Twelve

2K 245 13
                                    

®Fikrah Writers Association🖊

                 ©Jeedderh Lawals

                            *DOCTOR SHEERAH!*

                                         *•°12°•*


          Hana tace ita atafau sai dai Abdul ya kyaleta ta fara aiki. Shi kuma yace ina! Ba dai a gidanshi ba. A ganinshi babu abinda ya rageta dashi da zata ce zata yi aiki.

Wasa-wasa fa rigima ta barke sosai, har sai da Hanan ta danganta da kiran Siddiqa. Ita tazo har gidan ta zaunar da Abdul suka yi magana, daga karshe dai ya yarda ya amince.

Hana ta samu aiki da wani banki anan Dubai din, babu bata lokaci ta fara aikinta itama ta fara cin gashin kanta. Matsala ta gaba data danno musu itace rashin lokaci da suke ba junansu. Hana ta dauki aikinta da matukar muhimmanci bana kadan ba. Kafin karfe bakwai na safe take fita wajen aiki, ta dawo karfe bakwai na yamma. Wani lokacin da kyar take samun lokacin hada abincin safe dana dare, watarana kuma sai dai su buge da yin order. Ganin haka shima Abdul sai ya fara bin PA dinshi wajen tafiye-tafiyen da yake yi. Shikenan, sai rayuwarsu ta zama kamar ta wasu bakin juna. In an hadu, sai da dare kawai. Da safe kafin miji ya tashi daga kan gado, mata ta fita. Kafin miji ya dawo daga wajen aiki, mata tayi barci.

Normally, on weekends su kan fita waje su zagaya gari sosai da wajajen shakatawa. Sai weekends din suka zamar musu lokuta na huce gajiyar aikin satin, shirya yadda satinsu na gaba zai kasance, da warware stress. Ayyukansu da rayuwar aurensu suka zame musu their first priorities. They were committed to their works.

A cikin shekarar Hana ta samu ciki. Bata yi farinciki ba, kamar yadda bata yi bakinciki ba. Ta cigaba da rainon cikinta. Sai data shiga wata na takwas sannan ta dauki hutun haihuwa a wajen aikin.
Ta haifi diyarta mace, kyakkyawa da ita wadda ta dauko kamanninta, taci suna Fadima. Watan yarinyar daya, Hana ta koma bakin aikinta. Su duka basu da lokacin zama raino, don haka tayi suggesting su dauki nanny da zata dinga kula da yarinyar. Shi a shawarar Abdul, a kawo wata daga cikin danginshi daga Nigeria ta dinga kula da yarinyar, amma Hana fir ta ki. Ta fito ta nuna karara cewa bata son dangin Abdul suna rabar shi, kuma hakan yana bata mishi rai duk da cewa shima din ba wani cika kula dasu yayi ba. Ko haihuwar Fadima mutane kusan bakwai suka je daga Nigeria, ciki har da Aina'u da Jamila. Matsalar, basu samu tarba mai kyau ba daga matar gidan. Shi kuma duk yadda yaso yayi entertaining dinsu abin ya gagara, no matter how hard he tried, sun kasa zama comportable a gidanshi. Kwanansu biyu suka koma. Ko zancen nanny dinma, Aina'u ce ta bashi shawarar ya dauko wata daga gida. Tana tsoron yaran Abdul su tashi basu san yare da al'adarsu ba.

Sun gama magana dashi lafiya lau, har ta buga waya Kazaure an samu wata dattijuwar mata da mijinta ya rasu. Kawai sai ya kirata washegari yace ai Hana ta riga data samu wata nanny din, don haka aka bar maganar.

Hana ta samu wata balarabiyar mata, Aifa. Bazawara ce dake zaune a cikin Dubai amma yar Qatar ce. Tana zuwa da safe kafin Hana ta tafi wajen aiki ta koma da dare idan ta dawo. Idan Hana ta ba yarinyar nono ta sha sai ta bar mata ita ta tafi wajen aikinta, ita kuma ta zauna ta kula da yarinyar.

Rayuwar tasu dai haka taci gaba da tafiya, babu armashi ko na anini. Watan Fadima tara Hana ta yayeta gabadaya. Kwata-kwata sai Aifa ta koma gidan da zama. Daki guda aka ware mata. Sai ta zama kamar yar aikin, tana shara, girki da sauran hidimomin gida. Don haka Hana ta sakar mata ragamar aikin gidan gabadaya.

Bayan shekaru uku, Hana ta sake samun wani ciki. Wannan karon sam bata yi murnar samun cikin ba. Tana gab da samun karin girma a wajen aikinta, samun cikinta yana nufin wannan damar ta wuceta kenan. Haka nan dai taci gaba da zuwa wajen aikinta, tana kuma rainon cikin har ya shiga watan haihuwarshi.

Doctor Sheerah! (SAMPLE ONLY)Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt