®Fikra Writers Association
©Jeedderh Lawals
Is it too late now to say soorrryyyy!!?... Yeah, I know oh oh that I let you down, but is it too late to say sorry nowww!!!
Justin Bieber -SorryWatt pad _@jeeedorhh_
Tun kafin ya gama yin parking din motar shi, junior co worker din shi yake mishi alamun yana da magana. Yana fitowa ya tare shi da zancen Managing Director dinsu yana son ganin shi, ya kara da yin kasa-kasa da murya yace "seems like you'll soon be in trouble... Deep!".
Kamal dariya yayi har dimple din shi ya lotsa, ya dafa kafadar matashin yace "believe me, I'm already in that deep trouble... Kada ka damu though, babu abinda zai faru" ya mika mishi brief case din hannunshi yace ya kai mishi office, shi Kuma ya wuce ofishin MD dinsu.
Murmushi yake dokawa lokacin da yayi knocking kofar ofishin, ya shiga. Mr. Solomon ya juya yana kallon shi, kallo daya zaka mishi ka tabbatar da cewa ran shi a matukar bace yake ba kadan ba. Kamal ya tsaya a gaban desk din shi tare da gaisar dashi, bai ma kai ga amsawa ba ya fara zuba mishi ruwan tambayoyi, "me kuka yi broadcasting last shirin ku Kamal?" ya daga kafada, "abinda muka saba, sir!".
Ya daga kai ya kalleshi sosai, "the usual? Kamal! Kasan cewa abinda kayi ya taka dokar aiki ko?" ya dan yamutsa fuska, "bai taka dokar aiki ba. Abinda muka yi shine abinda ake expecting duk wani reporter yayi, gaskiyar abinda ya faru muka fada, bamu kara komi ba".Mr Solomon ya girgiza kai, "abinda kayi ba hurumin ka bane, shiga gidan mutum da binciken gidansa ba aikinka bane Kamal, aikin police ne. Let them do their work (ka bar su suyi aikin su), kai ma kayi naka aikin. An tura muku warning notes kai da abokiyar aikin ta ka, next time am afraid ba zai zama warning note ba, ka fini sanin abinda nake nufi I believe?" Kamal ya gyada kai, "sosai, sir. Na fahimta" ya gyada kai. Drawer ya bude ya ciro ya mika mishi wasu takardu, Kamal yasa hannu ya amsa, ya duba. Mr Solomon yace "me yasa kake hada bayanai akan Alhaji Hamidu? Ina fata bashi da alaka da interview din da zamu mishi?".
Yayi kasa da kanshi ba tare daya tanka ba, hakan ya tabbatarwa da Mr Solomon zargin shi. Ya nuna shi da yatsa cikin fushi, "ka manta ko wanene Alhaji Hamidu a wajen mu ko Kamal? Ka manta cewa shi yake sponsoring dinmu ko?" Kamal yace "hakan ba shi zai hana mu fadar gaskiya akan shi ba, Sir. Mutumin nan...!"Mr Solomon ya katse shi a matukar fusace, "you stay out of this Kamal! A wajen ka aikin nan zai zama wasa, ko abun entertainment. Amma mu a gare mu, ya banbanta. Aikin nan shine komi namu, cinmu, shanmu, suturarmu, kuma rayuwar mu. Ba kai zaka yi interview din ba anyway, don haka na hane ka da kara sa hannu akan abinda ya danganci Alhaji Hamidu. Daga wannan lokacin har zuwa sanda zamu gama, kana fahimta ta?"
Kamal ya girgiza kai, "no, sir! I just can't understand. Me yasa? Kana da labarin cewa a navy officer was suspended jiya, saboda ya kama wasu muggan kaya a cikin kayan Alhaji Hamidu ya mika su ga hukumar tsaro? Indefinite suspension sir! Har sai an neme shi!! Me zaka ce akan haka, sir?". Mr Solomon ya cika ya batse, kamar zai tarwatse akan fushi. Kamal ya tsaya yana kallon yadda ya damke hannunshi yana kokari suppressing fushin daya taso mishi. Yace "baka taba saurarar mutane ko Kamal? Meye hadinka da wanda aka kora, da kayan wanda aka kama? Wannan shine karo na karshe da zamu yi maganar wannan Mr Kamal. Ka tsame hannunka akan wannan harkar, ka kula da naka aikin!".
Kamal yayi sighing, "ok sir!". Mr Solomon ya tsaya yana kallonshi sororo, cikin tsananin mamaki. Yace "ok kace Kamal, hakan yana nufin kaji abinda nace?" ya gyada kai, yace "Anya? Me kake tunanin aikatawa? A iya sani na baka taba barin case din daka fara ba, sai kaga karshen shi. Ko dai kana tunanin bullowa ta wata hanyar ne?" ya girgiza kan shi, "ko kadan sir. Ina da case much more important than this one, sai nayi tunanin meye na bata lokaci na akan wannan?" Mr Solomon ya gyada kai, "haka ne! If that's the case then, zaka iya tafiya" yace "ok sir, na barka lafiya". Ya fita daga cikin ofishin.
YOU ARE READING
Doctor Sheerah! (SAMPLE ONLY)
SpiritualRayuwarta, farincikinta, damuwarta, tashin hankalinta, komi nata ya ta'allaka ga mutanen nan su biyu ne kacal! Su kadai take kallo taci gaba da rayuwa kamar babu wata damuwa a ranta, her world revolves around them!! Me zai faru lokacin da abubuwa s...