Five

2.5K 301 21
                                    

®Fikrah Writers Association🖊

©Jeedderh Lawals


"Am afraid to say, condition din da take ciki yanzu dole sai anyi mata dialysis gaskiya!".

Sheerah ta furta a sanyaye, kuma a nutse tana sauke kallonta akan Ramlah data zaro idanunta waje. Kamal ya gyara zaman shi akan kujerar da yake kai yana kallon kanwar tashi cikin damuwa da kulawa wanda suka fita tun daga kasan zuciyarshi. Sheerah had no choice but to feel a little pang of sadness a cikin zuciyarta, inama!!

Yace "babu wata hanya da zamu bi, Doctor? Dole sai wannan?" ta girgiza kai, "wannan ita kadai ce mafita. But hey, it's just dialysis not a big deal I promise. Bashi da wani wahala, ko side effects. Da anyi shi zata dawo normal I assure you!". Ta kallesu, bata yi missing kallon kulawar da Kamal yake wa Ramlah ba, yayin da a bangarenta ta nuna kiris take jira ta rushe da kuka. Ta kara da cewa, "beside ba wai yana daukan lokaci bane. May be kamar minti talatin? Zamu sa tube a jikinta, mu yi amfani da inji wanda zai zuke wastes din. Zamu yi shi kaman sau uku a sati, shikenan. Sai dokoki da zamu kafa mata wannan idan aka bi su, komi zai daidaita in shaa Allah!".

Ya lumshe idanunshi yana kokarin calming nerves dinshi daga bugawar da zuciyar shi take yi. "Ok.. Zuwa yaushe kike tunanin za ayi aikin?" tace "ko zuwa gobene, saboda bana tunanin muna da saurin lokacin da zamu bata. Zamu rike ta a asibitin daga yanzu domin mu tabbatar da jininta is normal and stable saboda gudun samun complications... Before then, sai kuyi kokarin settling medical expenses saboda...!".
Ramlah ta katse ta da sauri, tace "Yaya! Ni dai gaskiya ba anan za ayi min aikin ba!" hankalin shi ya maida gareta kacokam, "sai ina?" ta turo baki, "ni dai ba a Nigeria ba!" yayi kasa-kasa da idanunshi, "me yasa baby?" tayi raurau da idanunta, "kaga fa Yayan Ubaida kawata da aka mishi dashen koda mutuwa yayi" yayi shiru yana kallonta, speechless.

Doctor ta dan rausayar da kanta tana kallon Ramlah, tace "ina jin baki fahimci wani abu ba. Muna maganar cire wastes daga cikin koda ne, ba wai yin dashen koda ba. Kina jin tsoron kar ki mutu ne, ko kuma kawai baki kaunar a miki aikin ne a Nigeria?".
Ramlah ta gyada kanta, "duka! Babu kayan aiki masu kyau a Nigeria, babu kwararrun likitoci kwararru! Aje garin yin aiki a tabo min wani wajen a barka da wahala!".

Tace "duk abinda kike bukata a kasashen masu jajayen kunne, daga likitocin har kayan aikin muma muna dasu anan, zan iya cewa mun ma fisu kwarewa a wani abun!".
Ramlah ta kalleta a yatsine, "doctor! Idan kudin aikin da zaki rasa ne kike wa ki fada mana kawai, ba wai ki zauna kina wani kauce-kauce ba...!". Sheerah ta kalleta na dan wani lokaci, murmushi ta dan sakar mata tare da girgiza kanta, "ko kadan patient.. I'm just..." ta daga kafada, "forget it kawai! Zaku iya tafiya duk inda kuke ganin zai muku".

Kamal yace "ko Akwai maganin da zaki mata prescribing wanda zai taimaka mata zuwa lokacin da zamu tafi, kamar kwana uku ko hudu haka?" kallonshi tayi sosai tana kissima wani abu a ranta, kanta ta girgiza a sanyaye "wannan ba hurumi na bane. Amma zaku iya zuwa ko wane pharmacy, nasan idan kuka yi musu bayanin zaku samu biyan bukata".

Kamal ya daga gira, "da alamun kanwata ta bata miki rai doctor?" kai ta girgiza, "ko kadan. Believe me, na hadu da patients iri-iri, cikin abubuwan dake faruwa kuwa ko irin wannan showing off din, kanwar ka bata yi komi cikin wanda suke yi ba. So I understand, ina dai fada muku abinda yake kenan ne. Ramlah ba patient dina bace, bani da right din rubuta mata wani magani kuma... Zaku iya tafiya!". Kamal ya yunkura zai yi magana, tayi saurin katse shi, "Akwai patients da dama dake son gani na, idan kuka ci gaba da zama anan zaku shiga hakkinsu!".

Ramlah tayi rau-rau da idanu, "Doctor idan maganganuna ne suka bata miki rai, don Allah kiyi hakuri. Ban fada don in bata miki rai ba". Sheerah ta maida kallonta gareta, "ko kadan bai baci ba". Tace "to don Allah ki rubuta min maganin kinji?!".
Yar dariya ta saki tare da rolling idanunta, "since you insist, bana tunanin ina da wani zabi, do I?" dariya suka saki su duka. Takarda ta yaga ta rubuta ta mika musu, "gashi, Allah yasa ayi aiki lafiya" Kamal ya amshi takardar, "mun gode doctor!". Ramlah ta tashi tsaye, ta sake wa Sheerah godiya, Kamal ya saka ta a gaba suka bar ofishin. Ajiyar zuciya ta sauke bayan sun fita, ta danna intercom "send next patient in, please!".

Doctor Sheerah! (SAMPLE ONLY)Where stories live. Discover now