1

2K 142 9
                                    

2007. A KAUYEN RARIYA

"Innalillahi wainna ilayhirrajiun! Yau babu kuluwa. Lokaci yayi kwana sun kare!"

Kalmar da ke fita daga bakin tsohuwar kenan wadda take fitowa daga cikin daki a rikice. Fadin hakan yasa Amina bata san lokacin da ta fadi zaune ba akan tabarmar kaba (wundi) mai kalar hankaka dake shimfide a tsakar gida. Daga nan ta fasa kuka sai yaran gidan da jamila matar iliya kanin maigidan suka karba, kuka mai tsima rai da ban tausayi. Kukan rashi wanda ke alama da faruwar mai yanke jin dadi, da sabo.

Kafin wani lokaci gidan ya fara cika da jama'a mafi akasari matan da ke makwabtaka da gidan mutuwar wato gidan Abu direba. Daga baya kuma sai ga maza sun shigo a karkashin jagorancin kanin maigidan iliyan Abu direba, matarsa ce jamila ta aika yara zuwa can shagon da yake dinki suka fada mai rasuwar. Ya firgita kwarai da a ka fada masa rasuwar. Bai tsaya ko ina ba sai gidan Liman, ya sanad dashi rasuwar. Tare da wasu abokan sana'arsa da Liman suka shigo gidan.
Abubuwan da suka biyo baya sune koke koke da ban hakuri musamman a tsakanin mata da yaran gidan. A karshe dai liman ya tsawatar aka sassauta da kukan sannan aka fara shirin wankan gawar marigayiya kuluwa uwargidan Abu direba, malama asabe da sauran mata masu ilmin islama da kuma karfin hali ne suka wanke gawar.

Duk kaye kayen nan da a keyi, Amina tana nan zaune akan tabarma tana ta sharbar kuka. Bambanci kawai shine yanzu akwai mutane zaune a tare da ita. Biyu daga ciki 'ya'yan mai rasuwa ne kuma 'ya'yan mijinta Abu direba. Yaran kuluwa su hudu ne duka, kasimu, imrana, hafsi, sai karamin goyon da ta bari wato Amina mai sunan amarya ana kiranta momi. Kuluwa ce ta roka aka sa sunan.

Haka a kayi ta shige da fice ana tambayar abubuwa kamar su turare, ganyen magarya da auduga, a gefe daya kuma an dora tukunyar ruwan zafi da ake diba zuwa dakin mai rasuwa har aka wanke gawar a bisa tsarin addinin islama. iliya ne ya shigo da farin likkafani dinkakke, malama ta karba aka shiga suturta gawar bayan an kammala wanka. Daga nan iliya da wasu maza suka shiga su ka fito da gawar akan karaga zuwa makabarta. Fitowa da gawar yasa mafiyawan jama'ar dake cikin gidan suka sake fashewa da kuka mai sauti, masu natsuwa a ciki suka dinga Salati, Hailala, wasu kuma suna fadin Innalillahi wainna ilayhirrajiun!!

Bayan an dawo daga makabarta ne mutane maza suka dinga shigowa gidan (a bisa tsarin al'adar malam bahaushe) suke kara gaisawa da mutanen dake zaune wato 'yan karbar gaisuwa. Mata musamman ba cikin unguwar, makwabta da abokan arziki suka dinga tururuwar shigowa gaisuwa su jajanta akan rashin kuluwa tare da addu'a da fatar Allah Ya gafarta. Abinda yayi ta faruwa kenan har zuwa la'asar, a gefe daya kuma wasu mata sun dora tukunyar abinci, kafin magariba aka sauke tuwo da miyar kuka ana ta rabawa mutane daga cikin gida har zuwa waje. Haka aka yi ta shigowa da abinci cikin manyan languna da kulolin abinci irin tsarin mutanen karkara. Jamila ce take ta kokarin ganin yaran gidan sunci abinci, malama asabe kuma tana tsaye akan amina da take kuka babu kakkautawa, haka ma taki cin abinci, da kyar take shan farau farau idan aka matsa ta.

Washegarin rasuwar, Abu direba ya iso garin cikin tashin hankali da alhinin rashin kuluwa. Iliya ne ya kira shi tun kafin a je makabarta ya fada mai cewa yayi kokari yazo gida, rashin lafiyar kuluwa ya tashi. Duk yadda 'yan uwansa suka so kar ya samu labarin rasuwar har sai ya iso gida, hakan bai samu ba, a dalilin kiran wayarsa da jama'ar gari su ke tayi su na yi masa gaisuwa. Da ya fahimci abinda ya faru, sai ya kira malam liman wanda bayan zamansa liman, kuma aboki ne ga mahaifinsu a lokacin da yake raye, anan ya kara tabbatarwa mai faruwa ta faru. A lokacin marece ne, kuma suna a jihar katsina, daga karshe yaron motarsa da direbobi abokan aikinsa suka hana shi tasowa shi kadai yadda yaso. Sai aka saka shi motar wani direban da zaya zo Sokoto, tashi motar kuma aka ce za a kawo har garinsu rariya.

Ya iso gida cike da tashin hankali, ya kara tabbatarwa kuluwa ta amsa kiran Mahalicci, zuciyarsa ta gigita sosai, ya samu kanshi cikin rudani da damuwa da halin da-na-sani. Ya shiga dakin marigayiya, ya gaisa da danginta. Yayarta ce rike da jaririya amina da bata wuce wata daya da haihuwa ba, wanda ga dukan alamu itace zata ci gaba da rainonta tunda ita ma tana shayarwa, ko banza amina matar mahaifinsu da bata cika shekaru biyu a gidan ba, akwai kuruciya a tattare da ita. Daga dakin kuluwa da ya fito, sai ya shiga dakin amina, mata da yaran da ke ciki suka mike suka fita, aiko sai ya fashe da kuka kamar ba namiji ba, ita ma amina sai ta durkusa kusa da shi ta fashe da kuka tana bashi hakuri. Sun dade a haka yana rike da hannunta yana kuka yana cewa "amina na shiga uku Allah Yasa kuluwa ta yafe min." Duk da tausayinshi da take ji sai da amina tayi tunanin ashe dai baban kasim yasan baya kyautawa! Sun dade a daki babu wanda ke iya lallashin wani, ita sharer hawaye shi kuma ajiyar zuciya!

A karshe iliya da yawale taubashinsa ne suka zo suka fita dashi waje, saboda mutanen gari da suke ta zuwa yi masa gaisuwa. Duk da yana cikin yanayi na damuwa da rikici, dole ya fita ya zauna yana amsa gaisuwa. Amma duk wanda ya kalleshi yasan yana cikin matsananciyar damuwa.

A cikin gida ko tunani ne fal a cikin zukatan jama'a musamman amina da dangin kuluwa. Takaicine a zuciyar dangin na marigayiya, mafiyawa suna tunanin hakuri da juriya irin na kuluwa akan mijinta da zaman hakurin da tayi da shi a tsawon rayuwar aurensu. Ita kuma amina mamaki ta keyi ashe baban kasim yasan ya abinda ya keyi baya kyautawa, yau shine yake kuka akan kuluwa, kuluwar da yake zalunta, ya danne ma ta hakkokinta? Kuluwar da yake duka ya zage ta kamar ba uwar 'yayansa ba! A gefe daya kuma tana tunani ko yaya rayuwarta zata kasance a wannan gida alhali babu kuluwa? Yaya zata iya zama da baban kasim da yaran ita kadai babu mataimaki? Wannan yasa ta kara fashewa da kuka.

Kallabi ko HulaWhere stories live. Discover now