5

669 66 8
                                    


Abu direba yana zuwa gidan hakimi cike da karsashi yana tunanin babu yadda za'ayi dashi. A ganinsa dole a dawo da amina, tunda shi yake aurenta ba wani ba. Yana zuwa fadar sai ya taradda takardar kira daga kungiyar kare ‘yancin dan adam, ana nemansa a ofishinta da yake a garin Sokoto akan tuhumarsa da laifukan dashi kan sa yasan ya aikata akan matarshi.

Abin mamaki, sai ga Abu ya rikice kwarai da gaske, yace “yanzu yallabai yaya za’ayi? Don Allah a taimaka a janye maganar nan.”

“Ai ba huruminmu ba ne, tuntuni abinda ake guje maka kenan, yanzu ina dadi ace har hukuma ta shiga maganar ma’aurata, zaman aure da ke bukatar sirri da girmamawa ” ya kara gyara zama, yace “amma yallabai ina ga baba liman ne ya kai maganar ga hukuma ko? don Allah a roke shi ya jaye idan Allah Ya yarda haka ba za ta kara faruwa ba.”

Hakimi yayi murmushi, cuke da takaicin Abu don ya san ba yau Abu direba ya fara fadin haka ba, ko lokacin da baya dukan amina ai yana dukan kuluwa. Kuma akan tauye ma iyalai hakki, an zauna dashi bayan auren amina lokuta da yawa, sai yace ya daina amma idan aka bincika saina taradda akasin haka.

Ya nisa yace “bani da wannan dama Abu, kuma ka sani ba liman ne ya kai rahoto ba, har nan aka zo aka same mu ni da shi.”

“Ranka ya dade ina neman alfarma, a rokar min ita amina idan anje can ta karyata haka, wallahi sharrin zuciya ne kuma ba tayi min biyayya, amma nayi alkawari……...”

“Ai bakin alkalami ya bushe Abu! yanzu ko ni nan Magana tafi karfina, ta fi karfin iyayenta, su din ma duk za’a nemo su.” A haka Abu ya koma gida jiki a sanyaye, ya kwana cikin fargaba da tunanin mafita.

Ranar da za a je ofishin human right, motar WH tazo har kofar gidan hakimin rariya aka dauki amina. Abu kuma ya roki iliya da kyar ya yarda akan zasu je tare. Sun isa ofishin, ya samu kanshi a gaban lauyoyi, ga amina matarshi, ga mahaifinta, da wasu mata guda biyu da suka yi mai kwarjini ya kara jin ya takura, musamman babbar a ciki mai sanye da gilashi. An tuhumeshi da laifin tauye ‘yancin matarshi yana yi mata gori har da na haihuwa, ga duka da zagi, aka kuma gabatarda kayan da take sanye dasu wadanda suka baci da jini lokacin da ya doke ta wanda ba shine na farko ba, ga fuskarta har a lokacin da alamun duka, kumburin lebenta bai karasa sauka da warkewa ba. Sannan kuma an fadi cewa mahaifinta ya aurar da ita ne a gareshi bisa ga dole alhali tsohon yaronshi ne yasan halayensa, kuma tun zuwanta gidanshi bata ji dadin zama da shi ba.

Bayan duka bayanai, Abu ya amsa laifukansa tare da bayar da hakuri. An saurari bayanai daga ko wane bangare, amina da mahaifinta suka dage akan lalle Abu ya sauwake mata ba zata iya zama dashi ba, karshe aka ce za’a mika maganar zuwa kotu, amma amina zata zauna a hannun kungiyar WH har a yanke hukunci.

Mahaifin amina ya kebe da ita tana kara yi ma sa bayani yadda Abubuwa suka faru, ta kare da cewa baba wallahi ba zan taba samun farin ciki ba idan ina tare da baban kasim, yanzu haka fa bani da lafiya na fada masa ya kai ni asibiti, amma sai yace ni ba haihuwa ba sai iya yi da dora ma mutane lalura. Kuma baba yaran nashi ma ba wani kula dasu ya keyi ba.” ya sa hannun rigarshi ya share hawaye da suka zubo  ba tare da ya iya tsayar dasu ba yace “kiyi hakuri amina, na gaza a wajen kulawa da rayuwarki, na kasa tallafa wa maraicinki, kuma ban cika burin mahaifiyarki ba.”

Dr asmau da barr sa’a da ke a gefe suna kula da amina da babanta suna magana suna sharer hawaye, sai suka karaso. Hajiya asmau ba ta iya kyalewa ba sai da ta kara tunatar dashi laifukansa, sannan suka ci gaba da fada ma sa yadda Abubuwa zasu kasance, kamar yadda suka fara kafin isowar Abu, sun kara fahimtar dashi tare da samun goyon bayanshi akan ceto da inganta rayuwar amina ta hanyar da zasu iya. Daga karshe su kayi sallama dashi, ya wuce garinsu dange, ita kuma amina aka ce ta shiga motar dr asmau za a wuce da ita kafin zuwan ranar da zasu shiga kotu.

Kallabi ko HulaWhere stories live. Discover now