Fifteen

1.8K 265 17
                                    

®Fikrah Writers Association🖊

                 ©Jeedderh Lawals

                            DOCTOR SHEERAH!

                                         •°15°•


               Fadima ta gama makaranta, yayin da Sheerah da Fairoz suka shiga aji biyu a Senior year dinsu. Lokacin shekarar Sheerah sha shida, Fairoz na da sha bakwai. Saboda rashin kyawun sakamakon Fadima yasa bata wuce jami'a kai tsaye ba, sai data tsaya shekara ta zagayo ta gyara wasu courses.

Tare da taimakon PA din Abdul din, Mr. David, ta samu gurbi a University of Cyprus ta tafi inda ta fara karantar law, wanda zabin Mr. David dinne don ta kasa tantance abinda ya kamata tayi. Sheerah da Fairoz sune yan rakiya, sai da suka taya ta yin komi, tayi settling a gidan da aka kama mata anan kusa da makarantar, ta gama registration da komi, sannan suka koma cike da kewarta. Suka cigaba da karatunsu ka'in da na'in don suna shekarar karshe ne.

Haka kawai inspiration ya shiga Sheerah. Wani lokaci tana zaune ita kadai a daki tana game a Ps4 dinta, ranar ma da gangan taki zuwa makaranta sai Fairoz ce ta tafi. Ta fara tunanin hakan fa da take yi, kanta ne kawai take cuta ba wani ba. Karatun ma fa idan tayi, ba don iyayenta zata yi shi ba sai don kanta, taga to me zai sa ta cuci kanta? Kafin Fairoz ta dawo gida, ta tashi ta hada kan gabadaya assignments da projects dinta ta fara aiki a kansu.

Da Fairoz ta dawo da kyar ta lalubo ta a study room, ta baza takardu a gabanta tana ta aiki. Farinciki ya cika cikin Fairoz, abinda take so kenan. Tayi godiya ga Allah tare da zama a gefenta ta ciro nata littafan itama.

Da haka suka fitar da pattern din karatunsu, zasu yi karatu kamar babu gobe. Sau tari during weekends rufe kansu suke yi a daki su wuni suna karatu. Amma fa duk ranar da suka so yin shakiyancinsu, sai su kusa tayar da gidan da sautin kida. Wani lokacin sai Hana ta leka ta musu magana, sai suce ai suna refreshing kwalwarsu. Sai tayi murmushi kawai ta juya.

Suna cikin zana final exams dinsu, watarana wani classmate dinsu, Hareeth ya biyo su gida zasu bashi aron wani textbook. Sheerah ta shiga gida ta dauko mishi, anan farfajiyar gidan suka tsaya tana kara wayar mishi da kai game da wasu jottings da tayi a ciki. Suna cikin haka Abdul ya dawo, a gefensu yayi parking din motarshi. Direban shi ya fita da sauri ya bude mishi motar ya fita.

Sheerah har ma da abokin karatun nata suka gaishe shi gami da mishi sannu da zuwa, ya amsa kasa-kasa ya shige cikin gida abinshi, direban shi ya bishi a baya dauke da briefcase dinshi. Sheerah taji jikinta yayi sanyi, yanayin yadda Abdul din ya amsa, kallon daya jefa mata, taji alamun a jikinta akwai wata a kasa. A tsaitsaye tayi sallama da Hareeth ta shige cikin gida.

Tana shiga cook dinsu tace Abdul yana bukatar ganinta a dakinshi, bata yi mamaki ba.

Tayi sallama a kofar dakin nashi, sai daya amsa sannan ta tura kofar ta shiga a hankali. A gefenshi ta duka kusa da kafafunshi, inda yake zaune akan daya daga cikin kujerun dakin, hannunshi daya dauke da cup din ruwa mai sanyi wanda ta tabbata yar aikin gidan ce ta kai mishi, ganin cewa Hana bata riga data dawo daga wajen aiki ba.

Yace mata, "waye na ganki dashi yanzu a waje?". Tayi kasa da kanta, haka kawai, bata san dalili ba taji gabanta yana faduwa. Cikin rawar murya tace "dan ajinmu ne. Ya ari textbook ne a wajena". Yayi shiru yana kallonta kamar bai yarda da abinda tace ba, can kuma ya gyada kanshi. Yace "koma menene a tsakaninku dai, a kiyaye. Ban fadawa ita yar uwar taki ba har yanzu, amma na riga dana muku mazaje. Saboda haka bana bukatar inji ance min yau an ga saurayin waccan ko waccan, kina ji na?".

Sheerah ta daga kyawawan idanuwanta da suka cika da firgici da tsoro, ta kalli mahaifin nata. Ba karamin gigitata maganar tayi ba. A tunaninta tuni aka daina irin wannan abin, a tunaninta tun zamanin su kakarta Adama aka daina wannan abin, a tunaninta wannan zamani ya riga daya wuce. Sai gashi taji da kunnenta, zai ma faru a karan kanta infact.

Bata san cewa tayi nisa a cikin tunani ba, sai data jiyo muryar Abdul kamar daga can nesa yana kara tambayarta, "... Ina fatan kin fahimci abinda nace?".
Da sauri ta hau girgiza kanta kamar wadda take kokarin cire wani abu. Yace "yawwa, tashi kije!". Cikin hardewar kafafu, kamar zata kifa, ta tashi ta fita.

Fairoz ta tari Sheerah da sauri ganin yadda take tafe cikin daukewar hankali, cikin gigita ta zaunar da ita akan gado tana jefo mata tambayar, "lafiya?". Sai data saisaita kanta sannan ta zayyana mata abinda ya faru, ita kanta ta girgiza. Ta dafe kanta cike da jimami, tace "ba ma ke nake tausayawa ba, sai Fadim. Ita da take tsakiyar soyayya da Hisham, gata da tarin abokai maza, bana tunanin idan Abbu yaji labari zai ji dadi. Itama ba zata ji dadin ba". Sheerah ta gyada kai, "exactly!".

Fairoz tace "amma ya fada miki ko su waye mazajen?" Sheerah ta girgiza kai. Ta zauna a gefenta hannunta daya a gadon bayanta tana shafawa, reassuringly., "kada ki damu kanki, ok? Everything will be fine in shaa Allah!". Sheerah tayi ajiyar zuciya, idanunta a lumshe tana jijjiga kanta.

Kwata-kwata ma bata bari maganar ta dame ta ba. Ba soyayya take yi ba, bata kuma da ra'ayin yinta a lokacin. Saboda haka tayi tunanin, me yasa zata dami kanta? Let her just live her life idan lokacin yazo, they'll surely cross the bridge. Don haka ta ajiye maganar can bayan ranta, taci gaba da harkokin gabanta.

                ⋆☆⋆⋆☆⋆⋆☆⋆

    Sun gama finals dinsu lafiya lau. Ranar Hana tayi abinda ya basu mamaki su duka. Kwarya-kwaryar liyafa ta hada musu. Ta gayyaci abokanan aikinta, har da su Siddiqa sai da suka je, da Fadima da suka samu hutu. Abin ya basu mamaki matuka, it was unlike Hana. Bata taba nuna concern akan harkokinsu ba, basu taba gani ba sai lokacin, saboda haka ace abin ya basu mamaki ma is an understatement.

Bayan kwana biyu da yin liyafar, su Siddiqa suka koma Bahrain har Fairoz. Ba karamin kuka suka sha ba lokacin da zasu rabu, kamar wadanda suka rabu kenan. Aka bar Sheerah da Fadima a gidan su biyu kwal, sai yan aiki.

Fadima ta tambayi Sheerah, "yanzu kuma ina kike tunanin zaki je ki cigaba da karatu, kuma akan me zaki yi majoring?". Ta rausayar da kanta, "ina tunanin in bi Fairoz Bahrain tunda acan zata yi karatu, ko kuma inje Abu Dhabi abina". Fadima tace "kizo Cyprus mana. Tunda makarantar suna yin courses da dama, duk wanda kike so akwai. Law zaki yi kema ko banking?" Sheerah tayi dariya, "neither. Medicine zanyi!". Wannan karon Fadima ce tayi dariya, "Lallai kin debo ruwan dafa kanki, karatun medicine ba fa karatun wasan yara bane!". Sheerah tayi smirking. Fadima tace, "koma dai menene, kizo kawai mu hade abinmu. Garin akwai dadin zama wallahi, zaki yi duk abinda kike so babu mai takura miki". Tace "sai nayi tunani". Washegari Fadima ta koma, ta bar Sheerah ita daya kwal a gidan.

Zaman gabadaya bai mata dadi. Ta saba zama ita kadai a gida, amma ba irin wannan ba. Tunda wancan lokacin, ga Fairoz nan da Fadima, yanzu kuwa ita kadai ce. Yawace-yawacenta ya dawo sabo fil, sai ma abinda ya karu. Idan kudi ne, bata da matsalarsu. Account guda gareta wanda aka bude mata shi tun tana shekara sha biyar. Duk karshen wata akwai adadin kudi da ake tura mata, ba fashi. Babu ruwanta da bani kaza, ko bani da kaza. Hana ma kanta, lokaci zuwa lokaci ta kan basu tace su sayi abinda suke so. Don haka bata da matsalar komi, sha'anin gabanta kawai take yi.

Sakamakonsu ya fita da kyau sosai, ita kanta bata yi tsammanin hakan ba. Fairoz ta fara neman admission a makarantar dake horarwa akan koyarwa anan Bahrain. Sheerah kam ta rasa madafar zuwa. Akwai makarantu da dama da take son zuwa, kuma dukansu idan tayi applying za a bata gurbin karatu saboda sakamakonta yayi kyau kwarai. Ta rasa wanda zata zaba.

Waje ta samu ta rubuta duk sunayen wajajen da take son zuwa, ta hada spinning table dasu, tayi spinning. Lokacin da pointer din ta tsaya, tana nuna sunan wajen, murmushi ta saki a hankali tana kara kallon sunan.,

"Cyprus it's!".


           ◌Short chapter? Yeah, I know. N imma really sorry for that. Zanyi dogo, dogo fa sosai next time in shaa Allah... By the way, ya kuke??◌

Please, Vote, comment, comment and comment some more. Baku san comments da votings dinku, suna matukar karfafawa jiddar nan gwiwa, as in sosai sosai ba??


#fikrawrites
#teamdoctorsheerah
#onelove😘
#anatare🤝

Doctor Sheerah! (SAMPLE ONLY)Where stories live. Discover now