SOKOTO, NOVEMBER 1993."Hello abba, kuna nan lafiya" a bangare daya aka amsa, "lafiya kalau maami, kun fita community mobilization ne yau?" "No, bamu fita ba, mun yi meeting ne da CMD, amma mun kare har na dawo gida, saboda yau off na keyi. Ina baby na, kwana biyu ban ganeta ba?"
Sai da ya nisa sannan yace, "Wallahi maami ita ce maryam take kokarin daukewa, ita fa dole sai na bata waya tunda na ambaci sunanki, yau tun safe ta daga mana hankali, a kai ta gidan maami, babu yadda ba'ayi ba ta gane cewa yau ba weekend bane, kuma yanzu ba irin da bane abubuwa sun yi yawa, amma yarinyar nan ta addabe mu ga maryam tana ta fama da amai, sai da kai ga dukanta" "akan me har da duka...." Bata karasa abinda zata ce ba ta ji yana fadin "bari mana naana!" "ka bata wayar muyi Magana."
Maimakon ya bata sai ya sa kan wayar na landline a kunnen yarinyar dake rikicin amsar wayar tun da taji an ambaci sunan maami. Tace "alo maami yaushe zaki zo daukana, maryam duka na ta keyi."
Maryam dake tsaye sai ta girgiza kai ta kama hanyar zuwa dakin bacci, ko banza a gajiye take jikinta babu kwari. Mami dake Magana a waya tayi murmushin zancen naana tace "wato naana baki ji ko, ban hana ki fadin maryam kai tsaye ba?" "Na daina maami, ki zo ki tafi dani."
Cikin murmushi mai sauti, maami tace, "zan zo naana, amma sai kin daina kuka." "za kizo maami da mota jiya ki tafi dani da kayan wasa na kuma da kaya na a cikin jaka?" daga maami har Abba da ke rike da waya, sai da su kayi dariya.
"zan zo Naana, amma gobe ake cewa ba jiya ba. je ki hada kayan wasan kafin nazo." To yaushe zaki zo." " zanzo gobe Insha Allah." "to maami yaushe ne Insha Allah."
Dariya Maami ta yi. Haka ta biye shirmen naana su kayi hira, daga baya tace, "kije daki ki hada kayan wasan, sai kin tashi daga bacci gobe zan zo". Da gudu ta fice daga palon zuwa dakin da kayanta suke. Kuma ita har a ranta da zuciyar ta kuruciya haka abin yake, bata iya zama ko ina sai a wajen maminta.Washegarin ranar ya kama ranar juma'a. bayan la'asar da misalin karfe biyar, mami ce tuka mota tun daga unguwarsu gawon nama zuwa unguwar runjin sambo titin kangiwa, a kofar gidan Abba tayi parking. Da gudu naana tazo ta rungumeta, tana cewa "maami tun gobe na tashi daga bacci amma baki zoba." To Naana baby ai gani nazo yanzu."
A daki ta taradda maryam tana fama da laulayin ciki, zazzabi da amaye amaye, nan take ta rubuta magani da allura abba ya je karshen layinsu ya sawo. Bayan ta yi ma ta allurar ta bada shawara akan idan ba a ga sauki ba gobe za a je da maryam asibiti ko gidanta a kara mata ruwa (drip). Daga nan tayi musu sallama, ta fito daga gidan rike da hannun naana, abba yana a gefenta dauke da jakar kayan naana. Suna hirar imam da babansa da suke can kasar Canada. Yace," maami anya wannan yarinya zata bari ki karasa shirinku na tafiya Canada? Na so ta zauna har ki gama da wurin aiki zuwa karshen watannan tunda ni yanzu study leave na keyi, ko banza ga jami'oin sun tafi strike."
"Kar ka damu abba, duk babu abunda zaya gagara, shirin tafiya ai baban Imam ya bar komi a hannun Baban Abdul. Kuma ina ce tafiyar nan da naana za'ayi? To ka ga ai gara ina tare da ita."
Naana da ke jin su tace "abba ba da kai za muje gun daddy ba, amma zan sawo ma abin dadi." Shi da maami su kayi dariyar shirmen naana. Sai da suka shiga mota maami ta ja suka dau hanya, naana ta dago mi shi hannu alamun bye bye, sai faman washe hakora ta keyi. Sannan ya juya ya koma cikin gida cike da kaunar 'yaruwarsa rabin jiki●○
💚💛💜
YOU ARE READING
Kallabi ko Hula
General FictionA tsakanin Haihuwa zuwa Mutuwa, Mutum dan-adam ya kan rayu ne a bisa kaddararsa. Ingancin rayuwar mace ko namiji sun ta'allaka ne akan abubuwa da dama ciki har da iyalan da ya fito daga ciki wato iyaye, dangi - da kuma gidan aure. Aure babban abu n...