10

500 63 2
                                    


   SOKOTO, JANUARY 1989.

Mota ce kirar Peugeot tayi parking a a harabar wani gida, a wani gida, titin clapperton, gidajen da ke unguwar gawon nama. Yaro ne dan shekara takwas ya fito daga bangaren mai zaman banza, yana saye da kayan makaranta na FGC Staff School. Daga bangaren direba kuma wani matashi  dan shekaru ashirin da biyar, shi kuma kayan ‘yan bautar kasar Nigeria ne a jikinshi wato NYSC.

Saurayin ya kama hannun yaron suka shiga gidan ta kofar baya tare da sallama, a kicin suka samu matar gidan tana kokarin kammala girkin rana tare da taimakon yarinya mai aiki farida. Mace ce matashiya ‘yar shekaru ashirin da takwas a duniya, tana da matsakaicin jiki da manyan idanu, kalar jikinta wankan tarwada.

Matashin ya gaisheta, ta amsa da cewa “Abba, har kun dawo, ashe lokaci ya tafi ban sani ba” yaron yace “mami sannu da aiki” tace sannu imam. Kun rubuta jarabawar? Ya amsa mata da kai, alamar eh, a lokacin da yake kokarin tattare safar da ya cire daga kafarsa, daga nan ya wuce dauke da jakar makaranta zuwa daki. Mami  bayan ta rage wutar murhun na lantarki, sai suka wuce zuwa cikin palon gidan tare da abba.

A palo suna cin abinci dukansu, bayan imam ya sauya kayan makaranta da na zaman gida, sai imam ya kalli mahaifiyarshi yace, “mami babu islamiyya yau?” tace “haka ne imam.” Sai ya mayar da hankalinsa zuwa ga abba yace, “abba zaka je dani kallon ball?” kafin abba ya amsa sai tace, “yau hakuri za kayi imam. Daga munyi sallar azahar Fita za muyi da abba.” “to mami ni zan tafi tare da ku tunda daddy baya nan.””no, kasuwa za muje da abba, za ka zauna gidansu Abdul tare da farida har mu dawo.”

Duk da yana so ya zauna gidansu Abdul din, amma yaso ya bata rai ganin ba za’aje dashi ba, sai abba yace, kasuwa za muje imam, me kake so a sawo maka.” Abinka da yaro sai kuma yayi murmushi yace school bag nake so da colour pencil ni da abdul.” Ya ba shi hannu ya ce “consider it done Ali boy!” Mami da take jin su tayi murmushi, a ranta, tace “abba kenan da imamunsa”

Sai kusan karfe biyar suka dawo gida dauke da kaya niki-niki, mami ta fada daki a gaggauce saboda ba tayi sallar la’asar ba, yayin da abba ya wuce dakinsa da yake a baskwata na gidan. Bayan ta idar da sallah ta dauki kayan da suka zo dasu da taimakon farida zuwa dakin da ta ajiye sauran kayan, a dakin mami ta zauna ta sauko da akwatuna sababbi fil cikin leda, kwara biyar da kit daga gefen kwabar ajiye kayan sawa dake dakin, sannan ta bude kwabar ta fito da kaya tana saukewa akan gado, laces ne sai atampopi, materials da shaddodi masu yawa da dan Karen kyau sai mayafai da undies. Ga kuma takalma da jakunkuna kala kala, masu tsayin dunduniya da marasa dunduniya duka girma (size) iri daya.

Ta fito da kayayyakin da suka sawo yau wato kayan shafe shafe na mata da turaruka da kayan karau na ado. Haka tayi ta shirya kayan a cikin setin akwatunan,. Tafi awa daya tana shirin kayan sai da ta kammala saka ko wane a cikin akwatin daya dace sannan ta tsaya ta diba, tana tunani tare da zancen zuci “kayan bacci suka rage, sai hand bags biyu da za a kara.” tayi murmushi mai nuna farin ciki, ta fadi a fili “Alhamdulillah, Allah nagode, abba na zai yi aure.” Ta share hawayen da suka zubo mata alhali murmushi ne akan fuskarta. Sai ta fita bayan ta jawo kofar dakin.

A palo taji wayar gidan tana sauti alamar kira, ta dauki kan wayar sai taji muryar maigidanta yana sallama “wa alaikassalam, yallabai yaya seminar” a daya bangaren aka amsa, “yau mu ka kamala Ma’u, amma ina ga sai zuwa Sunday zan dawo, yaya kowa da komi, gaskiya nayi kewarku ma’u na.” Tace “Allah Ya kai mu sunday, amma me zaka tsaya yi a lagos har nan da kwanaki hudu?”

“Maganar shigo da kayan nan ta kammala, Bello za ya zo gobe, sai mun tabbatar komi ya zama ready daga nan zuwa asabar Insha Allah, idan yaso sai mu juyo tare. A taya mu da addua.” “Addua kullum mu nayi sai dai a kara. Kuma ina so na kara godiya akan duka shirye shiryen auren abba, Allah Ya biya ka Ya kara budi.” Yace maman imam wai har yau godiyar ta baki bata isa ba, ai ina ce sai na dawo a yi min ta zahiri ta musamman.”  Dariya kawai tayi, yasan ba zata ce komi ba, a ransa yace Ma"u sarkin kunya! Aurensu shekaru goma kenan, amma har yau ma’u tana da kunyar fadin wata Magana a fili.

“Wato ba godiyar za kiyi da gaske ba kenan, ai waccan da ki keyi ta zama outdated idan na dawo za kiyi min ta gasken.” Tace to Allah Ya nuna mana.” “Wai ina imam ne, ko yana tare da abbansa?” tace “imam yana can gidansu abdul, anjima abba zai dauko shi.” Bayan sun yi sallama da maigidanta, ta gyara zama akan kujera tana tunanin irin gudummawar da yake bata a rayuwa, ya tallafi maraicinta har da na danuwanta, ya ba ta dama tare da jajircewa akan ganin ta ci gaba da karatu a makarantar aikin jinya inda ta karanta nursing & midwifery”, har gata yau ta zama cikakkiyar ma'aikaciya a asibitin kwarraru dauke da ke a garin Sokoto. Tayi nisa a tunani, sai taji ana kiran sallar magrib. Ta mike don gabatar da sallah.

Kallabi ko HulaWhere stories live. Discover now