Har lectures din ya k'are Labeeba bata fahimci komai ba, a hanyarsu na zuwa Masallaci yin Sallahr Azahar, Aisha Usman K'awarta take tambayarta lafiya yau ta ganta wani sukuku da ita, jim tayi kafin tace "Kaina ne yake dan ciwo amma ya bari yanzu" Aisha tace "haba ni dai ince, yau na ganki ga ki nan, Allah ya sauwak'e" murmushi Labiba tayi tana kara k'allon k'awarta.
Kafin su k'arasa Masallaci suka ji ana k'wala musu kira ta baya, dakatawa suka yi tare da dan waigawa, cikin hanzari ya k'araso yana me sakin su da k'ayattacen murmushi.
"Aisha, Labeeba, ya kuke?" a tare suka amsa masa da Ina wuni Captain Abu Sideeq? Ya amsa tare da cewa "kun gama lectures din yau ai?" Aisha ta gyada kai, Labeeba tace "eh mun gama" yace "Good, to kuje kuyi Sallahr, ku sameni a Ajinmu, sai mu duba karatun yau ko na 1hr ne" amsawa suka yi tare da wuce shi don nufar Masallacin.
Aisha tace "Son ki yake" Murmushi Labiba tayi, tace "na sani" da doki Aisha tace "I knew it, kema kina sonshi?" Labeeba ta sake wani murmushin kafin tace "ina dai ganin mutuncinshi, yana kuma burgeni, ina son naga mutum me k'wazo da basira" Aisha ta dan tafa hannuwanta tace "a sannu kema zaki fara son shi, ai ya hadune ya hada komai, ga bokon, ga addinin, ga kuma Kyaun".
Labiba tace "ba k'arya".
Daidai nan suka iso Masallaci, ko waccen su ta d'auki buta ta nufi Fampo.
Sun idar da Sallah suka nufi ND2 inda AbuSideeq yake, yana ganinsu ya k'araso yana jefan Labiba da wani irin kallon da shi kawai ya san ma'anarsa.
Murmushi kawai Labiba tayi, yace "muje daga k'arshen Ajin, yana gaba suna bin shi a baya, daga can suka samo Bench suka zauna, shi ne a tsakiyarsu, ba bata lokaci suka hado masa Jotting din Lectures Biyu da suka yi yau, dubawa ya yi kafin ya shiga yi musu bayani cike da k'warewa.
K'arfe 2:30 ya ce su dakata haka. Godiya suka masa me tarin yawa, ganin yadda AbuSideeq ke bin Labiba da wani irin kallo ya sa Aisha ta dan mik'e ta ce "bari na dan amsa waya".
Ganin haka yasa AbuSideeq fara magana "Labiba..." sai kuma ya yi shiru, ya sake fadin "Labiba ina... ina..." sai ya sake yin shiru, sai da, mintuna kusan 4 suka wuce kafin ya ce "bansan ya zaki dauki maganar nan ba, amma ina so in fada miki wani abu, amma kuma dai na kasa, k'ila rashin faden shi ne Alheri, bari kawai in bar shi, tashi muje na rakaku ku samu abun hawa".
Dago idanuwanta tayi ta kalle shi, kafin ta saukar da kai ta fara magana cikin sanyinta ta ce "So na kake yi, kana jin nauyi na, kana tsoron yadda za ka gaya mini, kana gudun kar hakan ya zaman silar bacewar kyakyawar Alak'ar da ke tsakaninmu?" da sauri ya kalleta.
Kai ya fara gyadawa kamar k'adangare. "Haka ne, wallahi haka ne Labiba, tun farkon haduwarmu a office din HOD, lokacin da Yayanki ya rakoki Registeration na kamu da sonki" Labiba ta danyi murmushi ta ce; "Ban yi mamaki ba, its obvious ai".
K'arfin guiwa ya samu, ya ce "Ina fatan zaki amince mini?" murmushi tayi ta ce "wallahi ban sani ba, bansan me nake ji a kanka ba, bansan me zanji nan gaba a kanka ba, amma nasan cewa ina matuk'ar ganin girmanka, sosai kake burgeni Captain, bansan ko nan gaba wata alak'a da ta wuce wannan zata shiga tsakaninmu ba, amma ko me ke nan, Allah ya zaba mana abin da yafi Alheri a rayuwarmu".Kallonta kawai ya tsaya yi, sosai ta burgeshi, sonta na k'ara ruruwa a zuciyarshi, bai taba ganin irinta ba, bai taba sanin Matan Katsina na iya kallon Namiji haka su gaya masa gaskaya ba tare da wani 6oye-6oye ba, ba ta rufe mishi komai ba, ta gaya mishi iyakar gaskiyarta, hakan da tayi ta matukar burge shi, yana da tabbacin da wata ce, yaudarar shi za ta yi, ko ta ce mishi eh itama tana sonshi ko don wani abu, ko kuma ta bata mishi lokaci, ko kuma ta ja mishi aji, haka yake so Mata su kasance Straightforward, in ana haka, da ba a samu Yaudara da cin amana a cikin Soyayya ba.
YOU ARE READING
DAN MAKAHO...
RomanceShi ba Makaho bane, amma ido daya gareshi, k'addara ya sa mai nakasu a idonshi na hagu, DANMAKAHO sunan da yan unguwa ke kiranshi dashi. * Bata san So ba, daga bisani Allah ya jarabbeta da son dan Shaye-shaye, dan zaman majalisa, dan zaman ka...