MATAR SO....💘💘💘

1.6K 63 5
                                    

MATAR SO.....💘💘💘
Page 1
By: MARYAM MU’AZ (HASENAH)
SADAUKAR WA....
Na sadaukar da wannan littafi ga mahaifiyata. ANTY BARAKATU MUAZ ABDULLAHI MUAZ. Wacce ita ce ta zam jagora ga rayuwa.
GODIYA....
Ina godiya ga Allah subhanahu wa ta’ala da ya bani iko da fahimtar rubuta wannan littafi. Nayi roko yadda Allah ya bani ikon fara wannan rubutu Allah ya bani ikon karkare shi.. AMEEN.
Sannan daga bisani ina rokon yan uwa da abokan arzikin da suke kaaranta wannan littafi da su yafeni idan nayi wani kuskure. Sannan kuma suyi mun addu’ar Allah ya karamin fahimta.
Za’a iya amun ci gaban wannan littafi a page ina na face book: HASEINAH NOVELZ. Ko kuma ta page ina wordpress.com/babyhaseinah ko kuma ta whatsapp group ina.. haseinah novels..08066362516...na gode.




Soyaiya ne me tsanani ke tsakanin pilot Mustapha da matar sa Iklima. Suna so da kaunar junan su matuka. Iklima ta kasance me son mijinta kamar zata mutu. Haka shima Mustapha baya son yaga abinda zai bata mata rai ko na miskala zarra. Shisa ma ya ke kiran ta da MATAR SO. Iklima ma tana son sa sai dai matsalar ta guda daya shina bata kaunar dangin Mutapha. Ta tsani taga wani dangin Mustapha sun rabe sa. Kwata kwata ta tsane su. Hakan ya sa ta ke yin kissa da kisisina iri iri dan ta raba sa da kannen sa. Mustapha shine babba acikin yaran gidan su. Matan baban sa Alhaji Ibrahim guda biyar. Biyu
. Yana son Iklima amma wani lokacin sai ya rika cewa daman ba ita ce matar sa ba. Da ma wata daban Allah ya basa wacce zata rika kula da shi yadda ya kamata. Muryar Iklima ne ya katse masa tunani inda take cewa “ka dafa dani Honey dan nima yunwa nake ji wallahi.” Kallo kawai ya bita da shi dan ya rasa abin cewa. Can kuma ya wuce madafan yana girbiza kansa dan shi abin ma mamaki yake basa. Tun tasowar sa ya ke ganin yadda mahaifiyar sa da kishiyan ta suke kula da daddyn su. Suna da yan aiki hudu amma basu taba yadda yar aiki tayi wa daddy girki ba. Amma se gashi yau a gidan sa ma shi ne ke yiwa matar sa girki. “amma ba komai duk a cikin so ne. son da nake wa Iklima ya sa zan iya mata komai dan in faranta mata.” Ya fadi yana murmushi. Jolof in taliya yayi musu. Ya dafa kwai ya daura akai. Shi da kanshi ya fito da abincin ya daura a dinning table sannan ya kira ta. Ba kunya ta taso ta zauna ta fara lodan abinci. “amma gaskiya abincin nan naka beyi dadi ba dan be ji gishiri ba.” Ta fadi tana yatsine fuska. Bin ta kawai yake yi da kallo dan ya rasa abind cewa. Can de ya daure ya ce “toh kiyi hakuri. Amma ai nayi kokari tunda ni na iya na dafa kin ci har kina complaine.” Ta kallesa fuska a daure tace “toh haushi kaji ne ko me? Ai gaskiya na ke fadi tunda abncin ba wai yayi badi bane. Kawai ni ka samar mun yar aikin da zata rika mun abinci ina ci. Dan na gaji da siyan abinci a waje.” Kallo kawai ya bita da shi be ce komai ba. Dan shi abin ma mamaki yake bashi. Iklima kenan. Shi kenan naji zan samo maki yar aikin.” Yauwa shi sa nake son ka dan kana mun abinda nake so.” Iklima ta fadi tana ta wake hakora.
   Washe gari da safe Mustapha ya je gidan su ya koro wa mahaifiyar sa ce wan yana bukatar yar aiki a gidan sa. Wai aiki yana yiwa Iklima yawa shisa ya ke so ya sama mata me taimaka mata. Kallo kawai mahaifiyar sa take bin sa da shi. Dan ta san karya yake yi. Amma se tace masa ba komai zata samar masa yar aikin. Haka ko akayi. Dan washe gari ta samar masu wata yarin ya yar shekara goma sha biyu me suna talatu. Yarinyar akwai aiki. Haka daman Iklima take so dan in ta kama saka yarinyar aiki sai ka tausaya mata.
    Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya a gidan Mustapha. Yau dadi gobe daci. Dan Iklima tama da matsaloli kala kala. Ga dan iskan kishi kamar me. Haka de Mustapha ya ci gaba da hakuri da ita dan yana matukar kaunar ta. A haka har Iklima ta samu cikin ta na fari. Murna a gun Mustapha da dangin sa kuwa ba magana. Haka sukayi ta kula da Iklima da ckin ta duk da iskancin da take musu amma suna hakuri saboda kawai dan da ke cikin ta. Bayan watanni tara Iklima ta haifo santalelen me kama da ita sak.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 13, 2018 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MATAR SO...💘💘💘Where stories live. Discover now