MAY 2007.Zaune take a doguwar kujera ta hutawa dake a ofishinta a gabanta karamin teburi ne da dauke da takardu da take dibawa. Tana sanye atampa dinkin zani da riga kalar bulu mai duhu da ruwan madara, jikinta lullube da mayafi babba mai kauri kalar ruwan madara. Sai gilashin idanunta fari wanda ya kawata fuskarta da matsakaitan idanuwanta.
Mace ce 'yar kimanin shekaru arbain da tara, mai matsakaicin tsawo. Za a fi saka ta a layin dogaye, tana da murzajjen jiki amma ba za a kirata mai kiba ba, kuma bata cika haske sosai ba. A kan karamin teburin da ke gabanta takardu ne da file tana aikin rubutu, tayi nisa da aikinta, wayarta da ke kusa da ita kirar Sony Ericson tayi kara alamar kira ya shigo, tana amsa wayar wanda kiran maigidanta ne aka kwankasa ofishin, sannan aka murda kofar tare da yin sallama, da hannu tayi wa mai sallamar alamar ta shigo.
Mai sallama ta karaso cikin ofishin, tare da jawo daya daga cikin kujeru biyu na zaman baki da ke a gaban teburin mai ofishin ta zauna kusa da mai ofishin tare da ajiye Jakarta gefen kujerar. A daidai nan ta kare wayar da ta keyi da Alh Adam maigidanta. Ta kalli mai sallamar tare da fadin " Wa alaikissalam, ke shigo ina magana a waya. Har kun dawo barrister?"
"Mun dawo maami, Allah Ya taimakemu ko da muka je community din anyi mobilising matan yadda ya kamata, sai kawai muka fara aiki. Ke san mutan karkara akwai kara da hadin kai musamman idan abu ya hada da community leaders nasu."
"Kai Maasha Allah, abu yayi kyau. Sannunku da kokari. Yau babu komi a ofis din sai dai ko idan zaki sha tea ko kuma malt akwai a fridge."
Ta mike tana fadin, ruwa kawai zan sha, na ci abinci a ofis tare da fauziya kafin na shigo."
Ta ajiye kofin da ta sha ruwa ta koma ta zauna, sai taci gaba da cewa, "Mami kar in manta ya kamata kiyi Magana da mr. danladi akan lecture da za'ayi a government schools, ni na kare nawa part, na samo conset daga duka ministries din."
Ta dago fuskarta daga kallon takardun dake gabanta, tare da fadin "Kar ki damu ko jiya munyi Magana dashi yanzu haka fauziya tace min ni kadai suke jira nayi signing check, amma na fadi su bani yau zuwa gobe na kara review na document din gaba daya. Aikin da kika samu ina yi kenan."
"ok, to shikenan, ban yi maganar da any of them bane shi yasa."
Shiru ya ratsa a tsakaninsu, yayin da mami ke kokarin hada takardun dake a gabanta cikin folder. ta katse shirun tana fadin "wai ina 'ya ta nafisa, Allah Yasa jamb result yayi kyau."
Barr sa'adatu tayi shiru ta nisa tare da girgiza kanta, sannan tace, " lamarin nafisa ya isheni, bayan duk lesson da iyayen litttafan da aka bata, bata ci jamb din nan ba, infact babu jami'ar da zata bada admission da marks din da ta samu. Ni na rasa wannan irin dakikanci irin na nafi.... Mahaifinta koda ya bar duniya engineer ne cikakke mai tarin ilimi." (anan muryar ta ta karye kamar wadda za tayi kuka)...
Cike da bacin rai take Magana, a lokaci daya kuma tana kokarin fito ta envelop daga cikin Jakarta, ta fito da sakamakon jamb ta mika ga mami, tana ci gaba da fadin, "al'amarin nafisa har da iya shege, duk yadda na ke kokari akanta, bata taimakon kanta, babu abinda tasa a gaba daga kwalliya sai son zuwa biki. Bata ko kallon kawayenta yadda kowa yake mayar da hankali makaranta. Yanzu ko amina bingyel da take dropout aka mayar da ita makaranta kwanan nan ba ga yanan ana alfahari da ita ba. Da na fada mata haka sai cewa tayi to ai mama su 'yan kauye kokari ke garesu. nayi mata maganar naana dake jami'a ce min tayi ai ita naana a Canada tayi primary school shi yasa....."
Duk da ta damu da damuwar abokiyar aikinta sai da tayi dariya. "Tace wato ita bata kishi wani ya fita sai kafa hujja da kariyar kanta."
Barrister tace "ai na fada miki yarinyar nan bata san ciwon kanta ba. abin takaici ga baban khaleed ba wani supporting dina yake a kanta ba, bambanci sosai yake nunawa a kanta, kullum maganarshi na aurar da ita a huta kamar akanshi take zaune. Ni ina ga zan bi maganarshi in aurar da ita kowa ya huta." Ta fadi haka cike da tsantsan damuwa
Ta zuro hannunta ta kama hannun barr saadatu tace "calm down saadatu, sau nawa za muyi maganar nan dake, ki rage sa damuwa a ranki. Kina sane da abinda ake kira individual difference, amma sai ki dinga zafafawa akan nafisa. Naki addua ne da kokari akan tarbiya, ina ga abinda za'ayi mu bi maganar baban khaleed a kai ta polytechnic kamar yadda ya fadi tun farko, ta fara diploma. Kuma kada ki kullace shi akan nafisa, na sha fada miki gani ya keyi duka kulawarki akan nafisa take yana taya 'yayansa kishi ne." ta karasa maganar tana dariya maras sauti.
Barr tayi murmushi tace, "mutumin nan ba zaki gane halinshi bane baya da kara wasu lokuta."
"haka zaki yi hakuri shi kuma da nashi good side din da zaki nema a gun wasu mazan ki rasa. Zanyi Magana da Abba nawa, Insha Allah za a samo mata admission a can, amma gobe kizo da result nata da sauran particulars." Mami ta fada cike da kulawa.
"Nagode mami, Allah Ya kara rufa asiri."
"Amin, amma ki tabbata kin fada wa baban khaleed din, kuma ki nuna cewa akan shawarar da ya bayar ne kike akai, a hakan sai ya ji dadi ya dinga sa kanshi cikin lamarin nafisar."
"wai yaya maganar bikin na Abdul, na hadu da yayar amaryar a saloon last week take fada min wai kamar za a dage bikin, nace mata bani da labari."
Ta nisa tace "kesan abdul da kausar ba suyi dacen matar uba ba, hajiya madina gata dai jinin mahaifinsu ce, amma duk abinda ya taso game dasu sai ta nemi ta kawo cikas musamman shi abdul da sam baya yi da ita. abdul tun yana secondary school yake son yarinyar nan amina, tun ana daukar abin na kuruciya har ga iyaye sun amince an tsayarda maganar biki. Ita ke son a dage bikin shi kuma alh bello kamar kullum baya da lokacin da zai tsaya ya kula yasa idanu a ba kowa hakkinsa"
"Allah Ya kyauta"
"Amin. Daga farko hujjar da ta bayar wai abdul din yayi sauri, aure da 28 years. Shine Alh baba ya fada mata cewa nata mijin koda yayi auren fari bai kai wadannan shekarun ba, kuma a haka ya haifi abdul. Yanzu hujjar da ta bayar shine, zata je umarah ita da ta hannun damanta hauwa a bari su dawo, to anan ma alh baba ne yace in dai umarah zata je daga ita har hauwa da take kanwar mahaifinsu babu wanda zaya jirasu."
"Wannan ba hujja bace gaskiya, hajiya madina bata kyautawa, ai d'a na kowane, idan ta rika abdul ai ita keda riba."
"madina bata san wannan ba saadatu, son kai yayi mata yawa, da kuma samun goyon baya ga sarakuwarmu saboda ko da bata auren babansu abdul, ita din danginsu ce, kakansu daya. Abdul baya girmamata ko kadan abin har yazo ya shafi alakarshi da babanshi. Ban cika son maganar mutum ba amma kwanakin nan nayi maganar madina har na gaji da maimaitawa, mun godewa rayuwar alhaji baba da bamu san yadda abubuwa zasu kasance ba, don ni da daddyn kullum cikin bata mu take wajen hajiya wai muna hurewa abdul da kausar kunne don ba ita ta haifesu ba."
Barrister da ta kula maganar tana tuna tasowa mami da tsohon bacin rai, sai ta juya akalar maganar tace "wai dan gidana, shi ya nemi matar?"
"imam ki ke Magana, ai wannan bamu san lokaci ba, yanzu shirin zuwa wani course ya keyi Ghana."
"ke san last week matar alhaji bala ta kara min magana akan shi, har yau ban dai na mamakin matar ba, ana zaune kalau ta aiko wai samira ta tsayar da imam a matsayin wanda zata aura. Shi kuma yayi tsaye akan bai san da hakan ba."
"Ai ni kaina na sha mamakin maman samira wallahi."
To shine fa da muka hadu a airport satin da ya gabata take cewa wai yara suna son junansu, idan ma auren ne ba a so yanzu sai a kara lokaci."
Ta girgiza kai cike da takaici, tace "na rasa inda mata suka kai kima da darajarsu a wannan zamani? 'ya mace tana bin namiji alhali bata rasa masu son taba? Mu kuma iyaye duk abinda 'ya'yanmu suke so haka zamu biye musu. Idan ba rashin mafadi ba ina samira ina zubar da kimarta tana fadin ga wanda take so aure shi kuma yana denying."
Cikin dariya saadatu tace, "to ai dan nawa ne ya hadu shi yasa ya keda farin jini."
"You see, duk kune ai iyayen na zamani. Kesan akan samira mahaifinsa yayi fada sosai, har fadi yayi idan auren yake so sai a hada da na abdul, amma kar ya hada shi da mutane, sanin kanki ne familyn su alh bala da famillyn lema akwai alaka mai karfi, an zama family friends tun iyaye da kakanni."
"Allah Ya kyauta, amma pls kar a matsa imam akan samira, namiji ai shi yake nemowa idan yana so."
"Maganar ta wuce, amma yaran ne sai da haka, a zatonmu ko karya yake, amma abdul yayi wa daddyn nasu bayani, cewa laifin samirar ne. sai dai mun kafa mai sharadi akan irin haka. Don gaskiya na gaji da case din imamu da 'yan mata. Ai ba shi kadai ne namiji ba."
"Allah Ya kyauta. Mami zamani ne, sai dai addua."
YOU ARE READING
Kallabi ko Hula
General FictionA tsakanin Haihuwa zuwa Mutuwa, Mutum dan-adam ya kan rayu ne a bisa kaddararsa. Ingancin rayuwar mace ko namiji sun ta'allaka ne akan abubuwa da dama ciki har da iyalan da ya fito daga ciki wato iyaye, dangi - da kuma gidan aure. Aure babban abu n...