Sixteen

2.1K 285 36
                                    

®Fikrah Writers Association🖊

                 ©Jeedderh Lawals

                            DOCTOR SHEERAH!

                                         •°16°•



               Ta online tayi registration tare da registering courses din da zata yi a wannan semester. A takaice dai daga gida ta gama komi. Fairoz tuni har ta fara halartar classes abinta. Itama ranar wata Asabar tayi sallama da Dubai, ta daga Cyprus. Daga ita sai jakar hannunta ta tafi. Ranar Hana ta ziyarci wata muhimmiyar seminar, sai a waya ma suka yi bankwana. Abdul ma baya gari ranar data tafi, don haka ita kadai ta tafi.

Saukarta a filin jirgin babban birnin Cyprus; Nicosia, ta shiga jirgin kasa wanda ya kaita har kofar Jami'ar ta Cyprus.

Ta sauka daga cikin jirgin tana karewa makarantar kallo.

Iyaye wadanda suka rako yaransu suna ta shigi da fici a cikin makarantar, Wasu kuma suna ta bakwana ana ta koke-koke.

Taji wani abu ya soke ta a cikin zuciyarta, gabadaya zuciyarta ta cushe, taji kamar ta saki kuka a lokacin. Tayi zaton ma ko Fadima zata je ta tarota daga airport, sai data sauka ta kunna wayarta sannan taga message dinta kan cewa ta fita ita da abokanta, ba zata samu damar zuwa tarenta ba. Ita ta bata directions da kwatancen gidan da take da pass code na gidan. Da yake gidan anan tsallaken makarantar yake, bai mata wahalar ganewa ba.

Gidan ne hawa na biyar a cikin apartment din. Ta bude gidan ta shiga. Gidane mai dakuna uku manya, ko wanne da toilet dinshi a ciki, sai babban kicin. Ta lelleka dakunan, ko wanne da tarkacen kaya a ciki banda na karshen wanda tayi zaton nan ne nata, ta shiga tayi wanka ta dauko kaya cikin na Fadima ta saka. Text ta yiwa Fairoz da Hana ta fada musu ta sauka lafiya kafin ta kwanta barci.

Sai da magriba sannan Fadima ta dawo gidan ita da gayyar abokanta su uku. Abun ya ba Sheerah mamaki da tace ai tare suke zaune da abokan anan gidan saboda basu samu wajen zama ba. Gasu da dan banzan hayaniya, guda biyu yan India ne, daya ce balarabiya. Bata sa abun a kanta ba, tunda dai an bar mata daki guda nata na kanta, a ganinta ba matsala.

Washegari ta shiga kasuwa tayi sayayyar kayan sawa dana amfaninta, duk wasu littafai da abubuwan makaranta da zata bukata, ta tanade su kafin ranar Monday tazo. Ranar litinin ta fara halartar classes. Ta dauki lokaci mai tsayi kafin ta koyi yaren da aka fi yin communicating dashi a makarantar.

Duk da kasancewar kasar Cyprus babbar kasa ce, mafiya yawan mazaunanta kirista ne da kuma masu addinin gargajiya. Adadin mutanen dake practicing addinin musulunci a kasar, cikin kashi dari, to kashi goma sha takwas ne kawai musulmi kashi sittin da bakwai kirista ne, sauran kuma sune sauran addinai da ake practicing. Saboda haka just imagine, ya rayuwar yara kamar Sheerah da Fadima da suka taso babu cikakkiyar koyarwa ta ilimin islama, zata kasance a gari kamar Nicosia-Cyprus. Babu mafadi balle mai gyara.

Matsala ta farko data fara fuskanta a gidan, daga abokan Fadima ne. Tana kwance cikin dare, sai dai taga daya daga cikinsu ta shiga dakinta ta haye gadonta ta kwanta, ko kuma idan bata nan su shiga dakinta su mata amfani da kaya, ko toilet kuma ba zasu gyara ba balle su bata hakuri. Da tayiwa Fadima korafi, sai ta hau fada wai dama ta kula da cewa bata son abokanta, to bata da zabi dole haka nan zata zauna dasu don ba ita ta ajiye su a gidan ba. Gashi idan ta sayo kayan amfani, su rigata amfanewa, amma idan ya kare ba zasu saya ba. Ta kula ma kamar gabadayansu Fadima dince take ciyar dasu. Don haka ta cire kanta a cikin sabgar su gabadaya. Fridge ta saya babba ta kai dakinta, a ciki take adana duk wani abu da take bukata. Idan abinci ne sai ta dauka tayi warming tunda ba girki suka iya ba daga ita har Fadima din.

Doctor Sheerah! (SAMPLE ONLY)Where stories live. Discover now