ASALIN AMINA Bingyel..Tun bayan rasuwar saratu umaru ya kara canzawa, ya dawo wani shire shire, tamkar zautacce, a bangaren masu matsalar kwakwalwa a asibitin UDUTH ya fara ganin likita saboda yadda yanayinsa ya canza. Baya son shiga jama'a haka kuma baya son magana. Daga baya a ka tura shi zuwa asibitin masu tabin kwakwalwa dake a garin kware a jihar sokoto.
Baya son fita, Ko da yaushe yana kwance a gida. Da aka matsa ya fara tuka mota da pasinja, fita ta biyu ya samu hatsari akan hanyar sokoto-zamfara, Allah Ya kiyaye ba a rasa rayuwa ba. Amma motar ta lalace.
Daga lokacin yan'uwa da abokai suka bada shawara a raba shi da mota har ya dawo hayyacin sa. Bayan tsawon wani lokaci aka taimaka ya samu aikin bayar da kati a asibitin garinsu na dange.
Inna tana son Amina kamar yadda take son mahaifinta, kuma tayi nadama akan abubuwan da tayi ma saratu a lokacin zamansu. Abinda ke sanyaya ranta daya idan ta tuna, shirinsu da saratu kafin Allah Ya amshi ranta. A bangaren amina, sam bata raga ma inna a tunaninta inna bata son mahaifiyarta. A kasan ranta gani ta keyi kamar inna da goggo larai suka kashe mata mahaifiya. Bata ragawa inna tum tana karama, ita ma innar da yake ta iya tijara sai ta ajiye soyayyar gefe suyi ta fada da amina kamar tsaranta.
Shekara daya da rasuwar saratu, Umaru ya kara aure bisa matsi na innarsa da sauran jama'a, Da kyar aka samu umaru yayi auren, wata bazawara da mijinta ya rasu, mai suna Halima (lili). Mijinta na farko rasuwa yayi basu taba haihuwa ba. Wayayyiyar mace ce saboda tayi zama a cikin garin kano in da mijinta yayi aikin gadi. Bayan rasuwarshi kuma tayi aikin dafa abinci a gidajen masu hali a cikin garin sokoto.
Da aka auro mama lili, sai Amina ta kara fita daga harkar inna, Matar mahaifinta ke kula da ita. Babu laifi tana kula da amina. Saboda ta iya zama da jama'a kuma tana hakuri sosai da halayyar mijinta da ta sauya. Tasan yadda ta ke tafiyar da kowa. Tana hakuri da umaru, don wani lokaci sai yayi kwanaki bai yi Magana da kowa ba.
*****************Amina bingyel tana aji hudu a sakandire, a lokacin mahaifinta ya fara samun sauki har ya koma sana'ar sayar da dabbobi, sai dai rashin yawan magana. A lokacin aka fahimci alakar amina da kawunta musa tayi karfi sosai. Duk lokutan ziyara a makarantarsu ya kan aje duk abinda ya keyi ya kai mata ziyara tare da dimbin tsaraba. Ire iren sutura da kayan amfani da take zuwa dasu gida yasa hankalin mal umar ya tashi. Inna hadi ta samu labarin musa yana zuwa wajen amina sai tayi ta fadace fadace tana cewa "babba idan ba ka dauki mataki ba, wannan yarinya za ta canza addini, kuma kaci amanar mahaifiyarta."
Tayi ta kokarin cusa wannan a zuciyar umaru da mama lili kuma tayi nasara. Ya ja kunnen amina sosai sannan ya kira musa a waya (a lokacin wayar GSM ta shigo) yace baya son ya kara zuwa wajen amina a makaranta.
Bayan sun shiga aji biyar, wani hutu da suka zo gida, a bakin yaran makwabta da suke karatu a makaranta daya da amina aka samu labari cewa uncle musa yazo ya tafi da amina kwananta hudu ba ta dawo makaranta ba. mal umaru ya tsare ta da bulala ya tabbatar da gaskiyar Magana. Duk inda hankalinsa yake sai da ya tashi.
Da aka koma hutu ya tasa amina gaba tare da tsohon yaronsa Abu rariya wanda ya tuka su a mota yaje kai tsaye su ka samu shugabar makaranta da maganar.
Anyi bincike mai zurfi, aka tabbatar da musa ne ya tafi da amina da taimakon wasu malamai guda biyu, Mr. peter da Mrs Joy. Tun daga ranar kuma a wannan lokacin umaru ya cire amina daga makaranta bai saurari hakuri da rokon da shugabar makaranta da wasu malamai su kayi akan yayi hakuri hakan ba zata kara faruwa ba.
Musa da ya samu labari yazo har garin dange bayar da hakuri, akan ba zai kara kula amina ba ayi hakuri ta koma makaranta. Amma umaru da inna da suka ci mutuncinsa har da 'yan sanda aka kira ma sa, sanna suka fada mai idan ya kara shiga al'amarin amina to hukuma ce zata raba su da shi.
Da shawarar inna da larai aka matsa akan sai ta fito da miji a cikin samarin da take kora. Abu rariya yana jin haka, bai yi kasa a gwiwa ba, yace shi yana son ta kuma zaya aureta!
Da taimakon inna da amincewar mal umar aka fara shirin aure amina bingyel da abu rariya. Amina tayi kuka tayi bore, sannan ta roka haka ma malama luba aminiyar mahaifiyarta, akan a janye maganar aurenta da abu, amma mal umar da sauran danginsa suka yi kunnen uwar shegu.
Wanna shine sanadiyyar auren amina da abu direba Rariya. Toh a yanzu aure ya mutu. Kuma zaman amina ya dawo a garin sokoto a gidan Maami Asmau. Ko yaya rayuwar Amina zata kasance?
Allah Masanin Gobe
**************************CIGABAN LABARI..
YOU ARE READING
Kallabi ko Hula
General FictionA tsakanin Haihuwa zuwa Mutuwa, Mutum dan-adam ya kan rayu ne a bisa kaddararsa. Ingancin rayuwar mace ko namiji sun ta'allaka ne akan abubuwa da dama ciki har da iyalan da ya fito daga ciki wato iyaye, dangi - da kuma gidan aure. Aure babban abu n...