6

540 122 14
                                    


Zaman Amina a Sokoto a karkashin kulawar maami asmau ta fahimci abubuwa da dama game da iyalan gidan a cikin 'yan kwanaki kafin a je kotu. Sau daya ta hadu da maigidan Alhaji Adamu Lema. A kamanni sak shine wanda taga fuskarshi a hoto ranar farko da ta shigo gidan. Bata kara ganinshi ba saboda ta fahimci ranar da ta hadu da shi, a ranar tafiya zai yi, ga dukan alama mai nisa ce tafiyar saboda taji an ambaci cewa zaya je Ghana. Mutum ne ba mai yawan Magana ba, a lokacin da mami ta gabatar da ita gareshi, bayan ta durkusa sai ya umurceta da ta zauna da kyau. Da aka yi mai bayani akan ta, yayi mata fatan alhairi tun daga nan bata kara haduwa da shi ba, sai dai ta kula da wuya mutum yayi zaman awa hudu da mami bai ji tana waya da shi ba.

A bangaren naana, ta fahimci cewa a hali kamar mahaifiyarta take wato son jama'a, saukin kai da karamci. Idan ta kalli naana sai taji a ranta kamar babu 'yar gata irinta. Ga ta da kyau, ga mahaifanta a raye, tana rayuwa cikin daula, babban abin birgewa kuma tana aji daya a jami'ar usmanu danfodiyo Sokoto, inda take karatun ilimin komfuta.

A cikin kwanukan bata cika ganin naana ba koda yaushe tana makaranta, sai idan ta dawo ne da marece ko dare take shigowa su gaisa tayi hira a dakin inna jummai cike da barkwanci. Wani lokaci ta ja amina zuwa wajen mami su gaisa da yake ita din ma tana wajen aiki da rana bata cika zama ba. Yanayin jikinsu daya naana da amina, dukansu lauka lauka ne babu jiki,. Shi yasa tufafin da naana ta kyautar ma ta guda uku su ka yi mata daidai a jiki. Rashin jikin naana ya sa ake ganin tana da tsayi, sai dai a hasken fata amina ta fi naana fari, naana kuma tafi ta gogewar fata duk da kasancewarta kalar chakulet, saboda yanayin rayuwa ba daya ba. komi na naana birge amina ya keyi.

Kullum safe sai an je da amina asibitin UDUTH da ke a garin Sokoto. Idan suka fita da wata ma'aikaciyar jinya ake hada ta, matron hauwa, wadda take tsammani kila kawa ko 'yaruwar mami ce. Daga nan mami zata wuce wajen aiki. Idan ta kare da asibiti sai direban ya mayar da ita unguwar arkilla inda zata zauna tare da inna jummai kafin sauran mutanen gidan su dawo. A rana ta farko bayan taga likita aka rubuta magani da allurai har da gwaje gwajen fitsari da jini. Abinda ya bata mamaki a gida maami asmau ke yi mata allura, a zuciyarta take tunani ashe da ake kiranta Dr. kenan likita ce? Rana ta biyu aka koma yin gwaje gwajen, washe gari aka amso sakamakon gwajin, sai likita ya kara rubuta wasu magunguna.

Da daren ranar maami ta aika kiranta, bayan ta zauna tace, "to amina maganar rashin lafiya, Alhamdulillah ke samu ganin kwararren likita kuma babu abin damuwa. Kina da lafiya baki dauke da wata cuta zaunanna, infection ne yake damunki kuma idan ki ka dage da abubuwan da aka fada miki za ki warke da yardarm Allah. Ga magunguna da aka kara rubutawa nan ciki har da na cusawa (inserting), duk zan nuna miki yadda za kiyi amfani dasu. Sannan ga panties nan sababbi zaki dinga amfani dasu, duk ranar da kika je gida kar ki kara amfani da naki dake can, ki kona duka...." Amina bata san lokacin da ta dago kai ta sa idanunta cikin na maami ba, saboda jin an ambaci GIDA, ba zuwa gida take fargaba ba, saboda ta san nan ajiya aka kawo ta kafin a yanke hukunci, amma ta dauka iyakar zamanta gidan abu direba kenan. Burinta, a raba ta dashi ta koma hannun mahaifinta ko da dadi ko babu.

Mami kamar ta fahimci abinda take tunani sai taci gaba da cewa, "kar ki yanke ma kan ki kowanne irin hukunci, zamu yi iya kokarinmu ganin an shawo kan matsalar da kike fuskanta, amma ki sani ita shari'a sabanin hankali ce, haka nan babu wanda ya san abinda zai faru gobe sai Allah. Ki dage da addua kamar yadda muka fada miki tun farko, mu kuma zamu taya ki neman zabin Allah."

Amina bata san lokacin da ta fara shesshekar kuka ba tana kokarin tayi godiya ga mami amma maganar bata fita kuka yaci karfinta. Sai da mami ta tsawatar sannan tayi shiru. Abu biyu suka sa tayi kuka, kukan farin ciki da na rashin sa, na farko jin ana yi mata Magana cikin aminci da gaskiya, wanda rabon da ta samu gata irin wannan daga uwa mace tun rasuwar mahaifiyarta a lokacin da take yarinya karama, sai ko wajen uncle Musa da MALAMA LUBA!

Abu na biyu kuma da yasa tayi kuka, tunani ta keyi cewa a kotu za a iya mayar da ita garin rariya gidan baban kasim! Wannan shi yake sa ta kara kuka. Amma zata bi shawarar mahaifinta da wannan managarciyar mace mai kula da lamarin maras galihu, a take anan tayi kudirin mika lamarinta ga Allah.

Ranar da za a shiga kotu, tun da amina tayi sallar asuba ba ta kara kwanciya ba. adduo'i take yi, wasu har ta manta rabonta da yinsu. Littafanta gaba daya suna can dakinta garin rariya, amma a daren jiya da naana ta shigo dakin inna jummai ta fahimci damuwar amina sai ta koma daki ta kawo mata littafan hisnul muslim, 4o Rabbana da wasu duka na addu'a masu dauke da rubutun larabci, turanci da hausa. Tace "Amina ga wannan ki dinga karantawa, sahihan adduo'i ne a ciki tare da fassara da bayaninsu, ai za ki iya karantawa ko?" Cikin doki ta amsa, ta karanta a nutse ko gargada babu, abinda ya sa naana jin dadi da kuma mamaki. Tayi murmushi tace "kina mamaki ko naana?" "a gaskiya tun da naga yadda kike amfani da waya da kuma bin wasu abubuwa a TV nasan keyi karatu ko yaya ne, amma ban dauka za ki iya karatu haka fluently ba." tace "ai ina SS2 aka cire ni daga makaranta aka yi min aure."

Inna jummai da ke saurarensu a lokacin ta amsa da cewa "Allah sarki, Allah Ya zaba miki abinda yafi zama alhairi." Naana tana so kwarai ta tambayi amina labarinta, amma ta tuna mami ta hana ta tambayar, ta fada mata za a je kotu ne akan mijinta yana dukanta, daga nan bata kara fada ma ta komi ba.

A kotu bayan kowa ya hallara, aka tsaya jiran wanda ake tuhuma da laifi wato Abu direba. Amina duk da murnar ganin babanta, amma tana fargaba kada Abu yaki zuwa. Fauziya sakatariyar su mami ce take ta kwantar mata da hankali, tana fada mata ai komi tsagerancin mutum dole ne ya amsa kiran hukuma. Ba a dade ana jira ba, kusan karfe goma sha daya na safe, sai ga abu ya iso tare da wani abokinshi kabiru. Ko kallon kirki bai yi ma malam umar da 'yan WH ba, haka aka kira su cikin chamber alkali, daga abu sai kabiru wanda ya gabatar a matsayin wakilinsa, ita kuma amina ta shiga ne tare da mahaifinta da barr. Saadatu. Alkali ya gabatar da jawabi cewa an zo nan ne ayi Magana saboda a samo mafita a tsakanin ma'auratan. Yace "zamu baku dama ku fadi ra'ayoyinku sannan zamu bari kuyi Magana da wakilanku kafin a hada ku biyu. Amma kafin nan, Abubakar Rariya zan fara da kai, ina so naji naka ra'ayi akan duka abubuwan da suka faru?"

Please, please idan an karanta a dinga voting da commenting... haka ne zaya sa masu rubutu su dinga jin karfin gwiwa.

Kallabi ko HulaWhere stories live. Discover now