Budar bakin abu sai yace "Allah Ya taimaki mai sharia, ni dai a nawa ra'ayin gaskiya ba zan iya kara zama da matar da ta kai ni kotu ba, wani mawaki da nake yawan sauraro a rediyo yana fadin, kowa ya kai ka alkali ai kasan bai raga maka ba. Don haka ni Abubakar Atiku Rariya na yanke igiyar aurena daya a tsakanina da amina taje ta auri wanda zai iya da kakalenta, Allah Ya hada kowa da rabonsa!"Shiru kadan ya biyo baya, amina da mahaifinta kowanne fuskarsa sai da ta bayyanar da farin ciki, kafin alkali yayi Magana cikin kakkausar murya "Abubakar rariya ka nutsu ka san cewa kana a gaban shari'a ne. Mun zo ne nan saboda ayi Magana cikin adalci da sulhu, ba tare da an tozarta kowane bangare ba, ba muzo wani zancen banza da soki burutsu ba. dukan mu nan musulmi ne, maganar mawaki ai ba maganar Allah da manzo ba ce. Matarka ba kara ta kawo ka ba, matsalolin da suke faruwa a tsakaninku suka zama cutarwa a gareta, zamanta mace mai rauni yasa wadanda hakki ya rataya a wuyansu suka kawo Magana anan. Ina so kada kayi gaggawar yanke hukunci ka nutsu kuyi Magana tukun."
Yace, "yallabai ina neman afuwa, amma iyakar gaskiya ta kenan, kada a ja maganar nan da nisa, na riga na sauwake mata saboda bata da godiyar Allah!" alkali ya waiwayo amina da mahaifinta, suka nuna amincewarsu akan hukuncin. Dan gajeren bayani ne ya biyo baya, inda malam umar ke rokon alkali akan ayi bayani a gaban duka bangarorin biyu, amina zata je nan da kwana biyu saboda ta dauko kayanta. An nemi abu ya rubuta takardar saki saboda shaida, sai yace kabiru abokinsa zai rubuta, amma alkali yace idan har ya iya rubutu da ko da ajami ko da haruffan boko to ya rubuta da hannunsa.
Bayan Alkali ya karanta rubutun da abu yayi da boko, ya tabbatar da abinda ya fadi shine ya rubuta a takarda, sai ya mika takardar sakin zuwa ga mal. Umar. Abu kafin ya fita sai da ya tsaya kallon amina cikin sakonni da basu wuce rabin minti ba saboda ya yarda da maganar da ake fadi cewa duk yadda mace bata son miji idan ya furta saki a gareta zata kasance cikin tashin hankali.
Amma abin mamaki a maimakon haka sai ya hango amina cike da walwala sai ma wani kyau da ta kara, a tunaninshi kila ko don ya kwana biyu bai gane taba, haka kuma ya ji gabanshi ya yanke ya fadi! Daga nan ya fita daga harabar kotu cikin gaggawa tare da kabiru dake take ma sa baya wanda kuma yana daya daga cikin masu zuga shi akan cewa amina ta ci zarafinshi tunda ta kai shi ga hukuma. Amina kuma tare da mal. Umar da barrister su ka fito daga kotu bayan alkali yayi bayanin da rubuce rubuce, tana cike da farin ciki da annashuwa.
Da kusan karfe biyar na ranar mal umar ne yazo har gidan Alh. Adamu lema kamar yadda su kayi Magana tun rana a ofishin mami akan zai zo ya tafi da amina. A gadinar gidan, mami ce tare da fauziyya da ta zo kawo sako daga ofis, sai inna jummai da naana da ke a tsaye tare da amina da ke kusa da kujerar da mahaifinta yake zaune yana fuskantar mami da fauziya. Naana da inna jummai duka sun nuna alhininsu akan rabuwa da amina, saboda sabon da su kayi da ita a 'yan tsirarun kwanaki da tayi a gidan.
Mami da ke zaune a gefe tana murmushi tace amma ai kun sani dole taje gida ko. Amina ina so ki nutsu ki bi duka sharudan idda da ta hau kan ki, kuma kici gaba da addua. Kuma duk lokacin da kike da matsala to kar kiji komi, kina da number ta haka ma ta barriester, sai ki kira muyi Magana. Naana dake a gefe ta matsa kusa da mami tace, mami ba zata kara dawowa bane? Sai a lokacin mal umar yayi Magana tun bayan gaisuwa da godiya da ya kara jaddadawa gun mami tun farkon zuwanshi. Yace kar kiji komi 'ya ta, Insha Allah idan t agama iddah zata dinga zuwa kuna gaisawa, ai an zama daya.
*********************A GARIN DANGE
Ranar da Amina ta iso garin da ya kasance mahaifarta wato garin dange dake kusa da garin sokoto, mal umar bai bari sun karasa gida ba sai da ta je gidan malama luba wadda take a matsayin uwa kuma babbar malamar addini, ta kara jin bayanin komi, anan ta jajanta akan maganar sakin auren da ya faru, ta kuma kara fadakar da amina akan iddah da ta hau kanta. A cikin watannin nan da amina take idda tana zaune a gidan mahaifinta, bata zuwa ko ina.
Bayan sun iso gidan mahaifinta mai dauke da sashe biyu, wato bangaren inna hadi kakarta da bangaren mahaifinta da matarsa Halima da suke kira mama lili. A sashen innar suka fara yada zango, kuma acan suka taradda mama lili wadda ta tarbe su hannu biyu.
Inna hadi ta kalli uba da diyarsa, sai tayi tsaki tace "Allah Ya wadaran naka ya lalace, wallahi na fara yarda da maganar mutane da ake fadin ka samu tabin hankali Babba (haka take kiransa). Yau ni naga abinda ya isheni, yanzu kai baka ji kunya ba, kaje ka kasha auren 'yar ka sannan ka sako ta a gaba dauke da jakar rashin mutunci wai ita ga mai gidan uba. To sai kizo mu zauna, idan yaso ya mayar dake ciki ya kara haifoki. Albasa ba tayi halin ruwa ba, mahaifiyarki har ranar barinta duniya bata da abokin gaba, amma ke ai mijin ki ya kira ya fada min baya fadi baki mayar masa ba, 'yar rainin wayo."
A daidai nan kannen amina Hassan da hussaini suka dawo daga islamiyya suka shigo da murna suna karadin ganin yayarsu. Abinda ya sa inna hadi tsagaitawa da fada ta fara korar amina da tagwayen akan su fita daga dakin. Sai kuma aka fara kiran sallar magariba, malam umar ya samu ya kubuce da sunan zai tafi masallaci.
Kwanakin da suka biyo baya, amina a gidan mahaifinta tana kokarin kiyaye duka shawarwarin da aka bata akan kasancewarta cikin iddah. Mama lili tana iya kokarinta wajen ganin ta kyautata mata, sai Hassan da hussaini da duk kwanan duniya murna su keyi ga yaya aminarsu a gida. Lokaci zuwa lokaci suna yawan gaisawa da Naana a waya, wani lokaci har su gaisa da mami idan tana gida tare da naana.
Uncle musa da ya samu labarin yadda abubuwa da suka faru, sai ya ce mata "ba zan zo ba meenah, kada zuwana ya sa ki samu matsala, ki bari muga matakin da babanki zaya dauka after your waiting period yadda kika fada min." Lokaci zuwa lokaci yana kiranta a waya ko ya aiko mata da katin waya, kamar ko yaushe.
Babbar matsalar da amina take fuskanta ita ce ta inna hadi, kowa ya shigo sai ta fara bayar da labari wai amina ta ki zaman aure, yaro dan arziki yana sonta amma babba ya goya mata baya an kasha aure. Tun amina tana yin shiru har ta fara tankawa.
YOU ARE READING
Kallabi ko Hula
General FictionA tsakanin Haihuwa zuwa Mutuwa, Mutum dan-adam ya kan rayu ne a bisa kaddararsa. Ingancin rayuwar mace ko namiji sun ta'allaka ne akan abubuwa da dama ciki har da iyalan da ya fito daga ciki wato iyaye, dangi - da kuma gidan aure. Aure babban abu n...