Mafari

1.4K 97 13
                                    

*** GIMBIYA YALUSAH YAR SARKI MAI FADAR ZINARE***

Ismail I. El-kanawy

SAMARAQANDA  shine babban birnin daular IFRIQIYYAH wacce sarki rashid ke mulka a tsahon lokaci daya shude, kasace mai cike da arziki da yalwar kasar noma, kuma babbar cibiya ce ta kasuwanci wacce take like da kasashen larabawa irinsu Sham,Yemen, da kuma Baharain.

Mutanen birnin samaraqand suna matukar kaunar sarki rashid saboda adalci, rahama, da tausayin da yake lulluba musu a koyaushe. Da yawa daga cikin mutanen birnin tasowa sukai sukaga sarki rashid na mulkin samaranqada, babu wanda zai iya gaya maka ga ranar da aka dorashi akan karagar mulki, wani dai tsoho a birnin dan kimanin shekaru sittin da biyar yasha bada labarin cewa tun yana dan shekara bakwai yaji ana cewa sarki rashid shine sarkin samaraqanda.

  Wata rana sarki ya kwanta rashin lafiya mai tsanani wacce ba a taba gani yayi irinta ba, likitoci sukai ta kaiwa da komowa da magunguna iriri, tsibitsibi, amma ciwo sai cigaba yake kamar ma kara shi akeyi, malamai suka dukufa da addu'a a masallatai babu dare babu rana akan Allah ya bawa sarki lafiya amma abu sai gaba yakeyi, da dai sarki rashid yaga ciwo yaki ci yaki cinyewa sai kawai ya bada kai bori ya hau, ya tabbatar cewa lalle ajalinsa ya karato, sai ya fara tunanin wanda ya dace ya barwa wasiyyar da take kunshe a zyciyarsa a cikin manyan yan fadarsa kafin rai yayi halinsa, yasa aka kirawo masa wani kebantaccen wazirin sa wanda ya yarda da gaskiya da amanarsa ana cewa dashi waziri Yahya, ya kasance mai zurfi a ilimi na addini da adabi, kwararre ne a ilimin mandiki da kiďa, shahararre a wajen iya tsara zance da kudubah, amintacce a wajen sarki da jama'a.

   Cikin gaggawa waziri Yahya ya amsa kiran da sarki yake masa, sarki ya kalleshi da yamutsatssiyar fuskarsa wacce tsananin ciwo yasa ta tamushe kamar alayyahu. Yace: yakai waziri , kai kadai ne wanda na aminta dashi a cikin kaf jama'ar da suke fadata , saboda yadda kake min biyayya da kuma kiyaye surrukana, kaga dai yadda ciwo yaci karfina, yanzu babban abinda nake tunani kuma yake damuna bai wuce lamarin dana yarima Ma'amun ba, wanda har yanzu bai kai yadda nakeso ya kai ba.

Na jima ina neman haihuwa a tsahon rayuwata amma ban samu ba saida ajalina yazo dab da karewa, ina so ko bayan raina ka zame masa madubin dubawa wanda zai dinga kalla a duk yayin da abubuwa suka curkurkude masa, ka koya masa ilimin tafiyar da mulki da jama'a dan ya zamo shugaba adali wanda za a dinga buga misali dashi a duniya, ka ladabtar dashi da sashi a hanya kamar yadda uba ke ladabtar da dansa, in dai kayi min haka toh ka gama min komai a duniya, zan mutu ina mai cike da natsuwar zuciya da kwanciyar hankali.

  Waziri ya goge hawayen dake kwarara daga fuskarsa, sannan ya kada baki yace : Allah ya karawa adalin sarki lafiya nayi maka alkawari zan kula da yarima sama da yadda zan kula da dana, zan kasance a kusa dashi matsawar rayuwata, zan kuma cika maka burinka na son ganin ya zama adalin shugaba ga al'ummar sa, saboda haka ka kwantar da hankalin ka.

Sarki rashid yayi murmushi ya koma ya kwanta, waziri kuma ya tashi ya nufi kofar fita daga turakar, amma kafin yakai ga fita muryar sarki ta kuma riskar sa, "waziri" sarki ya fada, "Allah ya taimakeka" ya bashi amsa, "bayan na mutu; ka nunawa yarima duk dukiyoyi da kadarorin dana bari, ka kuma nuna masa sauran dakunan dake cikin gidan nan amma banda daki daya".

Waziri ya dago cikin mamaki ya Kalli sarki, "Allah ya kara ma lafiya wani daki ne wannan da baka so a nuna masa? Sarki ya muskuta kadan sannan yace: dakin da hoton GIMBIYA YALUSAH yake, dan nasan muddin yaga hoton to babu shi babu kwanciyar hankali harse yayi kokarin nemota, neman gimbiya yalusah kuwa kamar neman tauraruwa thurayya ne a cikin miliyoyin taurarin dake makale a sararin samaniya...

Ko wacece wagga GIMBIYA YALUSAH da ba a so a nunawa yarima Ma'amun hotonta??

GIMBIYA YALUSA ÝAR SARKI MAI FAADAR ZENAREWhere stories live. Discover now