ASALIN AMINA Bingyel Cont..Bayan tarewar saratu kamar yadda kowa ke zato, Inna Hadi da mafi yawa a dangi ba su karbeta ko da hannu daya ba balle biyu. A haka ta fara rayuwa cikinsu. Da dadi ko babu ta yikudiri za ta zauna a gidan aure a garin dange gidan mijinta mal umaru direba saboda ta samu rahamar Allah kamar yadda Malam Isah Mafara da iyalansa suka kara kwadaitar da ita a zaman da tayi dasu na watanni kadan. Don haka zata jure duk runtsi, duk wuya. Ko banza ai idan bata jure ba, ta sani iyayenta ba zasu karbe ta ba.
Ga umar ba mazauni ba, sai yayi kwanaki baya gari musamman idan yayi lodin pasinja nesa da jahar sakkwato. Sai dai yana kokarin wadata ta da duk abinda yasan za ta bukata. Cikas daya ne, inna tana saka idanu, tace ya koma bawan mace, macen ma maras asali. Tun tana jurewa ta nuna ba ta ji haushi ba har ta fara boyewa tana kuka. Idan haka ta faru baya samun kwanciyar hankali sai ya lallasheta ya bata hakuri. Ya kan fada ma ta yace, "Saratu kiyi hakuri, watarana inna za ta gane ta daina wannan cin zarafin. Babu yadda zanyi da ita mahaifiya tace."
Sannu a hankali ta fara sabawa da rayuwar gidan, ta sha alwashin daurewa akan gori da fadace fadacen inna hadi. Bata dade a dange ba, taci gaba da neman ilimin addini akan wanda ta fara samu daga gidan Mal. Isah. A gidan wata malama luba take daukar karatu duk dare, umaru ne ya hada ta da ita. Ko ranakun da babu islamiyya zuwa ta keyi, musamman idan umaru baya gari. Daga baya ya bata jari ta fara sana'ar chinchin da su alawar madara, kuma babu laifi ana saye, saboda yadda take inganta sana'ar, kamar yadda ta taso taga mahaifiyarta churi ta nayi.
Daga cikin kudin sadakinta kuma tace a sawo mata tela. Ta fara koyon dinki a wajen malama da 'yayanta da yake sana'arsu kenan. Inna sam bata kaunarta, duk da kyautatawar da saratu ta ke yi mata. Ta kafe sai umaru ya kara aure, shi kuma a yadda yake jin saratu a lokacin, sam ba zai iya hada ta da wata mace ba. Mutane da yawa a boye suke hulda da saratu saboda gudun fadan inna. Wasu kuma su dinga goyon bayan inna su na habaici da cin zarafi ga saratu.
A cikin wata na shida da auren, musa ya samu yazo wajen yayarsa, yayi kewarta ba kadan ba, kuma yana so ya sanad da ita ya samu gurbin karatu zaya fara karatu jami'ar ABU Zaria fannin Engineering. Kamar yayi kuka da ya sameta ita kadai tana laulayi. Inna ce a tsakar gida tana zaginta, tana fadin "ai dole kiyi amai wanda ke shagwaba ki yana sawo miki lemun kwalba baya nan, 'yar banza nunar rana kodaddiya dangin arna."
Alhali ita ce ta karar da crate biyu na lemun kwalba da kwalayen cabin buiscuit da umaru ya ajiye ma ta don bata iya cin abinci har sai ta hada da lemu ko ta dinga cin cabin haka nan, idan tayi sa'a ya tsaya a cikinta ba tayi amai ba.
Musa yayi sororo cikin takaici, yana jin cin mutunci daga bakin wannan dattijjuwa, yana mamaki wai yau sarah ake yi ma wannan cin mutunci akan lemon kwalba! Saratunsa! Ita da a gidansu suke sayar da shi har su ke kyautarwa. Bayan ta juya suka shiga dakin saratun suna hira cikin harshen fulatanci, inna ta fado musu tana fadin "me zan gani haka, wannan kedarin arnen a daki? yazo ne ku iyar da lashe kuruwar umaru? Toh ta Allah ba ta ku ba, wai gayyar tsiya arna a taron idi. Maza zo ka fice kafin nasa yara su kore ka kamar karnuka 'yanuwanka."
Haka ya mike ya fita cikin takaici. Kafin ya baro garin ya sawo mata lemu da fruits. Maimakon ya shiga kamar yadda ta sa aka shigo dashi farkon zuwansa, sai yasa a kayi kira ma sa ita, ta fito a soron gidan, saboda ya ga alama inna hadi tana son tara ma sa jama'a. A kan hanyarsa ta komawa gusau yake tunani wai wannan ita ce mahaifiyar umaru direba! Umaru mai sanyin hali da hakuri.
A cikin irin wannan rayuwa ta haifi Amina, wadda take kira da Bingyel, a shekarar 1990. Ko a lokacin musa ne kawai yazo. Da zaya wuce ta fasa kuka tace ya rokar mata iyayensu gafara tazo ta ganesu. Wata goma da haihuwarta umaru ya dauketa su kaje gusau, sam churi taki karbarta, ta koreta daga ita har diyarta da bata ko tsaya ta ga kalarta ba. Mahaifinta daya dawo ya samu labari, yaso suje amma churi tace ya kyaleta, idan taji wuya zata gudu ta dawo hannunsu, amma yanzu tana a tsakiyar makiyansu bai kamata su amsheta ba.
Haka shekaru su kayi ta tafiya saratu da diyarta suna cikin tsangwamar inna hadi. Daga baya ta fahimci umaru ya canza saboda wani karin shakku da tsoron mahaifiyarsa daya karu a kan na da. Ba wai ya daina son taba, amma kuma baya iya kare ma ta hakkinta a gun mahaifiyarsa kamar yadda yake kokari can baya, sai dai idan sun kadaice yayi ta lallashi da bata hakuri.
Lokaci zuwa lokaci musa ya kan ziyarci 'yaruwarshi saratu. Duk da kyarar da inna ta keyi ma sa. Ya tsani tsohuwar sosai, kuma ya fara jin haushin umaru. A ganinsa, me yasa ita sarah zata bata da iyayenta saboda shi, amma shi ya dinga jin shakku wajen hana mahaifiyarsa cin zarafin da ta ke yiwa sarah. Yana kokari kwarai wajen ganin ya shawo kan mahaifansu, har Allah Yasa churi ta fara saukowa. Ko dama babansu yana kewar saratu, kafewar tafi karfi a bangaren churi.
Bayan saratu ta yaye amina, musa da yazo hutu daga ABU, ya hadu da umaru su kayi yanke shawara akan saratu za tazo gusau ta ziyarci mahaifansu. Da kan shi umaru ya kawo ta, amma bai shiga ba. kuma a wannan karon ta samu sassauci kwarai. Ita kuma churi, haka kawai zuciyarta ta jarabtu da son Amina Bingyel, motsi kadan zata dauketa ko ta zura mata idanu tana kallo fuskarta dauke da murmushi. Daga ta fita ko da makwabta ne, sai ta shigo da wani abin da sunan Bingyel.
Tun daga wannan lokaci, saratu da Amina Bingyel su kan ziyarci iyayenta duk shekara. Idan zata tafi, sai ta tanadi sallayarta, da hijabai musamman da take kebewa don ibadah. Mahaifinta bai damu akan wannan ba amma mahaifiyarta a kullum ta ganeta tana sallah, sai tayi ma ta fada da wa'azi. Wai kada lokaci ya kure bata dawo hanyar gaskiya ba. Abinda ke ci mata tuwo a kwarya, umaru baya barinta tayi kwanaki da yawa idan taje. Daga ta kwana uku zuwa hudu sai yazo daukarta. Mama churi za tayi ta fada da zuga saratu, amma a haka zata shirya ta bi mijinta.
Amina tana aji uku a firamare, kakanta Ja'e ya ziyarcesu a garin dange. Saratu tayi murna kwarai, har malama luba said a ta aika tazo ta gaisa da mahaifinta. Inna hadi da ta shigo ta ganeshi zaune tare da musa da umaru, da suka gaisheta ta amsa sai ta kalleshi sama da kasa yana saye da shadda mai haske, harda babbar riga tace "Allah sarkin zaki, ta bakin barawon zuma. Hadarin da babu ruwa holoko."
Ta fito tsakar gida tana ta yada zance. Tana fadin, "shikenan Babba ya tabbata a surukin arna, wato ni duk jikokin da zaya Haifa min, sai daga tsatson wadannan batattun fulanin. To wallahi da sake. Bari larai tazo. Dolensa ya kara aure ko yana so ko baya so.

YOU ARE READING
Kallabi ko Hula
General FictionA tsakanin Haihuwa zuwa Mutuwa, Mutum dan-adam ya kan rayu ne a bisa kaddararsa. Ingancin rayuwar mace ko namiji sun ta'allaka ne akan abubuwa da dama ciki har da iyalan da ya fito daga ciki wato iyaye, dangi - da kuma gidan aure. Aure babban abu n...