Ranaku suka shude zuwa makonni, haka makonni suka hadu suka zama watanni sai ga kuluwa ta samu kusan wata bakwai da rasuwa. Abubuwa da yawa sun faru a lokacin, daga farko kamar Abu direba zaya canza munanan halayensa zuwa nagari, amma daga baya da mutuwar ta zama jiki, sai ungulu ta koma a gidanta na tsamiya, halayensa da ake ganin ya fara gyarawa, kamar rashin kulawa akan yara da hakkokin iyali na tsakar gida duk sai ya ci gaba da abinsa. Amina bata samun matsala da yaran kuluwa, mahaifinsu dai shine matsalar.Tun farkon tarewarta gidan Abu direba ta fahimci cewa azzalumi ne. Na farko baya ciyar da iyalansa da kyau alhali yana da hali da ikon da zai yi hakan. Sannan baya mutunta matarsa kuluwa duk da yawan hakurinta da biyayya. Daga farko zuwanta ya kawo canji a rayuwar gidan kwarai da gaske, saboda takan yi tsaye sai yayi wasu Abubuwa da bai yi niyya ba duk da karancin shekarunta kamar ta fannin abinci ko suttura da sayen magani. Tana tilasta ma yaranshi zuwa makarantar allo da ta boko kuma ta matsa akan sai ya biya duka abinda aka ce a saye a makarantar, duk da ba wasu kudi masu yawa bane, amma Abu ya na kyashin ya cire ya biya.
Idan ta matsa shi yayi wani abin daga karshe sai ya sauke haushi akan kuluwa mareniyarsa, saboda Allah Ya jarrabeshi da son amina, don ma ita din bata bashi hadin kai yadda yake so, koda yaushe hankalinta da kulawarta yana akan kuluwa da yara. Ya sha fada da ita akan su har yace mata, “wai kuluwa da ‘ya'yanta kike aure ko kuma ni?” tun tana kyaleshi saboda tana ganinshi babba wanda ya girme ta da shekaru masu yawa, da kuma gudun kada ya kai kararta gun babanta ko kakarta, har ta fara mayar ma sa da martani takan fada ma sa “wallahi baban kasim ka ji tsoron Allah, idan baka kyautata musu ba ina nike da tabbacin cewa ni zaka dore da kyautata min?” wani lokacin idan ya sawo mata wani abin ita kadai yana nema ya bata cikin sirri, takan fada mai ita bata iya cin hakkin kuluwa ba. Shi da yaga zai iya yayi ta dannewa. Idan irin haka ta faru sai yace “wallahi ke yarinyar nan ‘yar rainin wayo ce, babu abinda mutum zai yi ya birge ki.”
A lokuta da yawa ita ke tare ma kuluwa fadansa na rashin hujja, idan tsiyarta ta tashi zai yi fada da kuluwa amma ita zata dauki fushi da shi na kwanaki. Haka abin za ya dameshi, sai ya dinga sayayya daga garuruwan da yake zuwa kai pasinja, yayi ta hidima dasu matansa da yara har sai yaga murmushinta sannan zai samu nutsuwa. Wani zubin kuma idan Abu ya hado su sai ta tattaro yara daga dakinsu ta kwana dasu alhali tasan girkinta ne, kuma tasan babu abinda ya ke hasala Abu kamar ta hana shi kanta. Yara kuma da basu san dawan garin ba, sai suyi ta murna zasu kwana a dakin mama amarya suna jin dadi zasu hau kan gado da doguwar kujera. To gado ne wanda duk a garin rariya babu mai irinshi. Duk lokacin da hakan ta faru sai Abu ya sauke haushi akan kuluwa. Da kyar kuluwa ta shawo kan amina ta daina amfani da yara tana bata ran babansu.
Ana cewa sabo turken wawa, amma amina ta kasa sabo da Abu da halayyarsa balle ta bude zuciyarta ta kaunace shi. Rasuwar kuluwa maimakon su kara ba juna kulawa, sai kowanne ya kasa hakuri da danuwansa, shi yana ganin ta raina shi, kullum fada akan ‘ya’yan da ba ita ta haifesu ba, ita kuma tana yi mai kallon mara imani, tunda ko mutuwa bata sa ya daina halayensa ba. Baya kula da yaran yadda ya kamata, kamar karatunsu ko ibada, dalafiyarsu. Dai a wuni a gidan babu wani abinci mai inganci, ko da yana gari bai je wani gari ba. Sai dare yayi ya sawo kaza, ko ya zo da tsire da madarar kwali ko lemon kwalba yana neman kasancewa da ita matarsa. Kasancewar da tafi komi bata ma ta rai, take kuma wahalar da ita.
Watarana ya dawo daga zamfara ta fada mai babu ko sukarin da yara zasu sha kunu, kuma basu da takalma silifas, sabulun wanka da na wanki. Bai kula ba ya fice, sai dare ya dawo dauke da ledar gasasshen nama. Can cikin bacci taji shi yana so ya haike mata, ta dakatar dashi ta na tambaya ko yazo da wadancan abubuwan amfani da ta fada mai? Cikin bacin rai yace, “iskancin naki ya tashi kenan, ‘yar rainin hankali, ban sawo ba sai gobe idan na fita.” Tace amma ka san cewa gobe tun safe su kasim ke zuwa…….” Bata karasa baya jawo ta zuwa gareshi, ita kuma ta kwace kanta, daga nan sai fada cikin dare, har yana cewa “wai ke amina me kike takama da shi ne? ko kin manta asalinki ke jinin tubabbiya ce, idan ba don ina tausayin mahaifinki ba, wane namiji ne zai yarda ya auri mace irinki” Ran amina ya baci fiye da ko yaushe, hakan yasa ta rufe ido ta fada mai duk abinda ya fito daga zuciya zuwa bakinta, tace “naji ni din jinin tubabbiya ce, kai haifaffen musulunci amma kana halin jahilai, jahilan ma na kauye.” “sosai ni haifaffen musulmi ne uwa da uba, kuma duk abinki nine mijinki sai na daga kafa za ki shiga aljanna ba.” Ta share hawaye tace duk abinda ka keyi wallahi Allah zai yi maganinka, kuma zai saka mana ni da maman kasim, Allah Ya isa!!” Ya sa hannu ya mareta sau biyu abinda bai taba gwadawa ba (sai akan kuluwa). Sannan ya fice daga dakin ya koma zauren gidan ya kwanta.
Gari bai gama wayewa ba taji motsin fitarshi zuwa masallaci, sai ta laluba kudi a aljihunsa ta kwashe duka ta sulale ta fita daga gidan ba tare da kowa ya gane ta ba. Sai da tayi tafiya mai nisa da sauran duhun asuba, sannan ta hau mashin har zuwa tashar garin dange da ke kusa da kauyen na rariya, kuma wanda yake nan ne mahaifarta garin mahaifinta. Anan tayi sallar asuba, daga nan ta sake hawan mota sai babbar tashar mota garin Sokoto. Karfe takwas da kusan rabi ta hau motar da zata kai ta gusau a jihar zamfara. A garin gusau ta wuce zuwa unguwar gada biyu.
Isarta gidan keda wuya, taci karo da mama churi kakarta a tsakar gida da alamu zata fita unguwa, sai suka rungume juna suna kuka. Saboda ta dade bata ganeta ba. Bayan sun zauna amina ta sha shayi mai zafi da fanken da mama churi ke saidawa, a nan take fada ma ta duka abubuwan dake faruwa. Mama churi ta fara zage zagen da ta saba, har tana fadin “wannan abin shi nayi ta hangowa a lokacin da mahaifiyarki zata auri bahaushe, bahaushen ma musulmi” sai kuma rayuwar amina ta fara baci, “mama ba fa don yana musulmi bane, halinsa ne.” mama churi dai bata fasa fadanta ba, yi takeyi tana zage zage, tayi da hausa tayi da fulatanci. Ladi ‘yaruwarta dake taya ta zama tana ta bayar da hakuri.
A ranar ko harkokin sana’ar ta bata aiwatar ba, hawan jininta ya tashi sosai, sai ga amina da ta dako yaji daga gidan miji ta koma jinya. Kamar yadda ta keyi duk lokacin da ta zo gidan, a makwabta gidan malam usman taje ta aro shimfidar sallah tayi sallar azahar, sannan ta dora abinci. Daga baya mama churi ta farka daga bacci, a lokacin amina tana waje tana sallar laasar. Ta dauko wayarta ta kira musa dan ta da yake aiki a kaduna, tace yayi kokari yazo gida akwai matsala!!
YOU ARE READING
Kallabi ko Hula
General FictionA tsakanin Haihuwa zuwa Mutuwa, Mutum dan-adam ya kan rayu ne a bisa kaddararsa. Ingancin rayuwar mace ko namiji sun ta'allaka ne akan abubuwa da dama ciki har da iyalan da ya fito daga ciki wato iyaye, dangi - da kuma gidan aure. Aure babban abu n...