abokina ne

477 14 0
                                    

Eesha dake tsaye a cikin airport misalin karfe 9:30am na safe tana jiran driver wacce mahaifin ta ya rasu sanadiyyar hatsarin motar dayayi a hanyarsa ta dawowa daga kasar london wajen habbaka kasuwancinsa tsakanin airport da gidansu,hakan yasa mahaifiyarta bayan tagama idda takoma kasarsu wato kasar turkiyya inda mahaifin isha ya ganta yayin da yaje karatun sa na masters ya kuma aure ta bayan yarjewar iyayensu .A yanzu kam isha ta kammala karatunta na gaba dadigree hakan yasa ta dawo nigeria damin ta zauna tare da dangin mahaifinta
Bayan wayan su yan mintina driver daga gidan alhaji muhd bashir jiddah wanda aka fi sani da MB JIDDAH wato kakansu esha yakaraso , bayan sun gaisa ya dauki akwatin kayanta yasakasu cikin bayan mota kafin su dauki hanyarsu zuwa MB JIDDAH RESIDENT wandayake a unguwar racecourse . da shigarsu gate na farko dake cikin gidan wanda suke a kan kwaltar da suka hau tundaga kwanar gidan wanda zata isar dasu bangaren wan mahaifinta wanda ya zabi ya rike ta tare da yayansa gaba daya . su goggone da kawu da kuma sauran mutanen gidan ne ke tsaye suna jiran motar data dauko esha tayi parking , Gida ne kato wanda aka kera shi cikin sanin ciwon naira,gida ne mai bangare bangare wanda aka. zageyeshi da abubuwan kawata rayuwa kamar lambu, swimming fool, furanni, da kuma wajen ibada wato masallaci . sakkowa tayi daga cikin motar cikin nutsuwa cike da farinciki da annushuwa tare da zare bakin shades din ta maitsada dake kan idonta , ajiyar numfashi tayi sannan tayi murmushi ta gaishe da mutanen gidan tare da rungume su " hakika nayi kewarku sosai nayan shekarun danayi ba tare da ku ba" "muma munyi kewar ki sosai daga ke har mahaifiyarki dafatan tana cikin koshin lafiya" " tana nan lafiya goggo kuma tace na gaisar mata daku sosai sosai" " to muna amsawa , yanzu dai yakamata kije ki watsa ruwa ki kwanta ki huta kinji , malam musa sai ka karasa mata da kayan ciki ko" goggo tafada . cikin gajiya eesha ta nufi babbar kofar shiga bangaren abba kabir wan mahaifinta wato abba saleh . kafar bene ta nufa inda dakinta yake, da shigar ta fada bandaki ta watsa ruwa sannan tafito ta sauya kayan jikinta zuwa marasa nauyi sannan ta fada kan gado ta kwanta.
Hakika isha yarinyace mai kimanin shekaru 20 mai ladabi da biyayyah wacce Allah ya halicci suffofin kyau wadda duk wata ya mace take burin mallakarsu, yarinya ce mai haske wadda baza a kirata fara ko baka ba wacce fatar jikinta da manyan idanunta da kuma dan kara min bakin da Allah yayi mata ga dogon hancin da ya nutsu a kan fuskarta tare da zarazaran gashin ido dana gira ga bakin dogon lallausan gashin kai with her twin dimples involved, dadin dadawa yarinyace mai addini da tsoran Allah wadda bata damu da abinda mutane zasu fada akan taba ga cikakken diri son kowa kin wanda ya rasa.
Hakika ta shaku da yanuwanta duk da cewa ita kadai Allah ya albarkaci iyayenta da su wato yayan kannen babanta da kuma yayyensa.
Esha dake kwance akan gadonta ce tayi juyi sannan ta bude idanunta,mike wa tayi tare da nufar inda kayen ta ke ajiye ta canza kaya sannan ta nufi kafar bene inda ta tarar da areef wanda yake a zaune kan wata zagayayyiyar lallausar kujerar (sofa) da akayiyo order ta daga dubai duk dama cewa yawancin kayan alatun gidan bana kasarnan bane yana danne danne a cikin laptop dinsa sanye da head phone a kunnen sa. zama tayi cikin nutsuwa tunda ta fahimci Areef bai san tana kusa dashiba sannan ta zare head phone din dake kunnensa ta kuma saka a kunnente "waka mai dadi" tafada cikin zazzakar muryar ta ,da sauri anwar ya jiyo ya kalle ta sannan yayi ihu tare da yunkurin rungumeta, sauri tayi ta rike hannayensa tare da fadin " dakata ! dakata ! me kake kokarin yi haka? Ashe har yanzu baka canza ba kananan da halinka koh? Ko duk murnar saduwar da muka yine bayan wadansu lokuta masu tsayi domin kuwa nayi kewar abokina sosai" "dagaske shi yasa kika dakatar dashi daga rungume ki koh " " Allah sarki abokina bahaka bane amma idan kaji haushi Allah ya huci zuciyar ka , yanzu ka iya rungume ni" ta fada sannan suka rungume juna cikin farinciki "nayi kewar aminiyata sosai da sosai amma yanzu ta dawo ai dole ma muyi shagalin murna" " nima nayi kewar abokina sosai kamar yadda nayi kewar mahaifina wanda ya damu dani sosai" tafada tare da hawayen dake kokarin zubowa daga idanunta " haba Esha ai zaki bata wannan kyayyawar kwalliyar da kika yi wadda take birge kowa da kowa" ya fada tare da goge hawayen dake kokarin zubowa daga idanunta, rike hannunsa tayi wanda ya kwanta akan kumatunta tare da fadin " na goda Areef dina Allah ya barmu tare " "ameen" " wai ina su anti laila ne tunda safe da muka hadu ban sa ke jin motsin su ba" " suna dakinsu watakila " " toh bari naje" ta fada sannan ta nufi kafar bene inda ta shige dakin anti laila ta kuma tarar da samira wacce suke tare suna hira "oh my girls, i really miss you guys " " bake kadai bama dukkan mu munyi kewarki musamman ma idan muka ga bakowa a bangaren gidanku, ke dai bari" sai dai hakan ya tunawa Eesha rayuwarta da mahaifinta da sauri anti laila ta danguri samira alamar tayi kuskure , samirah ce ta bude bakinta cike da danasanin kuskuren data yi "eyyah ya eesha i'm very very sorry for my comment dear" "a'a karki damu everything is ok kawai dai na tuna lokacin da nake tare da abba cikin farinciki neh" tafada sannan suka cigaba da hira eesha na basu labarin kasar turkey.
Da safe misalin karfe 8:58am lokacin eesha na kwance akan gadonta lillibe da bargo a lokacin da tayi juyi sannan ta bude idanunta , zame kanta tayi daga cikin bargon sannan ta fada bandaki ta kunna shower tayi wanka sannan ta zauna a kan kujerar dake gaban mudubinta ta fara taje dogon lallausan gashinta .a daidai wannan lokacin ne areef ya kwankwaso kofar dakin azatonta su samira ne hakan yasa ta cigaba da tazar kanta ,muryar areef taji yana yi mata magana a lokacin da tayi sauri ta mike. Tana sanye da short towel wanda bai wuce cinyar taba da sauri areef ya juya tare da rufe idanunsa "muna jiranki a dinning for breakfast" yafada sannan ya fice , ajiyar numfashi tayi sannan tayi maxa ta saka kayanta a white sleeveless dress with pleatings on it and a denim jacket with an appearing of bun hair style .Da sauri ta koma kan stool din ta ta dauko makeup kit dinta and as usuall she applied a light makeup ta kuma fesa arabian perfume dinta wanda anti laila ta kawo mata daga egypt wadda bata dade da dawowa daga egypt ba in da tayi karatun digree din ta as she hurriedly put on flats wacce bata fiya son wedge shoes ba. Da fito war ta ta nufi dakin umma maman su areef ta gaisheta lokacin abba kabir ya dade da fita zuwa company dinsa na textile materials. Cikin nutsuwa ta sakko daga bene inda ta tarar da kowa ya riga ya hallara ita kadai suke jira "goog morning guys" tafada sannan ta janyo dinning sit ta zauna,Areef dake zaune a gefen tane ya matso kusa da kunnen ta sannan yace " nice scent, na dade ban ji irin wannan kamshin a rayuwata ba" "kada ka damu idan kayi aure da kanka zaka din ga siyo wa matar ka irin wadannan turarukan" fada tayi sannan ta janyo tea cup dinta with a slice of sandwith sannan ta fara ci a lokacin da samira ta tofa albarkacin bakin ta itama "ya eesha kin yi matukar kyau sosai " "sosai ma amma ni hair style dinta yafi burgeni " anti laila ta fada" "thanks all" ta fada sannan ta cigaba da breakfast dinta .
Da yamma misalin karfe 3:20pm
su eesha na zaune a babban falon dake kasa suna hira lokacin umma tafita zuwa wajen aikin ta hospital dayeke ita babbar likita ce wadda ta karanci bangaren gyneacology ." anwar ya maganar company din ku kuwa hope everything is going well"" yeah komai na tafiya daidai" yafada dayake MB jiddah ba mai son family din sa suyi aiki under government bane yafi son mutum yayi aikin da zai laru da kansa hakan yasa yakan bawa wadansu daga cikin jikokinsa wayanda suka mallaki hankulansu companies din da zasu iya daukar nauyin kansu dayake shi mutum ne mai tarin dukiyar gaske wanda yake aiki da companies din kasashen katare duk da cewa yana da wayen wajajen gudanar da kasuwancin sa anan gida Nigeria,yana da bakuna,gidajen mai da kuma stores banda sauran companunuwan dayake dasu da kuma gidaje.
Da daddare eesha na daki ita dasu samira tana shisshirya kayanta tana kuma fito da tsarabar da kawo wa yan gida "anti laila wannan nakine turare ne na siyo miki nasan kuma zaki soshi sosai" "kaaii amma fah na gode sis" "wannan kuma doguwar riga ce da stilleto shoe naki ne samira saboda nasan kina son hill shoes, sai kuma wannan agogon na areef neh musamman na siyo don shi ,wayannan ragowin turarukan ku nasauran mutanen gidan ne samira sai ki bama kowa nasa" tafada sannan ta cigaba da jera kayanta cikin wor drobe din ta "ya isha amma fah wayannan english wears din naki da dogayen rigunannan naki da wayennan shoes din naki sun tafi dani ,ke kam baki son saka kayan gargajiya tunda kika bar kasarnan" " hmm kar ki damu kwanannan zan koma gargajiya amma fah bazan iya rabuwa da saka english wears din ba" "toh ai shikenan ya eesha ,ba yadda zamuyi dake. Ni zanje na kwanta sai da safe" " ka tsaya mu tafi tare nima baccin nake ji, eesha sai da safe" anti laila ta fada tana saukowa daga kan gadon isha " "au duk tafiya zakuyi , toh have a nice dreams" " and you" samira tafada sannan suka wuce dakunansu . Ajiyar numfashi eesha tayi sannan ta fada bandaki tayi alwala ta fito tayi shafa'i da wuthri dinta ta dan yi karatun Alqur'ani sannan ta dauko system dinta ta fara danne danne .
AREEF POV
Da safe Areef na tashi ya fada toilet yayi wanka sannan ya fito ya saka kayansa light blue lightening shadda in colour, his traditional light blue and white cap, his black polished shoe was not left unnoticed, bude akwatin wristwatches din sa yayi looking for a mathching one alokacin da eesha tayi knocking kofar ta shiga " argh! kada kabatawa kan ka lokaci wajen neman wristwatch din da zai yi matching da kayanka,wannan black din shi zai dace da kayan ka ka gane? " ta fada sannan ta janyo hannunsa ta daura masa agogon"dubi yadda yayi maka kyau abokina yadda yayi maka das kamar wani dan secondary school". Anwar saurayine mai kimanin shekaru 25 wanda ya kammala karatunsa na masters a kasar Malaysia , saurayi ne fari dogo, yana da dogon hanci ga dimples din dasuke a kan fuskarsa koda kuwa bai yi dariya ba , yana da bakar cikakkiyar gira da kuma saje wanda ya hade da kwantaccen gashin gemunsa , yana madaidaitan idanu da kuma dan karamin baki (pink lips) shi ne babban abokin Eesha kuma dan uwanta na jini wanda bata boye masa surrikanta. Sun taso tare ne tun suna yara duk da cewa ya ya bata yan wayansu shekaru, mutum ne me son zaulaya da wasa wanda yakasance bafulatanine ta bangaren mahaifinsa wayanda suka zo daga jihar yola na garin adamawa , "kasan me abokina kayi matukar yin kyau sai dai matsalar abu daya neh" "what? " "wannan!" Tafada sannan ta dago turaren dake ajiye akan mudubinsa sannan ta fesa masa tare da dora hannunsa bisa kafadarsa" da alama za ka je zance koh? Toh bari na kyale ka kayi shiri sosai domin kuwa bana so akira yaya na kazami" tafada tare da yin wani dan murmushi wanda ya fito da dimples da sukan kara mata yayin da tayi murmushi. Areef ne ya bita da kallo yayin data fice daga daga dakin yana rike da kugunsa lokacin data jiyo da sauri kada ka manta idan kaje ka gaisar min da ita ,daga gira yayi alamar (dagaske!) Sannan ta harareshi " kaai kadena yimin irin wannan murmushin ni ba ita bace" tafada sannan ta fice , shi kam murmushi yayi sannan ya gigiza kai " su chalenger an dawo sai abida hali yayi" ya fada yana gyara hular dake kansa wanda tayi cas akan bakin kwantaccen gashin da yake tarawa irin na fulanin asali.
Easha ke tsaye da ita da su samira suna tsunkar furanni lokacin da Anwar ya shigo cikin murmushi ta juyo ta kalle shi amma ta fahimci irin kallon da yake yi mata yadda tayi parking din gashinta da kuma sajen daya kwanta a gaban goshinta ga short-sleeve shirt da kuma wando pela dake jikinta wanda ya kara nuna matsayinta a cikin mata amma hakan bai hana ta daura jacket a kan kuguntaba wanda ya kara mutunta shigar da tayi. " har ka dawo daga zancen ne?" " ke dai kin dame ni akan wannan batun, toh idan kuma kece future wife din fah" " hakan bazai faru bama, ba wannan bama me ka kawo mana neh cikin wannan ledar dake hannunka. Kaai nima dai na fiya shisshigi dayawa anyway shike nan dai " " kin san me na kawo miki kuwa ? Abin da kika fi kauna " "meye wannan, abinda nafi kauna?" ta fada cike da mamaki" " uhm toh watakila smoothy" " oh my G ! Wannan shine abinda ka siyo min amma na gode sosai gillor ashe dai kana sona " tafada tare da jan kumatun sa."towo wariyar launin fata za ayi min kenan, in banda haka to ina nawa" " kar ki damu yar auta ga naki nan cikin leda " samira ta fada sannan suka kwashe da dariya.
Eesha ke zaune a babban falon dake kasa kafin ta tashi ta nufi dakinta , shiga tayi sannan ta durkusa gaban durowar don daukar agogon data siyo wa areef daga Turkey lokacin da wayarta tayi ringing,zura hannunta tayi cikin aljihunta ta zaro wayar sannan ta duba - wata kawartace da sukayi secondary school tare daga wa tayi sannan tace" hello sarah, kina lfy?" " lfy qalau MBJ, ya kasar tamu " "lfy sarah ina nan tare da yanuwana yasu momma?" "Lfy qalau ina surikinnamu? " " hmm aboki ne kawai,duk wata ya mace tana da male frnd wanda duniya suke daukar sa amatsayi na daban" ta fada tana rufe drowar sanannan ta nufi babban falo inda ta tsaya a gaban babban mirror din dake falon sannan ta cigaba da wayar ta, areef ne ya nufi inda take a tsaya sannan ya tsaya kusa da ita yana kallon a cikin mirror din " hmm da sirikin namu ake waya neh" katse wayar tayi sannan ta jiyo ta kalleshi "are you jaelous of dat?" " meye sa zan yi hakan ? Yanzu kam da kika batarai kinyi kama da biri" a fusace ta kalle shi cikin harara " what! Kai kuma da me kake kama kenan kana kama da micky mouse idan kayi dariya,haka neh? " "watakila, akwai abinda kike so ki fada, fadi kawai ina jinki" " ba waninan kawai ka fito straight forward kace na baka abin da ke hannuna " " me kike nufi ?" " nidai gashinan it is a wristwatch from turkey for you, is dat ok" ta fada sannan ta juya ta nufi glass wall dake gefen ta " tnks dear " areef ya fada sannan ya ka da cewa" kin dade ba kije irin wayancan guraren ba koh ?" " me kake kokarin fada neh? Kai fa dan kauye ne, watakila ma idan an ritsa kama ba lallai ka iya swimming din ba" "toh ko za'a gwada neh " " kana son dai kawai kayi wasan ruwa koh? To badani ba" Anti laila ce ta shigo wadda ta dafa kafadunsu " guys meye labari? " " wlh ba labari" areef ya fada " bawani anti laila zo muje dakina na baki labara mai dadi" eesha ta fada " yawwa sisto xo muje" nan suka tafi suka bar areef tsaye yanna yana mamakin yadda eesha take al'amuranta hakika eesha ta fara burgeshi a matsayinta na aminiyar sa .
Da safe misalin karfe 12:45am eesha na zaune akan stool dinta dake gaban mudubi ta jiyo hayaniyar su amira yayan kanin babanta da sauri ta mike tana sanye da dan short da short sleeve shirt kafin tagama shiryawa tasaka cikakkun kaya rike da lip gloss wanda zata shafa a lips dinta. Cikin murna ta zura kayanta ta shafa powder da dan lip gloss sannan ta sauka da sauri ta tare su "oh! Anti mami kune sannunku da zuwa, nayi matukar farinciki sosai " "yawwa sannu eesha kindawo lfy ? Gaskiya munyi kewarki sosai " " nima haka, amir ya kike? Dazu nagama cewa zan kira ki awaya kuma sai gaki kinzo" "eh wlh naji kinzo gari ne shiyasa na dinga rokon mami ta kawo ni naganki" "Allah sarki amma naji dadi sosai sisto zo muje dakina mudan zanta" " toh shikenan mutafi , kinga kuwa yadda kika kara kyau sai wani kyalli kike yi" amira tafada lokacin da suke nufar kafar bene , areef ne yafito daga dakin umma dake sama lokacin da sukayi gware da eesha wacce take rike da hannun amira "wayyo wai meyake damunkane? Ya kamata kadinga kallon gabanka idan kana tafiya " " toh chuchu naji, amira sannunki ina anti mamin? " "tana kasa gillor" " au kema kin dauka koh?" " kaga mu bamu waje" eesha tafada sannan suka canza hanya kuma cikin rashin sani yayi kokarin canza hanya lokacin da suka kara bangazar juna har eesha takusa gangarawa. Aref ne yayi sauri ya riko hannunta wacce ta dawo jkinsa cike da faduwar gaba wacce take iya jin kamshin turaren dake jikinsa . Hannun sa yasa ya gyara gashin da ya rife mata fuska wanda ya sakale shi a bayan kunnenta " dafatan babu abinda ya same ki" " har kaji tsoro koh?"tafada ,dariya tayi wacce dimples dinta ya loma sosai kuma dan karamin pink lips dinta suka karakyau sannan ta fada daki cike da kunya , amira dake gefe tana kallon alakar da ake kiranta da abokantaka kafin ta shige cikin dakin isha .Murmushi Areef yayi sannan yace " eesha" ya kuma kalli bangaren da dakinta yake . " hmm wannance alakar da ake kiranta da abokantaka , adai rada mata wani sunan amma ba wannan ba" " amira kada fa kiyi wani tunani na daban alakar mu da areef bata wuce alakar da kike da ita tsakaninki dashi ba wato yan uwantaka amma banda haka bana tunanin wani abu na daban" " hmm eesha kenan bakya boye min komai da shafi rayuwarki ba kuma ban fitar da ran zaki sanar dani wannan bama alokacin da kika tabbatar wa da kanki hakan " " share kawai" ta fada sannan cigaba da hirar su ta yanmata.

Areef na kwance akan gadon sa yana bacci misalin karfe12:30 na dare wayarsa dake ajiye akan bedside din dake dakin ce tayi ringing, tsaki yayi cike da kasala sannan ya duba -Oli ce yar kanwar umma wadda babar ta tarasu shekara daya data wuce hakan yasa take zaune tare da umma kafin tatafi kasar waje karatu.tsaki yaja a karo na biyu sannan yayi yunkurin daga wayar " wacce irin waya ce wannan da baza ayita ba sai a irin wannan lokacin" ya fada tare da daga wayyar " hello oli !" " na' aam yaya na ya kake ya jindadi? Da fatan kana cikin koshin lfy" " eh komai normal" " kayi kewata sosai koh yayana kada ka damu saura 8 months na kammala karatuna gaba daya, ai nakusa dawowa" " toh Allah ya kaimu, saida safe kanwata" ya fada sannan ya kaste wayar. Daure fuska ta tayi cike da bakincikin katse mata waya da yayi ta yastine fuska sannan tace " da alama baya son yin magana dani a wannan lokacin" ta fada tana yatsine fuska sannan taja bargo ta kwanta.Hakika Oli budurwace mai kimanin shekara 22 wacce take matukar kaunar areef ,wacce take kishin ganin duk wata ya mace a kusa dashi . hakika abba ne ya zabi ta zauna tare da umma a cikin gidan tare dasu samira tunda dama ita kadai iyayenta suka haifa wayanda sukayi hastarin mota suka mutu gaba dayan su, bayan Alkawarin da abba ya dauka akan ya amince ta zauna agidan na dun-dun-dun bayan amincewar kawu hakan yasa ya dauki nauyin kara tunta nagaba da secondary, duk da cewa dai oli ba wani muni ne da itaba , tana da dogon hanci, madaidai cin baki, doguwar fuska da kuma bakin cikakken gashi mai dan tsayi dayake su yan jihar katsinane,sai dai kuma oli tarasa abu guda wanda duk wata ya mace take burin mallakar sa , wannan abinkuwa ba komai bane face cikakken diri amma dai hakan bai hana ta samari dayawa wayanda suke sonta da aure ba sai dai ita ba kowane a gaban taba illa Areef.
Da safe bayan isha tashi ta karya sai ta nufi dakin inda ta bukaci areef ya rakata bangaren kawu domin ta gaida shi,suna tafe akan doguwar kwaltar dake cikin gidan suna yar hirarsu ta yan uwa rike da sweet din da take tsosa a hannunta.




You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Oct 03, 2018 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

So Sirrin ZuciyaWhere stories live. Discover now