya,ganin Lailan yasa su ma suka fara mata,,Hajiya ce ta fito jin tsiyar da ake ma Laila, ita kwa bin su take tana ta wage baki,,Naina ke gyara mata zanin,tai mata daurin baya,kan ta karbi dankwalin tana daura mata..Faruq kallon su kawai yake,kan aka zuba musu abinci sukai tsakar gida da darduma. Ana gamawa Faruq ya dakko cemeran shi ya fara daukar su hoto. Da dare suna d'aki suna kallon film din India,labarin Mas'ood take bata,,"ni wai ke baki saurayi ne hala? Murmushi Nainan tayi, kan ta girgiza kai,,tashi tai da ga rub da cikin, kan tace"tab,ni ai nan da 2 years ina U.K nida Maj'nu,, da mamaki Nainan ta kallo ta,,"toh zama Nurse din fa? Ko kin fasa? Murmushi tai,kan ta danna pause,,"a chan zan yi,, ya kema kince Nurse kike son zama ba? Murmushi Nainan tai,kan ta girgiza kai,"ya Faruq ke so,,ni nafi son na zama yar jarida,, amma tunda choice din shi ne,kuma kema naki ne,sai tai murmushi,"nima ya zama nawa. Murmushi Lailan tai mata. Anan Nigeria ta gama hutun ta,kan suka dau hanyar koma wa. Bangkok, nan ne kasar da zai tafi masters zuwa inda zai tsaya. Gobe yake shirin su tashi..Suna d'aki da Naina da Hajiya,duk sun tasa shi gaba abin tausayi,sai fadan rike addini take mishi,banda zama da yunwa...kallo Hajiyan yana murmushi,,Naina murmushi take musu kawai,kaya suke hada mishi,sai satar kallon juna suke da Nainan. Washegari tun asuba Naina ta tashi,tai rub da ciki,tunanin ta tafiyar yayan ta,gani take kamar in ya dawo zai iya fin karfin ta,tunda har yau ba wai ya furta mata so bane,hawaye taji yana zubo mata,ko dai ta mishi k'an k'anta ne? Duk tana karanta wa a littafin hausa a 15 ai ana cewa ana son ka...kofar d'akin aka bude,Faruq din ne ya shigo dakin,dan bugawa yai yana sallama, da sauri ta goge idon ta,murmushi ta k'akalo,kan ta kira sunan shi,d'akin ya shigo yana kallon fuskar ta,,gaishe dashi tayi kai kasa,"Naina mey ya faru? Kai tai kasa dashi tare da girgiza wa..sai yai tunanin ko tafiyar shi take wa,sai ya dan murmushi,"ba wai zan zauna ba sosai, sai kuma yai shiru,"kedai ko kingama makaranta ki maida hankali akan ta gaba,banda kula samari...sai ya sake shiru,,kallon shi kawai take,wato kar ta kula samari? Toh shi a wa? Haka akai sallamar duk ya kasa gano kanta. ~~~~~~~~~~~~~~~~ Kamar yadda komai aka sa mishi rana zai zo ne ina da rai. Yau ne dangin su Mas'ood na Kano suka zo sa ranar Laila a gidan kakanin ta duk a sakamakon dawowar Mas'ood,sun sa wata biyu mai zuwa. Gaba d'aya suka tattaro gida dan auran.. Zaune suke suna ta tsara yadda lamarin zai kasance, ta gumi Laila ta maka ta tafi tunani,sai zuba Naina take da sauran yan matan gidan da k'awayen Nainan biyu,,kai ta dungure mata tana hararar ta,,"ina kika tafi muna ta magana? Murmushi tai da ajiyar zuciya,"Soyayyar da zan shimfida ma Maj'nu kawai nake tuna wa 6s,,(u know?) Ban san irin son da nake Mas'ood ba Naina..ta riko hannun ta,"ji nake kamar na janyo sati tazo...baki suka rike,"Lalle baki da kunya! Maza kije inna Bilki ta ji ki zaki tsara... Murmushi tai,dan gani take baza su gane ba. Suna haka ya kira ta,ta tashi tana musu 10 minute,,Naina ta bita da kallo,tai murmushi, nan da wata shekara Yayan ta zai dawo. Tasan zai farin ciki,dan tana sa kamin nan ta gama BASIC din ta tasa uniform..Murmushi tai lokacin data hasko ta cikin uniform. Yau jama'a suka sheda auran Laila da Mas'ood,dan murna ji suke kamar su daga yau...barin Laila,kallon lallen ta take tana murmushi,"oh ni y'annan, anya Laila da kunya a idon nan? Inna Bilki ke mata,,"fada mata dai inna,,inji Naina dake shigo wa.. Harara tai mata,kan ta mata gwalo.. Washegari aka tattara ta aka kaita Kano,,sai kuma da akazo tafiya ta hau kuka,ita bazata ba,inna tace toh tazo su zauna. Kai da gwiwa ta hada,yau gata garin Kano,garin da bata taba takawa ba..garin da ba Mamyn ta..tabata taji anyi, a hankali ta dago tare da goge idon ta,,Naina ce,"yanzu Laila sai kanki yazo yana ciwo? Kiyi hakuri,kowa da haka yake sabawa,,na zata ma kinyi bacci.. Kanta ta daura a kafadar Nainan,,"wayyo mamy..sai ta fara kukan shagwaba,,dariya Nainan ta fara.."a karya kike Yarinya, gwara ma kice wayyo Mas'ood,, dariya ta fara itama,kan tace"toh wayyo Mas'ood. Washegari suka tattara zasu tafi,su inna Bilki sai fada suke mata,tuni kukan gaske ya dawo,dan gani take kamar sallamar karshe take musu,dan ba da jimawa ba zasu koma U.K.Momy ke ta bata baki kan tai shiru. Sai dare ya shigo,suna dakin momy,a kan mirror ya zauna yana ma momyn ya gida..Laila duk ba baki,,sai ta bala'in bashi tausayi..ya kalli Momy, sai ya kasa ma Laila magana,dan kunyar momy.. Zama yai yana dan kallon ta a sace,ji yake kamar yaje ya rarraso kayan shi,,a hankali ta dago tana kalle shi,sai ga wani hawayen. Momy na kula dashi tsaf,tashi tai ta basu waje. Kamar jira yake da sauri yai saurin hawo wa gadon tare da ruko hannun ta,,ajiyar zuciya yai,kan ya kalli idon ta, kamar mai jira kuwa ta kara fasa kuka..da sauri ya rungumo ta yana dan bubbuga bayan ta da rarrashi,,zuwa chan tai luf,komai ta tuna kuma,tuni ta fara kiciniyar kwace wa gaban ta na faduwa,, ta dan harare shi tare da matsawa. By Feenat Ja'afar
[12/17/2017, 1:57 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 23_ Murmushi yai tare da kada kai,matsowa yai tare da fara mata abinda yasan yanzun zata ware.."my interpretè,, my Laila,,,tuni kwa ta soma kunshe dariya,ganin yadda yake mammatso ido kamar mai shirin kuka..hanci ya lakuce mata,"yauwa my lovely Wife,,dariya ta fara,sai ya fara mata wakar ringtone din shi na "I love you baby muahh!muahh!!muahh!!!..tuni kwa tahau dirka dariya ya fara mantar ta gida..suna haka Momy ta shigo,ganin dariyar Lailan yasa tai murmushi,, tasan shi zai iya...gyaran murya tai,da sauri Laila tai baya tare da gyara gyale,tuni yahau sosa keya,, yadda yake mamyn ma ta fara tana yake,hanya ta nuna mishi,"Oya,Allah bamu Alkairi,, tashi yai yana kallon Lailan,,Momy ta bashi waje,,a ranshi yana amma Momy kin kwafsa,ya zata nan zai kwana yau d'aya. In banda juyi da dan tsaki ba abinda yake,har yai bacci. Washegari tana kitchen ya shigo,ta zata Momy ce ta dawo da taji taku, sai dai jin an ruko kugun ta yasa da sauri tasau service spoon din cikin source din da ta ke a tsorace,, "morning sweet Laila.. Da sauri ta juyo tana zame wa"kai,fita,fita Momy fa na nan,,wuyan ta ya fara sisina,,ya wani lumshe ido,,"oh Laila...ture shi tai kan tai saurin rage gas din,,ta ciro service spoon din tana nuna mishi hanya,"Oya,fita kan na dan dana maka, matsowa ya fara yana murmushi, sai ta fara ja da baya,"Allah fa zan sa ma,,ina,shi kamar zigashi take..ganin ya kusa cimma ta da sauri ta kalli kofa"Momy,da sauri yai baya zai juya tai sauri tura shi zata gudu ya ruko hannun ta..sai wani lumshe ido yake kamar mai jin bacci,,bai nufa ba yaji ta sau mai cizo a hannu, da sauri ya cikata tai waje tana dariya da mishi gwalo.. Kai kada,yana zaki shigo hannu. Dare nayi yaga yauma irin ta jiya momyn zata mishi kawai sai ya bisu dakin,lokacin tana adu'a da zata kwanta,,Momy ta kallo shi,"au,Udu,baka kwanta ba?gadon ya kalla, kan ya sosa kai yace"nifa Momy tsoron chan nake,,kai ta kada,Laila sai kunshe dariya take,tashi momyn tai,kan ta k'ank'ance ido,"toh jirani, ina zuwa..yana gani ta fita da sauri ya hawo gadon yana"amma bakida kirki intepretè,,da sauri ta duro kasa ganin yana kokarin jawo ta,,Momy yaji tana"toh fito,ganan zinnu zai taya ka kwana,,harar Laila ya fara ganin yadda take dariya harda kama ciki..kai ya kada mata..kan yai waje. By Feenat Ja'afar.
[12/17/2017, 1:58 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 24_Kwana 5 sukai bayan bikin suka tafi,dan tun kan tazo Kano ya kammala komai..Murna take yau sai United Kingdom. Suna dira yai musu shata a taxi sukai masaukin su,dan flat ne mai 1 bedroom, parlour, toilet da kitchen. Yace ta jira shi zai dawo yanzun. Dakin take kallo,duk ya baza kayan shi,su takardu,, a gado ta jabe,duk kanta juyawa yake,yau d'aya ta hau jirgi. Tana hutawa ta hau ramakon sallah,kan ta cire kaya ta ciro towel din ta tashiga wanka. Ta fito kenan taji sallamar shi,, gyalen ta jawo da sauri tana kokarin rufe bayanta,,kan ta zauna shafa mai. Da abinci ya shigo,yana bata hakurin ya dan jima. Da dare suna parlour ya tasa kanshi a cinyar ta sai kallon ta yake ya sabuwar halitta, ita kam kunya ma ya fara bata da wannan kallon nashi,,kan ta kwanto fuskar shi yana mata rada"shekarun ki nawa? Murmushi tai kan ta kalle shi,"(32)..yai murmushi," kg? Ta sake murmushi"(70).."height..ta dan doke hannun shi dake neman sawa a cikin ta kan ta ce"dai dai naka..kai ya dungure mata,"ai komai dama nawa kika fada...tai murmushi. Cilak ya dauke ta sukai d'aki suna dariya,, a gado ya dire ta,,"kin ma kanki bukulu yarinya, koh kazar amare bazaki ci ba..tai murmushi"au,amare suna da kaza? Ya kada kai,,"au baki sani ba? Kai ta kada mishi..yai murmushi,"amma ai kin san sallar amare ba? Da sauri ta kara girgiza kai,,,yai murmushin mugun ta,"mai alya fa? Murmushi tai kan tai kasa da kai,,yace"kima tashi,dan momy ta tara miki aiki,wai ni take ma k'walelen Laila,Laila na min dariya koh?? Gefe tai kai,tare da yin kalar tausayi,,"sorry"..kafada ya make,,da sauri ta fara "wayyo Momy"..yace"kwala da karfi, bata ji ba,,chakulkuli ya fara mata,,tuni ta fara dirka dariya. Sallah sukai,kan yai musu adu'a, tambaya yake mata cikin hikima da wasa tana bashi amsa,,duk da yasan Lailan shi ba baya ba..sai dai da wasan yai gaba ido sai ya rena fata..yau kam Maj'nu yasha rakin Lailan shi,,da d'ai d'ai da d'ai d'ai yan Nigeria da k'watano sai da aka kira su neman taimako..hmm sai dai sun mata nisa. Alo tsiya, Alo Danja, asibiti ko gidan yari,yau tamkar yar goye haka ta tashi,,duk inda aka taba a sau kara,,gashi taki bari yaje ko'ina,gashi an fara wuce shi a makaranta. Da kyar ta bari ya siyo musu kayan break fast,shima sai da ya hada ta da waya da yan k'watano ya zame ya bar ta. Laila da Maj'nu kam ko a tarihi akwai soyayya, in ka gansu gwanin sha'awa, domin soyayya suke cikin wasa da tsantsar tattali,makaranta kawai ke wuce shi. Ana haka admission din ta ya fito na QUEEN'S UNIVERSITY BELFAST (QUW)/SCH. OF NURSING AND MIDWIFERY,, BSc(Hons)/Diploma in Midwifery studies ta zaba na(18 months programme). Sosai idon ta ya raina fata randa ta fara shiga class,, sai dai da taimakon Maj'nu da kuma son karatun ta dan sake..yayin da gogan yake kan zama cikkakken likita..zaman garin ya dan mata dadi,shi kam dan gari ne,dan a kalla ya shekara 5 U.K. Yau duk suna gida ba makaranta,watan ta biyu da jona makaranta,,a gaba ta tasashi sai sun fita,shi kuma yace karatu zatai,,ita ta dage fita,sai bori take mishi,jaka ya zuge ya dakko popcorn yana dan hararar ta,,zama yai a kan gado yana facing din ta a kasan da take ya juye a bowel... littafin shi da yake project yake duba wa yana hulla popcorn din d'aya bayan d'aya,, yai burus da ita,dan ya fuskanci kwana biyu bata son duba littafin ta sai gantali,,yasan tana son popcorn,,lumshe ido ya fara,halamar dadi..tuni kwa ta hau hadiyar yawu,yana kula da ita,, wani ya kara diba a ya kai baki,da tsokana yace"uhmmmm,,dadi.. Ai da gudu tai wajen jakar ta dakko littafin ta ganin yana neman cinye wa,,gadon ta hawo tare da mika hannu zata deba,da sauri ya dauke tare da yin sama dashi,,kunne ta kama,sai ya sakko dashi tare da nuna mata littafi,yadda yake haka itama take hulla wa tana kuma duba littafi,ba wanda ke magana..kan ta farga ta samu abu dayawa a karatun. A fuska taji popcorn d'aya, da sauri ta kalle shi,tukun ta cigaba,wani ta kara ji,tana kallo ya boye hannu..a na uku gaba d'aya ita robar guntun popcorn din ta zuba mishi aka..tuni karatu yazo karshe,,suka hau tsere a dakin na sai ya rama. By Feenat Ja'afar. ®NGR WRITER'S ASSOCIATION (NWA)
[12/17/2017, 1:58 PM] Feenat Ja'afar: "K'ADDARA CE" © Feenat Ja'afar. 25_"Ki ci dai a hankali Naina,ke gaki da nawa, amma bazaki shirya da wuri ba sai kullum kinzo kina abu a gurguje.. A marai rai ce tace"toh Hajiya,, tea ta kur'ba kan ta tashi tana rataya jakar ta,da kallo Hajiyan ta bita,"wai har kin koshi? Kai ta kada,"nayi latti ne,ga yau zamu fara Hospital Final din mu..hannu ta daga tana tafiya,"sai na dawo,,kai ta kada Hajiyan, kan tace"a dawo lafiya,Allah bada sa'a,, ai ita tuni ta kai waje,,yadda bata samu matsala a baya ba ko dan yanzun a Final nata bata fatan samu,, da gudu kadan ta karasa motar, fadi take yai gudu dan Allah... Har an shiga kuwa,lecture za a fara...tuni suka fara mata tsiya, sarauniyar latti.. Ba ita ta dawo ba sai shida na yamma,, tun daga bakin parlour ta fara"washh Allah Hajiya ta,,ga zafin gari, ga yunwa,,karamin hijab dinta ta cire,dan kwalin ma,ido a rurrufe tai kitchen da dingisa K'afa tana cije lebe halamar gajiya,,fridge ta bude, kan ta dau ruwa,ta juya ta dau kofi ta tsiyaya,, da guntun na robar da kofi a baki ta fito tana sha, ta kara kadan zata kai baki taga mutum yai poster da chokali a hannu yana kallon ta,,a razane ta zubar da abun hannun ta ruwan kofin yai sama,sai akanta...ajiyar zuciya ta saki dan sanyin ruwan,, kallon shi take tana murje ido,,wato ya bar zuwa mata a mafarki ya dawo zahiri? Ashe da gaske ne mutum na maka gizo? Shidai murmushi kawai yake ba umm..ba um-um. Tsaye taga ya tashi daga kan dining din yana tahowa wajen ta, da sauri taja baya tare da kwalla wa Hajiya kira da karfi tana matsawa kitchen din.. Ido ta rintse,da fatan in ta bude taga ya bace,, a hankali ta bude ido d'aya, sai gashi gaban ta yana mata murmushi,, da sauri ta kara rintse tana karanto"Wat'taba'u a baiyane,,dariya ya fara lokacin da yaga Hajiya ta sakko da sauri,,"Naina lafiya,ido d'aya ta bude,yana nan sai dariya yake,da gudu tai wajen Hajiya tana"wayyo Allah na,,rukunkume ta tai tana nuna mata shi tare da cigaba da tofa adu'a,,itama Hajiyan dariya ta fara tana kokarin babbare ta,,"ke, yayan naki ne baki gane ba komai Naina? Da sauri ta kalli Hajiyan kan ta kalli Faruq din,murya na rawa tace"yau..yaushe yazo? Murmushi tai kan ta zaunar ta kujera,,"tsorata ta kai ne haka? kai ya kada yana murmushi,,ta kallo Naina da ke kallon shi,har yanzu jikin ta rawa yake. "A dole ta tsorata,ta ganka ba zata..murmushi yai kan ya tafi karasa abincin shi,,Hajiya ta kallo ta"toh ki nutsu haka,ba gamo kikai ba,kin ganshi nan nima haka na ganshi,ashe ya sanar da Abban ku mu yaki fada mana.. Sai da yamman nan naga mutum..kasa tai da kai tana murmushi, kan ta dan dago ta kalle shi,,duk ya sauya, ya sake zama dan gayun da yafi da,ya kara mata mugun kyau,da ka ganshi kaga dan bokon wata kasa,gashi da baida saje,amma yanzu yaje an mishi,ba dole ta tsorata ba..tuni kuma ta fara raina kanta,don sai taga yafi karfin ta yanzun,,sai yarr hawaye. "Toh fa,duk murnar zuwan yayan ne da kuka Naina? Da sauri ta goge tana k'ak'alo murmushin dole,kanta na kasa tace,"sannu da zuwa ya Faruq,,kai ya daga mata da murmushi,,tashi hajiyan tai tana"nasan ko abinci dak'yar in kinci? Tai wajen Faruq tana debar mata....dankwalin ta taja tana goge gashin ta da ya jike, sai ta dauki hijab din ta daura a kan ta,,wajen shi ta dan kalla a sache,sai suka hada ido,a hankali ta maida kai kasa..."taso maza kici kan a kira sallah.. Dagowa tai taga Hajiyan ta ajiye a akan table din,,sai ta kasa tashi,ganin kusa da Faruq ne. Sai da ta kara mai maita ta basu waje zuwa kitchen..kan ta tashi,a hankali kamar bata so take tafe..ta dan dosana kadan tare da janyo abincin,,duk sai kace bako ya zame mata. Chokali tasa tana dan juya abincin gaban nata,ya kalle ta,sai wani sanyi da ta kara yi,,"Naina...dumm, taji gaban ta ya fadi,, hatta muryar shi ta sauya a shekara uku..."haba Naina,ki saita K'wak'walwar ki man kar ya gano ki..wata zuciyar ta k'wabe ta. Murmushi ta k'ak'alo, kan ta amsa ba tare da ta kalle shi ba,,"Naina" ya sake kira,karan nan sai ta dago a hankali, da gira ya nuna mata abincin, halamar ta ci.. Kai ta kada mishi,kan ta fara diba kamar bata so,,"Naina"...ido ta rintse, kada ta zauce fa da muryar nan,hala sunan dadi yake mishi? Ido ta bude da zummar kallon shi,chokali ya debo da abinci ya kawo kusa da bakin ta,,sai tai murmushi,
ya tuno mata da. By Feenat Ja'afar.