SANADIN KIDNAPPING

11.2K 351 38
                                    

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*SANADIN KIDNAPPING*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*ZAHRA SURBAJO*

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*Kirkirarren labarine,banyishi dan wani ko wataba,dan haka akiyayi juyamin shi ta kowacce siga,duk wanda yayi na barshi da Allah*

*Gani Allah ya nufa nazo muku da wani sabon karatun,littafine daya kunshi abun tausayi,Yaudara,Nishadi,fadakarwa,uwa uba zazzafar soyayya,kubiyoni cikinshi kusha mamaki,dan da yardar ubangiji,babu kamarsa ajerin littattafaina,takowacce siga,comnents dinku shi ze bani kwarin guiwar yinshi akan lokaci,kubiyo yarnufawa domin jin wainar da zaa toya,#nice de dinnan Surbajo for life*

*1-2*

"Who is he?"ya tambaya cikin kakkausar muryar dake nuna tsananin tashin hankali da bacin ran da yake ciki. jiki na bari,wanda aka tambaya ya matsa kusa dashi ya duka yace. "Sir,He is a contract killer,he can do anything for Morney" "Oh God,how can we find him now"ya fadi yana yamutsa gashin kansa. "Sir the solution is,we have to be very smart first ,dan mutum ne shi me hatsari in aka nuna masa karfin mulki ze iya kashe Sanaya kuma ya gudu batare da anganshi ba" Se a lokacin matar dake zaune a gefe tana ta shirgan kuka,tace cikin kukan. "Alhaji,ni ba komai nakejiba,se Sanaya,nawane milyan dari,kayiwa girman Allah kabasu su sakomin yata,kana ganin Yadda hankalin Munaya yatashi sabida rashin yaruwarta" Shuru yayi yana kallonta,zuwacan yace. "Ba naki bada kudin bane,kawai inaso naji muryarta ne,to kuma sunki bata wayar tai mgn,amma tunda hakane zan basu,hajiya ki kwantar da hankalinki" Dubansa yakai gurin me tsaron lafiyarsa yace cikin kakkausar murya. "After given them the Ransom Morney,you guys i want you to find the person who was behind this kidnapping,if you find him chop him in to tiny pieces,so that no one can recognize him,this is an order"ya fadi cikin kakkausar murya.yana kaiwa nan ya fice Daga falon kamar kububuwa. Da sauri me tsaron lafiyar tashi ya bishi a baya. Ita kuma hajiya mikewa tayi ta nufi dakin Munaya domin ta rarrasheta ta samu taci abinci. *DAJIN KUDARU* Wani babban dajine me manyan dutsuna,da bishiyoyi,ga duhu,kwata kwata dajin beda kyan gani ko a ido ne,dajin na kan hanyar pambegua zuwa Saminaka. Wasu gungun matasa ne zaune cikin wani kogon dutse,sunkai su ashirin dukansu babu alamar imani atattare dasu,inka cire daya daga cikinsu wanda ke zaune can gefe rike da bindiga ya takure, Wata kyakkyawar budurwace zaune a tsakiyarsu sun daureta se kuka takeyi,ko suturar jikinta kawai ka kalla kasan yar manyan masu kudice. Wani bakin mutum ne mummuna rike da kwalbar giya ya nufeta yana tangadi,sharab ya zube agabanta yana dariya,Hannu yakai ya shafo fuskarta yace. "kaga wata jar fulawa,gaskiya ko babanki ya bada kudin bazan sakekiba,sena huta ajikinki"yayi maganar cikin muryar maye, Hannu yasa yana kokarin shafo boobs dinta,ayko a zafafe wannan matashin yataso ya iso gabanshi ya ture yarinyar daga kusa dashi yace cikin bacin rai. "haba oga ya zaka bata mana ayki,bafa daukota mukayi dan haka ba,kawai mun ɗaukotane dan kudi,to meyasa kakeso kaci mutuncinta?" Dariya ogan yayi sannan yace. "kaga shegen yaro,Wlh wannan fulawar se na mata ban ruwa koda so biyune kan ta bar gurinnan," Gabadaya sauran dariya suka kwashe da ita,shiko matashin shuru yayi yana binsu da ido,yayinda ita kuma yarinyar ta tsananta kukanta jin abun da ogan yace. "Wannan ba daidai bane,kuma wlh hakan bame yiwuwa bane,babu wanda ya isa cikinku ya taba mutuncin wannan yariyar matukar ina numfashi"cewar saurayin cikin kakkausar murya. Wani ne daga cikin sauran yataso da sauri yazo gurin saurayin yace. "Haba Safwan kasha kwayane,ka tunafa taimako ka nema agurina na kawoka gurin oga,dan kasamu kudin biyawa mahaifiyarka kudin operation din da zaa yimata,shine dan rainin wayo har oga na fadi kana fadi wlh kashiga hankalinka"yafadi yana me nunashi da yatsa. Cikin matsanancin fushi,yace. "Don't point your fingers at me or else i will cut them,ina danasanin haduwa dakai hafizu,kar ka kara fushina kasa na saukeshi akanka" Sanin halin safwan na bakar zuciyane yasa hafiz jan bakinshi yayi shuru. Sauran dayake abuge suke ba wanda yay mgn,guri safwan yasamu yana huci. Jan duwawu yarinyar ta dunga yi har tazo kusa da safwan din,Bayanshi taje ta lafe,tana hawaye. Waigowa yayi yana kallonta,sosai tabashi tausayi,hannu yasa yacire mata plasta din da suka rufe mata bakin.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 27, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

SANADIN KIDNAPPINGWhere stories live. Discover now