Ranar da ta kasance itace ranar da su Yarima Shahidul Islam Zasu kama hanya tunda farin hantsi Aka kawo ma Sarki Sharahudden ruhoton Yarima Zulum Zubi shima zai fita domin neman lu'u lu'un sarautar a daidai wannan ranan da Yarima shahidul islam zai fita.
Bayan kamar sa'a guda sai ga wani d'an sak'on ya kawo ruhoton gimbiya Larita y'ar Sarkin Ruwa ma yau zata fita tare da tawagarsu,
Sanin da sarki Sharahudden yayi na dukansu ma'abota tsafi ne wannan yasa hankalinsa ya tashi take yasa akai masa kiran yarima Shahidul islam wanda a lokacin yake tsaye a cikin turakarsa cikin shirinsa na tafiya, kayan da ya sanya kai tsaye ba zaka dangantasu Dana yak'i ba haka zalika ba zaka kirasu dana ado ba,kaya ne masu ado had'e da azurfa a jikinsu,kayan sunyi matuk'ar k'ara masa kyau gami da sa kwarjininsa ya sake fitowa fili.
Bayan saqo ya rizqesa na kiran mahaifinnasa sai ya kulle kofar turakar tasa gabaki d'aya da katakon da suke amfani dashi domin rufe d'akuna a gidajen sarauta sannan ya doshi hanyar fada.Ko gezau baiyi ba bayan ya gama sauraren bayanin da mahaifinnasa yake masa,gwauron numfashi ya sauke sannan yace"ya Abbana kada wannan abun ya daga maka hankalinka ya tashi in sha Allah babu abunda zai faru sai Alkhairi kasancewar mun rik'e Allah ubangiji Sarkin duk duniya,hak'ik'a babu Mai yi sai shi haka zalika ni nayi imani babu abunda zai samemu sai da yardarsa,koda ace zasu shekara suna tsafi akanmu bazai yi tasiri ba bi iznillahi"
Ajiyar zuciya dattijon yayi tare da sauke fuskarsa akan ta d'annasa yace"ya kai d'ana haqiqa kayi gaskia sai dai inaso ka sani tsafi gaskia ne,Amma tunda yake mun riqe Allah shikenan,Ubangiji yayi maka Albarka,ya baku nasara"
Yace"Amin ya Abbana,sannan Abbana inaso in sanar dakai cewa yanzu mu ukku zamuyi tafiyar sakamakon ada dana sanar dakai cewa mu goma domin idan mukayi yawa tafiyar ba zatayi mana dad'i ba sannan da yake ta kasance tafiyace mai matuqar had'ari bamu sani ba ko mu dawo ko kuma mu mutu a chen ba zamu tafi da tarin jama'a ba".
"babu komai,duk inda kuke Allah na tare da ku hakanma yayi"ji yay kwalla na son zubo masa,har a cikin zuciyarsa yana k'aunar d'annasa,kuma a duk lokacin daya kallesa yakan tuno matarsa zajilat kasancewar matuk'ar kamar da sukeyi.
Sun cigaba da tattauna yanda tafiyar zata kasance,anan sarki ke shaida musu cewa su tabbata sun bar gari ta hanyar gabas sannan su fita da bisimillah,Daga haka sukayi sallama,ya fito ransa babu dad'i baya son tafiya ya bar mahaifinsa.
Sarauniya Zulzulatu ce tsaye a gaban fada tare da gimbiya Silirat sunzo masa bankwana suna jiran fitowarsa hawaye d'auke a idonsu,kallo d'aya yay musu ya d'auke dibansa daga garesu,baya so su karya masa zuciya a daidai wannan lokacin daya kamata ya nuna ma jama'ar yankin nasu tsantsar jarumtarsa. juyawa yay ba tare da ya k'arasa wajensu ba,gefe guda kuma sauran y'an fada ne wad'anda suka fito domin yi masa rakiya.
Amintaccen dakarensa mai suna Barde wanda har dashi zasuyi tafiyar shima k'ak'k'arfa ne na gaske don kaf dakarun dake yankin babu na biyunsa. Karasowa yay da dokuna guda biyu manya masu jini a jiki, sunsha ado da kayan k'arfe.
Kallon Barde yarima Shahidul islam yayi ya buqaci ya kira masa duka dakarun dake cikin masarautar,
Nan ya Amsa cike da girmamawa sannan ya juya domin cika Umarnin Ubangidan nasa.
Bayan kamar daqiqa biyar sai gasu sun hallara. Yarima Shahidul Islam ya kallesu kafin ya soma magana kamar haka bayan yayi musu sallama.
"Yaku zakarun dakarun wannan yankin namu mai Albarka,A yau ina mai sanar daku cewa zan fita cikin dazuzzukannan masu matuk'ar had'ari domin Neman Lu'u Lu'un Sarauta Wanda ya kasance walau muyi nasara ko akasin haka,ko mu dawo da rai ko mu rasu a chen" ya numfasa.
"Na za6i muyi tafiyar nan mu ukku daga ni sai Hishaf Sai kuma barde,don haka ina mai baku hak'uri na rashin saku a cikin tafiyar,ba wai don Baku chanchanta bane yasa ba zanje daku ba sai don Ku zauna Ku cigaba da ba yankin namu kariya daga duk wani mugu dake barazanar kawo mana farmaki,duk da ya kasance ubangiji shine mai kare bawansa,
sannan Ku Sani na damk'a Amanar Mahaifina,Ummata da k'anwata tare da duk wani mahalukin dake numfashi a cikin yankinnan a hannunku,na barku lafiya"yayi murmushi yana mai ja da baya.
Nan guri ya kaure da hayaniya inda wasu ke fad'ar su dai ya taimaka ya tafi dasu.
Girgiza kai yayi yace"inaso a koda yaushe Ku kasance masu tawakkali,Ku Sani da nan da Chen duk d'aya ne kudai Ku kasance masu yi mana addua"
Daga haka bai kuma magana ba ya haye dokinsa tare da kai kallonsa gun da barde yake yace"ka biya gidan galadima ka jira Hishaf ya gama shiryawa ku sameni bakin babban teku na zurar har"
Cikin girmamawa Barde yaa Amsa"umarninka nake bi ya kai yarima"
Sake kallon inda Su Sarauniya zulzulati suke tsaye yayi ya sakar musu murmushi,daganan ya sakar ma dokinsa linzami ya doshi hanyar da Zata sada sa da babban teku.
*************
Kwanaki biyunnan da suka shud'e gimbiya Larita tayisu ne cike da matsanancin fama da tunanin kyakkyawan saurayin da tayi tozali dashi zaune a bakin teku, Wanda tunda take babu wani saurayin da ya ta6a tafiya da hankalinta har ta ke 6ata lokacinta wajen tunaninsa face wannan kyakkyawan saurayin ma'abocin kwarjini da haiba.
karo na farko kenan a rayuwarta da taji tunanin wani saurayi ya Zauna a cikin ranta,tabbas da zata qara ganinsa da ta kasance cikin farin ciki marar misaltuwa haka zalika da zata san ko wanene shi sai ta ma Abbanta magana ya aura mata shi ko ta halin k'ak'a ko daga wane jinsi yake duk da tasan abune mai mutukar wahala Abbanta ya amince da auren wani jinsi wanda ya kasance ba jinsinsu ba.
Tun daga wannan ranan sai ya kasance kullum sai gimbiya larita ta fito bakin teku ta zagaya ko zata kuma ganinsa,sai dai har yau ko mai kama dashi bata sake gani ba,gashi yau che ta kasance ranan da zasu tafi,tafiyar da take sa ran yin nasara a cikinta.
YOU ARE READING
LU'U LU'UN SARAUTA
AdventureSun kasance masu neman Sarautar Lu'al Biyal wannan yasa suka fita neman Lu'u Lu'un Sarauta....