3

621 73 5
                                    


Musa bai iso ba sai washegari da safe, yana zuwa ya samu labarin duka abinda ya faru. Ya damu kwarai, amma babu abinda zai iya yi akai, idan ya tuna inda aka fito. Ya zaunar da amina ya bata hakuri.

Cikin tausasa harshe yace “kiyi hakuri meenah, munyi wannan maganar tuntuni, bazan so mu kara zama sanadiyyar da zaki kara samun matsala da familyn babanki ba, zan mayar da ke, idan yaso sai muyi Magana da magabata akan kada ya kara dukanki.

Cikin zafin rai da daga murya Mama churi tace “musa zaka mayar da ita ne a gun makiyanmu a kashe ta kamar yadda aka kashe mahaifiyarta! A gaskiya ban yarda ba, duk abinda zai faru sai dai ya faru.”

Yayi murmushin takaici yace “mama kin manta abinda ya faru tsakani na da iyayen amina shekara biyu da suka wuce? Ko kin manta da cewa mahaifinta da kakarta sun kafa min doka akan idan na kara shiga harkar amina ba tare da izinin ko saninsu ba zamu koma kotu?”

A nan kuma mama churi ta fasa kuka tana kururuwa tana kiran “Yesu al-masihu. Na rantse na tabbata, lalle kuruwar saratu dana mahaifinta ja’e zasu zo su dauki fansa akan umaru da danginsa.” Haka tayi ta mugun fata akan umaru dange da danginsa, amina ta makure akan kujera can gefe daya.

Bayan musa ya lallasheta, aka samu ta daina kuka da zage zage, aka bata maganin tasha, sai ya umurci amina ta tashi su koma zai mayar da ita har garin rariya.

Ko gardama ba tayi ba, saboda rashin son musulunci irin na kakarta churi yana tayar mata da hankali, a ranta take fadi, “ita ba irin uncle musa bace, shi ba ruwansa da sukar addinin da ba nashi ba.”

Ya dauke ta a mota bai zame ko ina ba duk da gajiyar da yake ji sai garin rariya. Yaje har gidan liman suka wuce gidan hakimi, sannan aka kira Abu direba wanda yake can hankalinsa a tashe yana neman amina.

Mahaifinta mal umar shi ma yazo garin bayan ya samu kira daga liman duk akan bacewarta. Aka zauna a wajen hakimi, musa yayi bayani tare da bayar da hakuri akan abinda aminar tayi.

Abu direba yaso ya tayar da jidali ya dora laifi akan musa, amma ga mamakinsa, sai yaji malam umar yace “babu mai laifi sai kai Abu, saboda kai ne ka doki matarka har ta gudu. Kuma wallahi wannan ya zama na karshe da zaka doke ta don ba jaka muka kawo maka ba.”

Liman ya kara da yaba ma musa da yayi amfani da hankali ya mayar da ita. Sannan aka ce Abu ka da ya kara sa hannu ya doke ta. Cikin fushi Abu ya fito daga fadar hakimi, akan cewa da dare Iya matar hakimi zata sa a mayar da amina dakinta.

Kafin su rabu, Mal. Umar yayi amfani da wannan dama bayan Abu ya fita, ya ba musa hakuri akan abinda ya faru shekarun baya da suka wuce. Daga karshe musa ya kebe da amina ya bata waya karama kirar nokia da kudi, yace “duk abinda take so meenah ki kira ni a waya, ki daina zaginshi har yana dukanki haka.” Tana kuka su kayi sallama ya kama hanyar komawa zai kwana a garin sokoto, da safe ya kama hanya.

Tun bayan dawowar amina, sai zama yaki dadi tsakaninta da Abu. Saboda ta fahimci yanzu mahaifinta ya dawo daga rakiyarsa. Inna hadi kakarta dake can dange ita kadai take goyon bayan Abu, saboda ya saye ta da kudi da ‘yan tsarabobin da yake kai mata tun asali. Ita a ganinta tsageranci ne kawai irin na amina yake hana su zaman lafiya. Shi kuma Abu yanzu ganinsa ya keyi daidai da kowa, ko banza yanzu ya rena mahaifinta tunda ya daina goya ma sa baya kuma ya fishi hanyar samu saboda tukin mota ya amshe shi, Abu kadan yayi mata gori akan tana alfahari da kafirai.

Takan dauki matakin hanashi kanta saboda hakan, shi kuma ya kira ta ‘yar wuta. Jamila tayi ta kokarin bata shawara akan ta kwantar da hankalinta tunda mijinta yana son kasancewa da ita, idan tana ba shi hadin kai zata samo kanshi. Amma amina tayi nisa a kiyayyar da ta keyi ma Abu, ta tsani halayensa, kuma tun farko ta saka shi a layin wadanda aka hada kai dasu aka cuce ta, ta hanyar aurar da ita gareshi ba da son ranta ba, a lokacin da ba tayi zato ba, kuma akan laifin da ba’a tsaya anyi bincike ba.

Wata biyu bayan dawowarta daga gusau, su kayi fada cikin dare akan yaki sawo maganin yara suna ta fama da zazzabi. Ya kira ta dangin chochi, tace “dadin abin da uba ake takama kuma babu wanda yafi wani a wajen Allah sai wanda yafi imani” sai ya amsa mata da cewa “mahaifinki da ya auro arniya aka mallakeshi, minene bamu sani ba, sakarya, waya sani ma ko can chochin aka cinye mahaifarki baki haihu ba sai famar sa ido akan ‘yayan wasu”

Amina ta harzuka ta fara ramawa daga nan ya fara kai mata duka ta ko ina bayan ya kulle daki. Su kasim suka ruga a guje suka kira iliya, da kyar aka fito dashi dakin bayan yayi ma amina dukan kawo wuka, baki da hanci duka sun fashe suna fitar da jini.

Kallabi ko HulaWhere stories live. Discover now