Ten

2.5K 279 31
                                    

®Fikrah Writers Association🖊

                 ©Jeedderh Lawals

          Wannan shafi gabadayanshi ya tafi zuwa ga Batoul Mamman. Congratulations on finishing your amazing, mind blowing novel, Kashe Fitila. Hakika ya fadakar, Allah kuma ya bamu ikon yin koyi da darussa na gari dake cikin littafin. Allah ya kara basira da zakin hannu, Ameen. Allah ya kara daukaka ahalin Fikrah baki dayansu, Ameen.

                                         •°*****°•

                 Babu abinda bata gwada yi ba wanda ta saba a duk lokacin da tension, stress ko damuwa ya mata yawa. Amma a ranar to no avail!.
Taji kidan, maimakon ya rage mata, sai ma ya kara mata tafarfasar zuciya. Ta gwada ci gaba da rubuta wani journal da take yi akan chronic kidney failure, amma gabadaya ta kasa hada kalmomi waje guda su bada abu mai sense. Zuwa lokacin data gama Yoga stance, hawaye share-share ke fita daga idanunta. Ta kwanta akan yoga mat din hawayenta na gangarawa cikin kunnuwanta.

Ta tsani kanta for clinging unto someone that didn't give a damn about her and her heart, ta tsani kanta akan kasa mantawa da tayi dashi, furthermore, she felt disgusted with her self!.

                              ☆☆☆

Ta kai cup din wine na biyu bakinta a wannan daren, idanunta suka sauka akan wasu matasa dake ta shakar tabar wiwi, wasu har hada kawunansu suke yi da bango saboda tsabar buguwa. Yayin da wasu suke ta watangaririya a wajen. Sam harkar shaye-shaye bai dada ta da kasa, a hakan ma da take shan giya, she felt disgusted. Amma ya zata yi? A daidai wannan lokacin ita kadai ce abinda zai kwantar mata da tafasar da zuciyarta ke yi.

Ranar bata zo da kowa ba, don haka cikin kaffa-kaffa take. Ta kai kofi na hudu bakinta, tun kafin ya kai bakinta taji an rike kofin. A fusace ta daga kai, duk da dusu-dusu da take gani da duhun wajen, hakan bai hanata gane ko waye ba; Kamal. Yadda aka yi ya san maboyarta da inda take, was beyond her imagination.

Fuskarshi dauke da matsanancin bacin rai yake kallonta kamar zai kona ta da zazzafan kallonshi. Duk da hakan sai da tayi gigin kara kai cup din bakinta. Bai yi wata-wata ba yayi wurgi da cup din gefe, abinka da glass ya hadu da bango, take ya fashe. Kwalbar ma bai barta a baya ba, ya sake hada ta da bango, sauran wine din da kwalbar suka tarwatse kowanne yayi nashi wurin.

Tayi scoffing tana shafa gefen wuyanta, frustrated, "are you kidding me? Who the hell did you think you are da zaka zo kana invading personal life dina?!" ta fada cikin daga murya, a fusace. Babu wanda yayi paying attention zuwa garesu, kowa abinda ke gabanshi yake yi.

Shima cikin daga murya cike da bacin rai yace "kin fini sanin ko ni waye Sheerah! Kin kuma fini sanin cewa I'm capable of more than invade your personal life!!..." ta katse shi, "wato dariya da kula ka da kaga ina yi shi yasa kake tunanin kana da damar yin abinda kaga dama, ciki har da tunanin juya ni? Well, you are wrong! Baka isa juya ni ba Kamal, kai ba kowa bane a gareni, so you might as well go, ka barni inji da abinda ke damuna!".

Ya kalleta sosai, "maimaita abinda kika fada. Ni ba kowa bane a gare ki??". Tayi shiru, kanta a can gefe guda. Ya kula da yadda idanuwanta suka kasa focusing waje daya, da yadda jikinta yake rawa, fuskarta tayi jawur, kada ma idanuwanta suji labari. Daga gani ba karamin kuka taci ba. Yaji wani irin abu ya tsarga cikin zuciyarshi, tausayinta ya dabaibaye shi, yaji kamar ya zauna ya saka ta a gaba yana kuka. Amma a matsayinshi na namiji, wanda yake so yayi comforting dinta, yana ganin ba abinda ya kamata yayi kenan ba.

Ya sassauta murya a hankali, yace "what happened to you Sheerah? Waya maida ki haka? Waye wannan mutumin daya maida rayuwarki upside down cikin yan awowi?". Ta hadiye wani daddatan yawu, "kada ka tusa kanka cikin matsalar da ba taka ba Kamal. Ka tafi kawai".

Doctor Sheerah! (SAMPLE ONLY)Where stories live. Discover now