ASALIN AMINA Bingyel.Mahaifinta Malam Umar direban mota ne bahaushe dan asali kuma zaunanne a garin dange, karamar hukumar dange-shuni a jihar sokoto. Ubangida ne ga Abu direba. A lokacin da umaru yake kan ganiyar tukin mota, Abu rariya yaron motarsa ne. Mahaifiyarta kuma asalinta bafulatana ce amma kirista mai suna Saratu Ja'e. 'yar asalin wani gari da ake kira gidan zallah a jihar zamfara amma mazauna cikin garin gusau a unguwar gada biyu, a gidansu dake gusau, saratu ce da kanenta daya mai suna musa, sai mahaifanta.
Malam umaru ya hadu da saratu a sanadiyar sana'arsa ta tukin mota a tsakanin jihohin arewacin najeriya. A shagon da take zuwa kai chinchin da alawar madara da su ke yi ita da mamanta a shagunan titin babbar asibiti anan suka hadu, shi kuma a kusa da shagon yake zuwa cin abinci wajen madam Risi.
Umaru ya so saratu kwarai da gaske, irin soyayyar da babu ruwanta da bambancin yare, asali ko addini, kuma ya samu martanin soyayya daga gareta amma mahaifanshi da nata babu wanda ya amince saboda bambancin addini da kuma kabilanci.
Ko da su ka fara kula juna, ana kan surutun ya fito da matar aure, shekarunsa a lokacin sun kai talatin. Sun fuskanci kalubale kwarai da gaske, saboda ko baya ga bambancin addini, manyan mutane ke neman saratu a cikin musulmi da kiristoci.
Saratu Ja'e, kyakkyawa ce ta bugawa a jarida, irin kyau mai daukar hankali da tafiya da zuciyar maza!. Bayan kasancewarta mai hasken fata sosai, tana da diri da gashin kai mai tsayi da santsi irin na Fulanin asali. Idan ka ga saratu zaka dauka yar Pakistani ce, komai ya ji a jikinta Masha Allah, duk da kwalliya bata dameta ba sai dai tsafta. Kawayenta da yawa musulmai ne, tun bata san ciwon kanta ba da kyar ake samu ta je choci, a lokacin bata ma san abinda yasa bata son zuwa choci ba. Ga mahaifanta suna riko da addinin yesu almasihu sosai, abinda ke rage mata farin jini kenan a cikin jama'ar gari da suke musulmi.
Mahaifinta baya so ta auri musulmi, daga baya ya sauko cewa zai iya bari ta auri musulmi ne kawai idan ya kasance bafillatani kuma mai sana'ar kirki a cewarsa ba wai direban kasuwa ba mai ilimin sakandire. Ita kuma ta kafe sai umaru dange, wasu har dauka su keyi ko asiri yayi ma ta. Ko an hana ta fita sai ta san yadda tayi suka hadu in har yana garin gusau. A na shi bangaren idan ya je lodin mota daga sakkwato, har canje yake da abokan sana'arsa saboda kawai yazo gusau yaga saratu hasken ran sa. Daga karshe mahaifan saratu su kayi mata korar kare saboda a zatonsu hakan zaya sa ta rabu da umaru direba, sun kara hasala ne akan taki yarda da auren wani kirista da yake zaune a kano mai kudin gaske, kuma yana masifar sonta, har mota starlet (a lokacin ita matasa ke yayi) ya ba mahaifinta kyauta, duka a lokacin shekarunta sha takwas kuma ta kammala sakandiren a nan gusau.
Da taimakon kanenta musa da wani makwafcinsu usman ta samu kudin abinci da wajen kwana har kwana hudu kafin umaru ya zo gusau (a lokacin babu wayar tafi da gidanka). Ranar da umaru ya iso gusau, ya fara aikawa ya fada ma saratu yana shigowa unguwarsu inda yasan zasu hadu a boye, amma sai ya samu mummunan labari daga bakin abu yaron motarsa da ya aika cewa an kori saratu daga gida saboda shi. Bai tsaya bata lokaci ba kawai ya tunkari gidansu saratu a cikin mota. baban saratu mai suna ja'e yasa aka fasa gilashin motar umaru, sannan ya ci masa mutunci sosai. Mazauna unguwarne suka shiga tsakani a kayi ta zuga umaru akan ya kai ja'e wajen hukuma amma sai ya bige da bayar da hakuri ga ja'e wanda yake ta famar zaginsa.
Da dare bayan ya kai motarsa wajen gyara ne musa tare da usman suka zo suka fada mai halin da ake ciki game da wajen da suka kai saratu. Jikinsa yana rawa suka rankaya har gidan risi mai abinci inda saratu ta ke boye kwana da kwanaki. Anan ya zauna a kayi shawara da ita saratu da usman da musa cewa zai tafi da ita ta zauna a sakkwato kafin ya shawo kan iyayensa. Saratu da bakinta tayi alkawari za ta amshi musulunci daga nan suyi aure. Musa yana kuka yace, 'amma dole sai ke shiga musulunci sarah? Na ji ana fadi cewa mace kirista zata iya auren musulmi.' Usman yayi ta kokarin fahimtar da musa cewa wannan ra'ayinta ne, amma musa a lokacin shi yana taimakon 'yaruwarsa ne saboda yadda yake son farin cikinta, yasan umaru take so, amma baya so ta karbi musulunci, a tunaninsa idan tayi zamanta a kirista wata rana ja'e babansu da mahaifiyarsu churi zasu amshe ta tunda ita kadaice 'yarsu, sai shi kanenta.
A bangaren umaru kuwa, cike yake da zullumin abinda zai je ya tarar a garin dange wajen mahaifiyarsa inna hadi. Yana sane da cewa har ta fara nemar masa aure na wata yarinya luba da ta fara karatun sakandire zuwa aji hudu, kuma iyayenta sun ce in dai umaru mai mota ne zasu cire ta daga makaranta su aura ma sa. A tunanin inna kila yar boko yake so shi yasa ya like wa kafira kamar yadda take kiran saratu. Tunani ya keyi yaya zai yi da inna? Ya sani cewa ya dauko dala babu gammo, saboda innarsa bata son zancen saratu sam! ta fada ta maimaita kada ya kuskura ya watsa musu kasa a ido yace shi ba zai auri lubabatu ba.
A garin sokoto suka yada zango, umaru bai kai saratu ko ina ba sai gidan malam isah talatar mafara, sananne kuma babban malami da yake da gida a unguwar lowcost housing, gida mai hade da islamiyya da masallaci. Umaru ya san malam isah saboda yayi daukar karatu a wajen malamin kafin hidimomin rayuwa su dauke ma sa hankali, kuma duk juma'a in dai ya shigo sokoto yana zuwa ya kai gaisuwa ga malam. Tun watannin baya malam yasan komi a game da labarin saratu da umaru, amma abinda ya sani ita ahlul kitabi ce umaru yake so ya aura ba yada masaniya akan sauran matsalolin ba. Ranar da suka iso da yamma ne, malam ya samu labarin saratu zata shiga musulunci, anan take ya bata Kalmar shahada (wanda dama ta hardace) kuma ya hada ta da iyalinsa aka fara nuna mata harkokin wanka, tsarki, niyya da wasu wajibai (Fard ayn) da ya kamata mutum musulmi ya kiyaye. Da amincewar umaru aka yanke cewa za ta zauna gidan malam.
Bayan watanni shida aka daura auren umaru mamman dange da saratu ja'e farkon shekarar 1989 akan sadaki mai kauri wanda wani alhaji dalibin malam ya biya saboda murnar shigar saratu addinin musunci. Inna hadi bata so auren ba sam, haka ma 'yan uwansa da suka riga suka hakikance akan cewa kafira zaya aura. An kai ruwa rana anyi tashin hankali sosai lafin a samu a daura auren. Har sai da malam yazo da kanshi yayi tattaki har zuwa garin dange yayi ta nasihohi aka hada da wasu dattijai daga baya tace aje ayi amma nan gaba dole yayi wani aure. Saboda ta samu tsarkakkun jikoki masu asalin kwarai a cewarta, saboda umaru shine kadai dan ta namiji, sauran duka mata ne.
YOU ARE READING
Kallabi ko Hula
General FictionA tsakanin Haihuwa zuwa Mutuwa, Mutum dan-adam ya kan rayu ne a bisa kaddararsa. Ingancin rayuwar mace ko namiji sun ta'allaka ne akan abubuwa da dama ciki har da iyalan da ya fito daga ciki wato iyaye, dangi - da kuma gidan aure. Aure babban abu n...