®Fikrah Writers Association🖊
©Jeedderh Lawals
'Where are you now?
Atlantis: Under the sea
Under the sea
Where are you now?
Another dream
The monster's running wild inside of me...
I'm faded... So lost.... Am faded...!'.
Alan Walker FadedSeoul-South Korea
Tun karfe takwas na safiyar ranar yake cikin meeting da wasu manyan shareholders da suke kokarin hada gwiwa waje guda domin bude kamfanin saka rigunan sanyi anan Seoul. Bayan fitar shi daga wancan meeting din, wani ya shiga. A takaice ranar sai karfe biyar da rabi ya gama meetings dinshi. Daga nan restaurant ya wuce, yayi brunch? Dinner? Bai sani ba. Saboda tun da garin Allah na ranar ya waye, babu abinda ya shiga cikinshi sai ruwan lemu daya sha a wajen meeting.
Karfe takwas na dare ya tura kofar suite dinshi dake cikin hotel din GK. Wanka yayi da ruwa mai dumi domin ya warware gajiyar data lullube jikinshi. Ba laifi yaji dadi a jikinshi. Yasa rigar barci sakar Marks and Spencer's yabi jikinshi da turare mai sanyin kamshi. Kai tsaye lafiyar gadonshi yabi, babu abinda yake bukata a lokacin irin barci. Kafin barcin yaci karfinshi Aysha ta fado mishi a rai; ko ya take ita da babyn shi? He made a mental note akan ya kira ta washegari da safe.
Bayan dogayen awowi na twisting da canza sleeping position kamar sau hamsin, Moustapha ya hakura da barcin shi. Tsam ya mike zaune idanunshi kafe akan agogo, karfe goma ce da rabi. Yasan can Nigeria dare ne yanzu, kila sunyi barci don haka bai gwada kiran kowa ba.
Kan wayoyinshi ya dauko ya bude, a nutse yake bin ko wani sako, email ko kira yana maida amsa. Abin ya bashi mamaki da yaga tarin missed calls din bakuwar number a personal phone dinshi. Voicemail da aka bari ya bude.
“Assalamu Alaikum wa rahmatullah...!!”
Ita kadai yaji, amma sai data sa duniyar shi yin sama-sama ta dawo kasa ta baje, ta tarwatse. But it can't be, why on earth Sheerah zata kira shi? Me ya kaita Nigeria?? Bashi da amsar tambayoyinshi don haka ya sake kunna wayar.
"... Ni doctor din dake kula da matar ka ce.., Look, ban san abinda ya hana ka zuwa ba and I wouldn't judge you. But muna bukatar sa hannunka akan aikin da zamu mata. So please and please idan zaka iya zuwa koda na rana daya ne, sign the papers and go your own way again. But let me tell you, kana wasa da damar ka. Har kullum mai gida na kwarai yana ajiye family dinshi ne as his first priority, kome zai faru suna kan gaba. Kada ka bari abin duniya ya hana ka kula da iyalanka, zaka yi dana sani. Ma'assalam!".
Bai san lokacin da tattausar dariya ta subuce daga bakinshi ba, ance wai dama mai hali baya canza halinshi. She's still the same, full of confidence and kindness. Wayar shi ya dauka ya dannawa PA dinshi kira. Bai damu da cewa karfe dayan dare da mintuna a sama bane, abinda ya sani kawai shine yana bukatar ya ganshi ya wayi gari a Nigeria kawai. Tambayar shi daya, me ya kai Sheerah Nigeria? Da wannan tambayar ya kwana a cikin ranshi, voicemail din Sheerah yana replaying a wayar shi over and over.
Bai samu jirgin da zai wuce Nigeria kai tsaye ba daga Seoul. Haka ya hau na yawo, bayan doguwar tafiya, zaman jira a jirgi, tortured awowi cike da longing, finally jirginsu ya sauka a Kano. Kai tsaye asibitin da aka kwantar da matarshi Aysha ya yiwa dirar mikiya, ba don ita ba, sai don mutum daya zuwa biyu.. And there they are...!
☆☆☆☆☆☆
Sheerah ta kurawa Moustapha idanu flabbergasted, gabadaya ta rasa abinda ya kamata ta tunana. Can wani abu yayi snapping a cikin kanta, take tayi regaining composure dinta. Ta kai yatsa daya ta dauke siririyar kwallar data gangara kan kumatunta, ta saki tattausan murmushi a nutse tace "oh Moustapha! Banyi tsammanin ganinka anan wajen ba. Me kake yi?".
YOU ARE READING
Doctor Sheerah! (SAMPLE ONLY)
SpiritualRayuwarta, farincikinta, damuwarta, tashin hankalinta, komi nata ya ta'allaka ga mutanen nan su biyu ne kacal! Su kadai take kallo taci gaba da rayuwa kamar babu wata damuwa a ranta, her world revolves around them!! Me zai faru lokacin da abubuwa s...