DUHUN DAJI
_(Labarin Sark'ak'k'iyar Soyayya)_
NA
ANEESA ABUBAKAR RIMI46
Sai a yau farhan yasamu damar shiga cikin gidan dan tafiya da matarsa maraicin ya isheshi...
Sallama yayi tareda kutsa kansa ciki ba tareda yaji wani ya amsashi ba..
Sake narkewa tayi cikin lallausan bargon dake gefenta alamun kamar mai bacci...
Starshine...starshine... bazaki ansani ba,ya fada a marairaice.
Dab motsawa tayi tace babyyy watz wrong nifa banajin dadi...ta zumbura baki.
Hmmmm!, dogon numfashi yaja tareda cewa ganinki nakeson yi idan zansamu inaso inyi mana gaisuwar rashin baffah,sannan....bai karasa ba hajiya Aminatu ta shigo tana kallonsa.
Ammie ina wuni...yafada yana shafa keyarsa.
Lafiya...farhan...kazo ne aje asibitin dakai rasa kunya.
A'a ammie kansa a sunkuye.. yafara tambayan kansa to waye ba lafiya kuma?
To ka tashi kaje ka kira farouk dashi zamuje kai kajira a gida.
To kawai yace ya mike ba tareda ya fahimci inda ta dosa ba.
Duk a wannan lokacin farhat batasan fatimah ta haihu ba,sunki fada mata dan kar a kuma samun wata matsala duk da cewa abun farin ciki ne.
Alh Ahmad da iyalansa sun koma gidansa tareda yanke shawarar barin firdausi a wajen hajiya Abu don debe mata kewa.
Tayi masu godiya kwarai dagaske ganin yanda suka dauketa tamkar yar uwa acikinsu,sukayi bankwana suka tafi.
Farhat kuwa anje asibiti ance haihuwa da saura Alh Ahmad yabawa farhan damar ya wuce da matarsa gida agani zuwa wani lokacin.
Tafiya sukeyi kan hanya yana bata shawarwari tareda dangana ga dukkan samu abu mai kyau ko mara kyau wato kaddara,sannan yake fada mata cewa wai baby baki tambayeni ina safwan ba.
Sai a lokacin tayi murmushi wanda yasa har wushiryarta ta bayyana...wlh inaso in tambaya baby na shafa'a ne,ina yake ina sisi na ko su basu san da rasuwar baffanmu ba?.
Hmmmm! Starshine ya fada can kasa kasa tareda lakuto kumatunta...ai safwan dashi akayi komai na jana'izar baffanmu,sisinki itama tazo ta fadi ta suma a lokacin akayi asibiti da ita...
Bai karasa ba ta dafe kirji nashiga uku...baby yanzu ya take muje asibitin pls.
No tun ranar rasuwan fa nake fada maki,yanzu tana gidanta da baby gal dinta a hannu.
Wow.....baby dont tell me sisi na ta haihu..ta fada cikin murna da farin ciki..duk fuskarta a kumbure ga tsohon ciki ga kukan rashin mahaifinta da tasha ga damuwar wane hali mahaifiyarta zata shiga wannan bai hanata nuna tsantsar farin cikinta a fili ba.
Oya baby mu wuce gidan sisi pls.
Fuska ya bata yace.. waike bazakije ki huta ba tukuna,bakiga babyna yana motsin yunwa yakeji kuma yana missing dadynsa isn't right?, ya daga mata gira.
Allah sai munje naga babyna tukuna...ta murtuke fuska
Toh uwar diya yana iya dole na nakaiki ai.
Kai tsaye gidan safwan suka wuce.Rungume take da babyn tana feeding nata tajiyo sallama muryar yar uwarta kamar daga sama.
Gidan makil da yan uwan safwan sunata hidima,kasancewar an daga taron suna saboda rasuwar baffah.
Taja taja babyn tasaketa tarike nipple gam dan bata koshi ba.
Yeeeee....sisi meee ta karaso kusa da ita,tareda kissing cute babe din.
Kallonta tayi wai kika haihu ban sani ba fatimah?
Haba sisi bakiga halin da muka shigaba ne ana takai wake ta kaya,kedai zauna sosai na miki maki babynki.
Ta gyara zama da kyar da kyar tasa hannu zata dauketa amma babyn taki sakin abinda takeyi suka kwashe da dariya...
Lallai aikin aikine sisi,to abarta ta koshi..
Baki fatimah ta tabe ita tagaji.
Saida farhan ya shigo yasa hannu ya dauki babyn sannan ta yarda.
Ohh...iyayenki maza sune naki zata canja zani ai...sukayi dariya baki dayansu.
Farhan yayi kissing babyn tareda cewa masha Allah...ina angon jego yashige?Wlh yaje gidansu ya dawo.
Okey!
Fatimah kun sauke kun barmu.
Ai kuma kuna hanya yaya farhan..
Uhmmn kawai farhat tace..tareda kishingidawa.*Real Aneelurv❣*
YOU ARE READING
DUHUN DAJI
General Fictioni think u will like to read DUHUN DAJI (Labarin Sark'ak'k'iyar Soyayya) By..Aneesah Abubakar Rimi