®Fikrah Writers Association🖊
©Jeedderh Lawals
Baki Kamal ya bude, cike da mamaki, mamaki, da wani mamakin dai. Ta kalli tsakiyar idanunshi ta saki wani sly smile. Ta matsa gaban gadon Ramlah ta dudduba yanayin vitals da blood pressure dinta, taga komi normal. Nan ta juya ta kalli su Alhaji AbdulQadeer, hakuri ta basu akan lattin da tayi tare da kara yi musu bayanin yanayin aikin da zasu wa Ramlah.
Tace "in shaa Allah ba zamu wuce mintuna hamsin ba, kada ku tashi hankalinku. Chance din is 98%, saboda haka ina tabbatar muku zamu fito lafiya!" su duka suka hada baki wajen furta, "Ameen... In shaa Allah!".
Ta juya ga wata matron balarabiya, cikin harshen larabci take mata magana. Ta mikawa matron din keys da waya, da sauri ta juya, yayin da Sheerah ta bada umarnin tura Ramlah zuwa dakin tiyata, ta bi bayan su.
Sai da aka rufe kofar wajen, sannan Kamal da mahaifan shi suka koma kan kujeru suka zauna. Mahaifinshi ya dube shi yace, "taya aka yi kuka san likitar nan, Kamal?".
Kamal ya ciza tattausan lebenshi cikin rashin sanin abin cewa, even in his wildest dream bai taba tunanin cewa lamarin zai juya ya zama haka ba. A gida ce musu yayi likita ne da kan shi ya musu recommending din asibitin, to yanzu kuma sai yazo yace musu me? Likitar data roki su zauna ta musu aiki a Nigeria da bakinta, suka ki? To amma idan ba hakan ba, me zai ce? Iyayensu basu dora su akan turbar yi musu karya ba balle boye musu abubuwan da suka shafe su. Kan shi a kasa, bai iya daga ido ya kallesu ba, ya zayyane musu duk abinda ya faru tsananin su da Sheerah.
Alhaji AbdulQadeer hararar shi kawai yake yi tunda ya fara magana har ya dasa aya, bai yi kuskuren kallonshi ba don yasan ba zasu kwashe ta dadi ba, gani yake kamar a kowane lokaci ruwan mashi zasu iya fita daga cikin idanuwan mahaifin nashi, su sossoke shi.
Nan ya shiga surfa mishi ruwan fada, ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba. Sai da Hajiya Aina'u ta shiga zancen, "Haba Alhaji. Don Allah ka bar fadan nan zuwa anjima. Yanzu dai muji da Addu'ar samun nasarar aikin nan" Daddy ya kuta yace "haka ne kuma... Amma zamu gauraya daku ne ina fada muku! Daga kai har Ramlah!!" Kamal dai bai furta uffan ba. Suka cigaba da zama anan, bakinsu dauke da addu'o'i fili da boye.Can Mommy ta dakata cikin tunani. A hankali ta daga kai ta kalli Kamal tace, "sunan likitar can sounds familiar to me... Sunan ta ma kamar na taba jin shi a wani wuri, amma na kasa tunawa". Kamal yayi shiru yana kallonta.
Awa daya bata yi ba, aka bude theatre room din, aka gangaro gadon da unconscious Ramlah take kwance akai, Dr. Sheerah cikin doguwar light ash surgery gown tana binsu a baya. Duka suka tashi tsaye. Ta tsaya a gaban su tace "it was successful Alhamdulillah! Sai zuwa gobe da yamma sannan zamu sake yin wani dialysis din. Zaku iya binsu kuga dakin da za a kwantar da ita. Anaesthesia din da aka mata ba mai karfi bace sosai, zata iya farkawa nan da kowane lokaci in shaa Allah". Suka mata godiya, ta wuce doctors lounge domin ta canza kayan jikinta, su kuma suka bi bayan nurse din dake tura gadon Ramlah har zuwa dakin da aka bata. Nurse din ta saita duk wata na'ura data kamata, ta musu sallama ta fita. Dakin karami ne, manne da bandaki sai kujeru hutu mai cin mutane biyu. Daddy da Kamal suka zauna, Mommy kuma taja arm chair kusa da gadon ta zauna.
Ramlah ta tashi lafiya qalau, har suka sha hira da ita. Anan suka yi Sallar Azuhur, la'asar har ma da Magriba. Da suka fita sallah Kamal ya siyo musu abinci suka ci, ita Ramlah asibitin ya bata nata. Ruwa mai dumi da abinci mai ruwa. Suna wajenta har karfe goma na dare ta gota, tuni Ramlah ta koma barci. Suna shawarar su tashi su koma masauki, su bar Mommy a wajen Ramlah, wata nurse ta shigo dakin. Tace musu basa bari a kwana da majinyaci.
Mommy tace "ya za ayi mu bar mara lafiya ita daya? Idan wata bukatar ta taso fa?" nurse din ta mata murmushi politely tace "kada ku damu Ma'am. Akwai wadanda suke kula da majinyata anan, suna karkashin kulawar mu". Ba don sun so ba, haka suka tafi suna waiwayen Ramlah.
ESTÁS LEYENDO
Doctor Sheerah! (SAMPLE ONLY)
EspiritualRayuwarta, farincikinta, damuwarta, tashin hankalinta, komi nata ya ta'allaka ga mutanen nan su biyu ne kacal! Su kadai take kallo taci gaba da rayuwa kamar babu wata damuwa a ranta, her world revolves around them!! Me zai faru lokacin da abubuwa s...