ASALIN AMINA Bingyel Cont...Duk kiyayya da cin zarafi da saratu take fuskanta daga inna hadi, a haka take jurewa. Tun bayan auren, imani da ilimin islama yake kara shiga zuciya da ruhinta, kuma tana kara samun karbuwa a wajen jama'ar gari saboda hakuri da kyawawan dabi'unta. Duk abibda aka ce Allah da manzo suna so, bata wasa a kai. Idan ko aka ce haram ne, tana kokarin nisanta kanta da shi.
Bayan karatun da take yi a wajen malama luba, yanzu har islamiyya aka bude sabuwa a garin dange ta hanyar kungiyar izalatul bidi'a acan take karatu. Sai ga saratu ta zamo daya daga cikin manyan dalibai masu kwazo da himma. A bangare daya kuma tana sana'ar dinki da kayan fulawa dasu alawar madara.
SHEKARAR 2000
Amina bingyel tana girma kamanninta da mahaifiyarta suna kara fitowa tamkar kwabo da kwabo. Yanzu har ta kai shekaru goma amma bata samu kani ko kanwa ba, saboda duk saratu ta samu ciki zubewa ya keyi. Umaru har asibitin Specialist ya kai ta, inda aka tura su zuwa asbitin UDUTH a garin sokoto, inda aka hada ta da kwararrun likitoci. Wasu lokuta tayi ta zubar da jini. A wannan shekarar Ja'e mahaifinta ya amsa kiran mahalicci. Tayi bakin cikin rasa shi, kuma tayi bakin cikin har ya mutu bai amshi musulunci ba.A bakin mutanen gari take ji wai inna hadi ce da shawarar diyarta larai ta ke yin asiri, akan umaru ya dinga yi mata biyayya sosai ka da saratu ta mallakeshi kuma kada ta kara haihuwa, saboda a cewar larai wasu 'yan bori sun fada mata saratu asiri ta keyi don raba inna da dan ta guda daya tilo namiji, kuma ta haifa ma sa karuwai idan bata tashi tsaye ba.
Saratu addu'a ta ke tayi akan maganganun da taji, amma ko ta samu cikin sai ya zube.
Kanwar umaru mai suna sadiya, wadda take bin larai, ita ma a anan dange take auren wani malamin makaranta ta sha fada ma inna hadi cewa wannan karyar masu bori ce. Sam ba halinsu daya da larai ba, sosai take jin tausayin umaru yayanta da iyalinsa akan kiyayyar inna da larai.Wata rana ta samu labari cewa larai ta amso magani za ta kai wa inna a ranar ta je gidan a fusace. Ta samu sun a maganar. Su na ganinta sai suka yi shiru.
A fusace ta fuskanci yayarta tace "larai ki ji tsoron Allah, shi yayan zaki zauna kina nemo asiri akan shi? Kuma saratu me ta tsare muku. Wallahi ta fi ki jin tsoron Allah don ayyukan ta sun nuna. Ranar da hakkinta zaya fita akan ki za kiyi da na sani, idan ba ki daina ba wallahi zan samu yaya da kai na in sanad dashi."
Ta juyo wajen inna da ke zaune rike da kullin magani da aka ce ta zuba a bandakin saratu da umaru tace, "inna ki daina biyewa larai kina cutad da mutanen da ke kula dake. Yanzu da kuke kokari kada saratu ta kara haihuwa da yaya, kika sani ko duka zuri'ar yaya umaru Allah Ya kaddaro ta tsatson saratu ne zasu samu? Me ya rage kida shi inna......." anan ta fashe da kuka ta kasa ci gaba, larai ko sai ta hau borin kunya ta dinga fadace fadace, ta dauki mayafinta da niyyar zata bar gidan.
A kofar dakin inna ta ci karo da amina dauke da kwanukan abinci da mamarta ta aiko ta kawo wa inna. A rude tace, ke munafuka me ki keyi anan? Ba tare da ta amsa ba, sai kawai ta dire abincin anan ta juya a guje zuwa bangaren mahaifiyarta. Kuma tun daga ranar kiyayyar goggonta larai da kakarta hadi ta kara samun wajen zama a zuciya da ruhinta. Abinda ta saka a ranta, duk ciwon da mahaifiyarta ta keyi, sune sanadi, kuma basu so mamarta ta haihu, haihuwar da kullum tayi sallah sai ta roki Allah Yaba mamarta lafiya kuma ta Haifa mata kani ko kanwa.
Bayan zuwan sadiya gidan, anyi sa'a, duk da yake inna hadi tayi nisa akan kiyayyar saratu amma maganganun sadiya sun shige ta, sai ta watsar da asirin, dama ba halinta bane zugar jama'a ne da shawarar larai. A lokacin ne ta fara saukowa daga kiyayyar da ta ke yi akan saratu. Dama ita saratu bata daina kyautata ma taba.
Tana aji biyar a firamare , saratu ta shawarci malam umar mahaifinta akan ta dauki jarabawar shiga karamar sakandire, haka ko a kayi. Ita babban burinta taga bingyel tayi karatu mai zurfi. Bayan Amina ta fara zuwa sakandire a makarantar kwana ta GGC da ke a garin Sokoto har ta shiga aji biyu, saratu ta samu ciki. Zangon karatu na farko amina ta yi shi ne duka cikin farinciki da doki saboda mamarta zata haifa mata kani ko kanwa. shekarunta na haihuwa a lokacin goma sha biyu.
Bayan ta koma makaranta a zango na biyu, Allah Ya amshi ran mahaifiyarta saratu wajen haihuwa, babu uwa babu jaririn da ta haifa, cikin da aka samu da kyar, tun haihuwar amina sai dai bari da take ta faman yi. Ta rasu ta bar diyar ta amina mai kamanninta sak kamar tayi kaki. Sai dai amina ba tayi farin saratu ba duk da ita din ma mai haske ce sosai. Amina tayi kuka tayi bakin cikin rashin mahaifiyarta, daga baya kuma ta dangana saboda ta sani wanda ya mutu baya dawowa.
Musa yayi kukan rashin saratunsa, yaji gaba daya duniyar ta fita ransa. A lokacin yana zaune a lagos ma'aikaci ne a kampanin PW. Ga mamakinsa, da yazo garin dange wajen gaisuwa, sai ga inna hadi tana tarbonsa ta karbeshi hannu biyu da sakin fuska. Musa baya son inna hadi, amma haka ya daure suke kara gaisuwar rashin saratu har tana zubar da hawaye tana rokawa saratu gafara.
Tace "bari kawai musa, saratu mutuniyar kirki ce, wallahi duk zaman mu bata taba bata min ba. Allah Ya jikanta Yasa ta yafe mana."
Bai yi mamakin canzawar umaru ba don yasan yadda yake kaunar yayarsa. Amina ta dawo daga islamiyya ta tarad da uncle musa nata a tsakar gida, a guje ta sheko da gudu ta fada jikinshi tana kuka. Shi ma bai san lokacin da ya farahawaye ba, duk da alwashin da ya sha akan ba zai kara kuka ba bayan wanda yayi shi da mahaifiyarsa akan sarah. Inda take rokonshi akan ya dauko mata bingyel ko zata samu sauki a ranta. Ya baro tane a halin rashin lafiya, tun lokacin da labarin rasuwar saratu ya risketa jininta yake hawa sosai.
Rasuwar sarah, ya kara fahimtar aure a karkashin addinin islama. Ya gane cewa namiji a matsayin uba ko miji yana da karfin ikon akan iyalansa a ko wane irin yanayi. Tun wani lokaci da ya shude ya yarda, ya saduda, ya sani wannan shine kaddarar sarah, wato auren umaru, zama a dange da haihuwar amina bingyel. Don haka zai yi ta lallaba mama churi tayi hakuri, yasan ba zasu taba samun damar rikon bingyel ba. amma yasha alwashi idan yana raye, amina ba zata ga bakin ciki ba, ba zaya bari inna hadi ta kassara ma ta rayuwa ba tunda ga yadda mahaifinta ya zama. ko banza duk lokacin day a kawo ziyara a dange ko kuma su kaje gusau ita da sarah, amina ta kan kwatanta mai irin halayen inna hadi. Ya san cewa duk da kasancewarta yarinya to bata son kakarta hadi. ya daukar ma ransa, zaya kula da Amina. Amina, Meenar sa, Bingyel din saratunsa amanar da ta bari a duniya!
YOU ARE READING
Kallabi ko Hula
General FictionA tsakanin Haihuwa zuwa Mutuwa, Mutum dan-adam ya kan rayu ne a bisa kaddararsa. Ingancin rayuwar mace ko namiji sun ta'allaka ne akan abubuwa da dama ciki har da iyalan da ya fito daga ciki wato iyaye, dangi - da kuma gidan aure. Aure babban abu n...